36 Bible Verses About God's Faithfulness
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku ƙasar da kuke shiga don ku mallaka, ya kuma kori al’ummai masu yawa a gabanku; wato, Hittiyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, al’ummai bakwai masu girma da ƙarfi fiye da ku. 2 Sa’ad da kuma Ubangiji Allahnku ya ba da su gare ku, kuka kuma ci su da yaƙi, sai ku hallaka su ƙaƙaf. Kada ku yi yarjejjeniya da su, kada kuma ku nuna musu jinƙai. 3 Kada ku yi auratayya da su. Kada ku ba da ’ya’yanku mata wa ’ya’yansu maza, ko ku ɗauko ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza. 4 Gama za su juye ’ya’yanku maza daga bina, su bauta waɗansu alloli, fushin Ubangiji kuma zai ƙuna a kanku da sauri, zai kuma hallaka ku. 5 Ga abin da za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza keɓaɓɓun duwatsunsu, ku farfashe ginshiƙan Asheransu, ku kuma ƙona gumakansu da wuta. 6 Gama ku mutane masu tsarki ne ga Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga dukan mutane a fuskar duniya, don ku zama mutanensa, kayan gādonsa.
7 Ba don kun fi sauran al’ummai yawa ne ya sa Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma zaɓe ku ba, gama ku ne mafi ƙanƙanta cikin dukan al’ummai. 8 Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar. 9 Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa. 10 Amma
waɗanda suke ƙinsa, a fili yakan sāka musu da hallaka;
ba zai yi jinkiri yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili.
11 Saboda haka, sai ku lura, ku bi umarnai, ƙa’idodi, da dokokin nan da nake ba ku a yau.
-
21 Duk da haka na tuna da wannan
na kuma sa bege ga nan gaba.
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;
saboda haka zan jira shi.”
25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,
ga kuma wanda yake neman shi;
26 yana da kyau ka jira shiru
domin samun ceton Ubangiji.
-
12 Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi! 13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
-
4 Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu. 5 Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku 6 gama shaidarmu game da Kiristi ta tabbata a cikinku. 7 Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 8 Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9 Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.
-
11 Ga wata magana tabbatacciya,
“In muka mutu tare da shi,
za mu rayu tare da shi;
12 in muka jimre,
za mu yi mulki tare da shi.
In muka yi mūsunsa,
shi ma zai yi mūsunmu;
13 in ba mu da aminci,
shi dai mai aminci ne,
domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”
-
23 Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.
-
7 Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.
8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.
-
19 Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya,
shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa.
Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne?
Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?
-
23 Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 24 Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
-
1 A ƙarshe, ’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku. 2 Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya. 3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.
-
ל Lamed
89 Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce;
tana nan daram a cikin sammai.
90 Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai;
ka kafa duniya ta kuma dawwama.
-
1 To, mece ce ribar zama mutumin Yahuda, ko kuwa mene ne amfanin kaciya? 2 Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah.
3 Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah? 4 Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana,
ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.”
-
5 Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai,
amincinka har sararin sammai.
-
8 Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka?
Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka.
-
16 Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna. 17 Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah? 18 Kuma,
“In da ƙyar masu adalci su kuɓuta,
me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?”
19 Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.
-
10 Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata;
ina maganar amincinka da cetonka.
Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka
a gaban taron jama’arka mai girma ba.
11 Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;
bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
-
Maskil na Etan dangin Ezra.
1 Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada;
da bakina zan sanar da amincinka
a dukan zamanai.
2 Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada,
cewa ka kafa amincinka a sama kanta.
-
1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,
gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,
abubuwan da aka shirya tun da.
-
3 Zan yi shelar sunan Ubangiji.
Ku yabi girman Allahnmu!
4 Shi Dutse ne, ayyukansa cikakku ne,
dukan hanyoyinsa kuwa masu adalci ne.
Allah mai aminci, wanda ba ya yin rashi gaskiya,
shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
5 Sun aikata mugunta a gabansa;
saboda abin kunyarsu, su ba ’ya’yansa ba ne,
amma wata muguwar tsara ce, karkatacciya.
6 Haka za ku biya Ubangiji,
Ya ku wawaye da kuma mutane marasa hikima?
Shi ba Ubanku ba ne, Mahaliccinku,
wanda ya yi ku, ya kuma siffanta ku?
-
4 Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,
ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
-
11 Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce, Saratu kanta kuma bakararriya ce ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne.
-
6 Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, 7 nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”
-
4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;
yana da aminci cikin kome da yake yi.
-
45 “Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci? 46 Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka. 47 Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa.
-
6 In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.
-
6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
-
4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya
filayen gidansa kuma da yabo;
ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;
amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, ka ji addu’ata,
ka saurari kukata don neman jinƙai;
cikin amincinka da adalcinka
ka amsa mini.
2 Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a,
gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.
-
29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.
31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?
-
13 Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa, 14 cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.” 15 Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari.
16 In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama. 17 Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. 18 Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu.
-
9 Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
-
11 Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.
-
19 Zan ɗaura aure da ke har abada;
zan ɗaura aure da yake cikin adalci da gaskiya,
cikin ƙauna da jinƙai.
20 Zan ɗaura aure da yake cikin aminci
za ki kuwa yarda cewa ni ne Ubangiji.
-
18 Wane ne Allah kamar ka,
wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?
Ba ka zama mai fushi har abada
amma kana marmari ka nuna jinƙai.
19 Za ka sāke jin tausayinmu;
za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka
ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.
20 Za ka yi wa Yaƙub aminci,
ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim,
kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu
tun a kwanankin dā.
-
5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,
“Ba zan taɓa bar ka ba;
ba zan taɓa yashe ka ba.”
6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,
“Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?”
-
14 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta,
Waɗannan su ne kalmomina Amin, amintaccen mashaidi mai gaskiya, da kuma mai mulkin halittar Allah.
Shows Read in context, Share and Copy.