59 Bible Verses About Truth
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. 4 Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”
5 Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”
6 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina. 7 Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.”
-
17 Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.
-
1 A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni. 2 Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. 3 Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. 4 Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.
-
20 Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi. 21 Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu, 22 sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. 23 A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. 24 Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.
25 Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.
-
31 Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske. 32 Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”
-
36 Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”
37 Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!”
Yesu ya amsa ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”
38 Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?”
Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba.
-
42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni. 43 Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata! 46 Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni? 47 Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”
-
9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. 11 A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.
-
1 ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2 Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.
3 Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. 6 Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.
-
12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. 13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 16 Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, 17 domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
-
23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;
ka nemi hikima, horo da fahimi.
-
18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta.
-
17 Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya,
amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.
-
12 Gama laifofinmu suna da yawa a gabanka,
zunubanmu kuma suna ba da shaida gāba da mu.
Laifofinmu kullum suna a gabanmu,
muna kuma sane da laifofinmu,
13 tawaye da mūsun Ubangiji,
mun juye bayanmu ga Allahnmu,
zugawa a yi zalunci da tayarwa,
faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya.
14 Saboda haka aka kau da yin gaskiya
adalci kuma ya tsaya can da nesa;
gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna,
sahihanci ba zai shiga ba.
15 Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya,
kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima.
Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi
cewa babu adalci ba.
-
5 Aboki kan ruɗi aboki,
ba mai faɗar gaskiya.
Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya;
sun gajiyar da kansu da yin zunubi.
6 Kai kana zama a tsakiyar ruɗu;
cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,”
in ji Ubangiji.
-
16 Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku;
-
16 Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, 17 Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.
-
13 Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna.
-
2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.
-
11 Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. 12 Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. 13 Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.
14 An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. 15 Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan 16 dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.
-
1 Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2 Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. 3 Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.
4 Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma. 5 Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu. 6 Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.
-
20 Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.
-
22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,
amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
-
3 Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya?
Ka buge su, amma ba su ji zafi ba;
ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara.
Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse
suka ƙi su tuba.
-
17 Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.
-
21 Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.
-
24 Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
-
18 Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.
-
13 An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. 14 Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.
-
14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku.
-
8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.
-
19 Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya,
shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa.
Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne?
Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?
-
4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;
yana da aminci cikin kome da yake yi.
-
6 Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki;
ka koya mini hikima a wuri can ciki.
-
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;
amincinka na kaiwa sarari.
-
160 Dukan maganganunka gaskiya ne;
dukan dokokinka masu adalci madawwami ne.
-
18 Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi,
ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
-
19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,
amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
-
28 Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Wannan ce al’ummar da ba tă yi biyayya ga Ubangiji Allahnta ba, ba kuwa ta karɓi gyara ba. Gaskiya ta ƙare; ta ɓace gaba ɗaya daga leɓunansu.
-
1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,
gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo
a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.
“Babu aminci, babu ƙauna,
babu yarda da Allah a cikin ƙasar.
-
26 “Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni.
-
7 Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku.
-
8 Saboda haka, sai mu kiyaye Bikin ba da burodi mai tsohon yisti ba, ba kuma da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da burodi marar yisti na sahihanci da na gaskiya.
-
4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya.
-
16 Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?
-
6 Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya. 7 Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
8 Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske 9 (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya) 10 ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.
-
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.
-
13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14 Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15 Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16 Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17 Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. 18 Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.
-
6 In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.
7 Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.
-
16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. 17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
19 Ta haka muka san cewa mu na gaskiya ne, kuma za mu iya tsaya a gaban Allah ba tare da rawar jiki ba. 20 Idan zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun san cewa Allah ya fi zuciyarmu, ya kuma san dukan kome. 21 Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan. 22 Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi. 23 Umarninsa kuwa shi ne, mu gaskata da sunan Ɗansa, Yesu Kiristi, mu kuma ƙaunaci juna kamar yadda ya umarce mu. 24 Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu.
-
3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,
“Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,
ya Ubangiji Maɗaukaki.
Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,
ya Sarkin zamanai.
-
7 Na kuma ji bagaden ya amsa,
“I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”
-
11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji,
zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka;
ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba,
don in ji tsoron sunanka.
-
33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35 ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36 Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. 37 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
-
3 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”
-
24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. 25 Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.
-
11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.
-
1 Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. 2 Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. 3 Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. 4 Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.
-
1 Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2 Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.
Shows Read in context, Share and Copy.