51 Bible Verses About Betrayal
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
14 Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci 15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. 16 Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.
17 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
18 Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ” 19 Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.
20 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun. 21 Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
22 Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
23 Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni. 24 Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”
25 Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?”
Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”
26 Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”
27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28 Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai. 29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”
30 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
31 Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya saboda ni, gama a rubuce yake cewa,
“ ‘Zan bugi makiyayin,
tumakin garken kuwa za su fasu.’
32 Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
33 Bitrus ya amsa ya ce, “Ko da duka sun ja da baya saboda kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”
34 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
35 Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
-
10 Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su. 11 Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.
12 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
13 Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi. 14 Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’ 15 Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”
16 Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
17 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun. 18 Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”
19 Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?”
20 Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano. 21 Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”
22 Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”
23 Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.
24 Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa. 25 Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”
26 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
27 Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa,
“ ‘Zan bugi makiyayin tumaki,
tumakin kuwa za su warwatse.’
28 Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
29 Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”
30 Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyu kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”
31 Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
-
45 Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, sa’a ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi. 46 Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”
47 Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su. 48 To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su, “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.” 49 Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Sa’an nan ya yi masa sumba.
50 Yesu ya amsa ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.”
Sa’an nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.
-
12 Da a ce abokin gāba ne ke zagina,
da na jure da shi;
da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina,
da na ɓoye daga gare shi.
13 Amma kai ne, mutum kamar ni,
abokina, abokina na kurkusa,
14 wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai
yayinda muke tafiya tare
a taron jama’a a gidan Allah.
15 Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari;
bari su gangara da rai zuwa cikin kabari,
gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu.
16 Amma na kira ga Allah,
Ubangiji kuwa ya cece ni.
17 Safe, rana da yamma
ina kuka da nishi,
yakan kuwa ji muryata.
18 Yakan fisshe ni lafiya
daga yaƙin da ake yi da ni,
ko da yake da yawa suna gāba da ni.
19 Allah, yana mulki har abada,
zai ji su yă kuma azabtar da su, Sela
mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu
kuma ba sa tsoron Allah.
20 Abokina ya kai wa abokansa hari;
ya tā da alkawarinsa.
21 Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun,
duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa;
kalmominsa sun fi mai sulɓi,
duk da haka takuba ne zārarru.
22 Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
23 Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye
zuwa cikin ramin lalacewa;
masu kisa da mutane masu ruɗu
ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba.
Amma ni dai, na dogara gare ka.
-
1 Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa, 2 manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane. 3 Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun. 4 Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su. 5 Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi. 6 Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, sa’ad da taro ba sa nan tare da shi.
-
1 Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu. 2 Suka daure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.
3 Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. 4 Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.”
Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”
5 Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa.
6 Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.” 7 Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. 8 Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau. 9 Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa, 10 suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”
-
47 Yana cikin magana sai ga taro sun zo. Mutumin nan da ake kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun, shi ya bi da su. Sai ya matso kusa da Yesu don yă yi masa sumba. 48 Amma Yesu ya tambaye shi ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?”
-
7 Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina;
suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,
8 “Mugun ciwo ya kama shi;
ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”
9 Har abokina na kurkusa,
wanda na amince da shi,
wanda muke cin abinci tare,
ya juya yana gāba da ni.
-
9 Yowab ya ce wa Amasa, “Yaya kake, ɗan’uwana?” Sai Yowab ya kama gemun Amasa da hannun dama don yă yi masa sumba. 10 Amasa kuwa bai lura da wuƙar da take hannun Yowab ba, Yowab kuwa ya soke shi da wuƙar a ciki, hanjinsa suka zube ƙasa. Ba tare da ƙarin suƙa ba, Amasa ya mutu. Sa’an nan Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka fafari Sheba ɗan Bikri.
-
16 Daga iyakokin duniya mun ji waƙoƙi,
“Ɗaukaka ga Mai Adalcin nan.”
Amma na ce, “Na lalace, na lalace!
Kaitona!
Munafukai sun ci amana!
Da munafunci munafukai sun ci amana!”
17 Razana da rami da tarko suna jiranku,
Ya mutanen duniya.
-
18 “Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’
19 “Ina faɗa muku yanzu tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi. 20 Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ”
21 Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
22 Almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake. 23 Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi. 24 Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?”
25 Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?”
26 Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman. 27 Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi.
Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.” 28 Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.
-
1 Kaitonka, ya kai mai hallakarwa,
kai da ba a hallakar da kai ba!
Kaitonka, ya maciya amana,
kai da ba a ci amanarka ba!
Sa’ad da ka daina hallakarwa,
za a hallaka ka;
sa’ad da ka daina cin amana,
za a ci amanarka.
-
43 Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.
44 Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.” 45 Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba. 46 Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi.
-
28 Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.” 29 Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.
-
9 “Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni. 10 A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna, 11 annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.
-
66 Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.
67 Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”
68 Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. 69 Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
-
18 Da Delila ta gane ya gaya mata kome yanzu, sai ta aika saƙo zuwa ga shugabannin Filistiyawa ta ce, “Ku ƙara zuwa sau ɗayan nan, ai, ya gaya mini kome.” Saboda haka shugabannin Filistiyawa suka dawo tare da azurfa a hannuwansu. 19 Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.
-
15 A ciki wasiƙar ya rubuta, “Tura Uriya a gaba inda yaƙi ya fi zafi. Sa’an nan ka janye daga gare shi don a buge shi yă mutu.”
-
9 In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama,
kada ka tona asirin wani,
10 in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka
ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba.
-
6 ’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka;
sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka.
Kada ka amince da su,
ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai.
-
10 Ashe, ba Mahaifi guda dukanmu muke da shi ba? Ba Allah ɗaya ne ya halicce mu ba? Don me muka keta alkawarin kakanninmu ta wurin cin amanar juna?
11 Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah. 12 Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki.
13 Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki. 14 Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.
15 Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.
16 “Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana.
-
17 Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”
-
16 Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa. 17 Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.”
18 Sai Ruhu ya sauko a kan Amasai, shugaban Talatin nan, sai ya ce,
“Mu naka ne, ya Dawuda!
Muna tare da kai, ya ɗan Yesse!
Nasara, nasara gare ka,
nasara kuma ga waɗanda suke taimakonka.
Gama Allahnka zai taimake ka.”
Saboda haka Dawuda ya karɓe su ya kuma mai da su shugabannin ƙungiyoyin maharansa.
-
21 “Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 22 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto. 23 Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.
-
12 “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.
-
2 An nuna mini mugun wahayi,
mai bashewa ya bashe, mai washewa ya washe.
Elam, ki yi yaƙi! Mediya, ki yi kwanto!
Zan kawo ƙarshen dukan nishe-nishen da ta jawo.
-
1 Da ya gama addu’a, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki.
2 To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa. 3 Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu ma’aikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai.
4 Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?”
5 Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.”
Yesu ya ce, “Ni ne shi.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.) 6 Da Yesu ya ce, “Ni ne shi,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa.
-
1 Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. 2 Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, 3 marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, 4 masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah 5 suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.
-
8 Sai ta rubuta wasiƙu a sunan Ahab, ta buga hatiminsa a kansu, sa’an nan ta aika su ga dattawa da manyan gari waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake. 9 Cikin waɗannan wasiƙu ta rubuta,
“Ku yi shelar ranar azumi, ku zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane. 10 Amma ku zaunar da waɗansu ’yan iska biyu ɗaura da shi, ku sa su ba da shaida cewa ya zagi Allah da sarki. Sa’an nan ku ɗauke shi ku jajjefe shi da dutse sai ya mutu.”
-
8 Ba ku ji ko balle ku gane ba;
tun da kunnenku bai buɗu ba.
Tabbatacce na san yadda kun zama masu tayarwa;
an kira ku ’yan tawaye daga haihuwa.
-
35 Gama na zo ne in sa,
“ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa,
’ya da mahaifiyarta,
matar ɗa da surukarta,
36 abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’
-
1 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa, 2 “Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”
3 Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas, 4 suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi. 5 Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”
-
16 Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.
-
12 Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah. 13 Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni.
14 Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus,
Yaƙub,
Yohanna,
Filibus,
Bartolomeyu,
15 Mattiyu,
Toma,
Yaƙub ɗan Alfayus,
Siman wanda ake kira Zilot,
16 Yahuda ɗan Yaƙub,
da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.
-
20 Kun yi niyya ku yi mini lahani, amma Allah ya nufe wannan ya zama alheri don yă cika abin da yanzu yake faruwa, ceton rayuka masu yawa.
-
14 Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci da kai ba.” Saboda haka sai ya ɗauki māsu uku a hannunsa ya zura su a ƙahon zuciyar Absalom, tun Absalom yana da sauran rai a maƙale a itacen oak. 15 Masu ɗaukan kayan yaƙin Yowab goma kuwa sun kewaye Absalom, suka bubbuge shi suka kashe.
-
6 Za a iya amince da rauni daga aboki,
amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
-
22 Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.”
-
33 amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba,
ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba.
-
12 Gama laifofinmu suna da yawa a gabanka,
zunubanmu kuma suna ba da shaida gāba da mu.
Laifofinmu kullum suna a gabanmu,
muna kuma sane da laifofinmu,
13 tawaye da mūsun Ubangiji,
mun juye bayanmu ga Allahnmu,
zugawa a yi zalunci da tayarwa,
faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya.
-
2 Tana yin kuka mai zafi da dare,
hawaye na gangara a kan kumatunta.
A cikin masoyanta duka
babu wanda ya yi mata ta’aziyya.
Duk abokanta sun yashe ta;
sun zama abokan gābanta.
-
5 Kada ka yarda da maƙwabci;
kada ka sa begenka ga abokai.
Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka,
ka yi hankali da kalmominka.
6 Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne,
diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta,
matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta,
abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.
7 Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji,
ina sauraron Allah Mai Cetona;
Allahna kuwa zai ji ni.
-
22 Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane. 23 Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki.
-
1 Ana nan sai Absalom ya samo wa kansa wata keken yaƙi da dawakai tare da mutum hamsin da za su sha gabansa. 2 Absalom yakan tashi da sassafe yă tsaya a gefen hanyar shigar ƙofar birni. Duk sa’ad da wani ya zo da ƙara don a kai gaban sarki yă yi shari’a, Absalom yakan kira shi yă ce, “Daga wane gari ka fito?” Sai mutumin yă amsa yă ce, “Bawanka ya fito a ɗaya daga cikin kabilan Isra’ila.” 3 Sai Absalom yă ce masa, “Ga shi, ƙararka daidai ne, tana kuma da gaskiya, sai dai ba wakilin sarkin da zai ji ka.” 4 Absalom kuwa yakan ƙara da cewa, “Da a ce an naɗa ni alƙali a ƙasar mana! Da duk mai ƙara, ko kuka wanda zai zo wurina, zan in tabbatar an yi masa adalci.”
5 Kuma duk sa’ad da wani ya zo wurin Absalom ya rusuna don yă gaishe shi, sai Absalom yă sa hannunsa yă ta da shi, yă kuma rungume shi. 6 Absalom ya yi ta yin haka ga dukan Isra’ilawan da suka zo wurin sarki don neman adalci, ta haka kuwa ya saci zukatan mutanen Isra’ila.
7 A ƙarshen shekara huɗu, Absalom ya ce wa sarki, “Bari in tafi Hebron in cika alkawarin da na yi wa Ubangiji. 8 Yayinda bawanka yake zama a Geshur, a Aram, na yi wannan alkawari, na ce, ‘In Ubangiji ya komo da ni Urushalima, zan yi wa Ubangiji sujada a Hebron.’ ”
9 Sarki ya ce, “Ka sauka lafiya.” Sai ya tafi Hebron.
10 Sai Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra’ila, ya ce musu su ce, “Da zarar kuka ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom sarki ne a Hebron.’ ” 11 Mutum ɗari biyu daga Urushalima suka raka Absalom. An gayyace su a matsayin baƙi, suka kuwa tafi cikin rashin sani, ba su san wani abu game da al’amarin ba. 12 Yayinda Absalom yake miƙa hadaya, ya aika a kira Ahitofel mutumin Gilo, mai ba wa Dawuda shawara, yă zo daga Gilo garinsa. Ta haka makircin ya ƙara ƙarfi, masu bin Absalom kuma suka yi ta ƙaruwa.
-
2 Sanballat da Geshem suka aika mini wannan saƙo cewa, “Ka zo, mu sadu a wani ƙauye a filin Ono.”
Amma makirci ne suke yi don su cuce ni;
-
12 Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin.
13 Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.
-
51 “Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki! 52 An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi 53 ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin mala’iku amma ba ku yi biyayya da ita ba.”
-
23 Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi, 24 bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.”
-
8 Sai Haman ya ce wa Sarki Zerzes, “Akwai waɗansu mutanen da suke a warwatse, sun kuma bazu a cikin mutane cikin dukan lardunan masarautarka, waɗanda al’adunsu sun yi dabam da na dukan sauran mutane. Mutanen nan ba sa biyayya da dokokin sarki; ba zai yi wa sarki kyau a jure su ba.
-
12 Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.
-
9 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri, 10 gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya. 11 Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka nemi Markus ku zo tare, domin yana da amfani a gare ni cikin hidimata. 12 Na aiki Tikikus zuwa Afisa. 13 Sa’ad da za ka dawo, ka zo mini da alkyabbar da na bari a wurin Karbus a Toruwas, da kuma naɗaɗɗun littattafaina, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.
14 Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi. 15 Kai ma sai ka lura da shi, domin ya yi gāba sosai da saƙonmu.
Shows Read in context, Share and Copy.