91 Bible Verses About Knowledge

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Knowledge
  1. 1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina

    ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,

    2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,

    kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,

    3 in kuma ka kira ga tsinkaya

    ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,

    4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa

    ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,

    5 to, za ka gane tsoron Ubangiji

    ka kuma sami sanin Allah.

    6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,

    daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.

    7 Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,

    shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,

    8 gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata

    yana kuma tsare hanyar amintattunsa.

    9 Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci

    da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.

    10 Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka,

    sani kuma zai faranta maka rai.

    11 Tsinkaya za tă tsare ka,

    ganewa kuma za tă yi maka jagora.

    12 Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane,

    daga kalmomin mutane masu ɓatanci,

  2. Gabatarwa, manufa da kuma kan magana

    1 Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.

    2 Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;

    don ganewa kalmomi masu zurfi;

    3 don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,

    kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;

    4 don sa marar azanci yă yi hankali,

    yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,

    5 bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,

    bari masu tunani kuma su sami jagora,

    6 don su fahimci karin magana da kuma misalai,

    kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.

    7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,

    amma wawaye sun rena hikima da horo.

  3. 1 To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina. 2 Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba. 3 Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.

  4. 13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. 14 Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. 15 Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. 16 Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.

    17 Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. 18 Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.

  5. 1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,

    gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo

    a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.

    “Babu aminci, babu ƙauna,

    babu yarda da Allah a cikin ƙasar.

    2 Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa,

    yin sata da zina;

    sun wuce gona da iri,

    kisankai a kan kisankai.

    3 Saboda wannan ƙasar tana makoki,

    kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace;

    namun jeji da tsuntsayen sararin sama

    da kuma kifin teku suna mutuwa.

  6. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. 6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa. 7 Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji; 8 shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi.

  7. 8 Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka;

    ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.

    9 Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima;

    ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.

    10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,

    sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.

  8. 3 Ta wurin hikima ce ake gina gida,

    kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;

    4 ta wurin sani ɗakunanta sukan cika

    da kyawawan kayayyaki masu daraja.

    5 Mutum mai hikima yana da iko sosai,

    kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi;

    6 don yin yaƙi kana bukatar bishewa,

    kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.

    7 Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai

    a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.

  9. 2 Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu.

    3 Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa. 4 Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.

    5 Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; 6 ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; 7 ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. 8 Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  10. 9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. 11 Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki 12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske.

  11. 13 Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,

    mutumin da ya sami fahimi,

    14 gama ta fi azurfa riba

    tana kuma da amfani fiye da zinariya.

    15 Ta fi lu’ulu’u daraja;

    ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.

    16 Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama;

    a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.

    17 Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi,

    dukan hanyoyinta kuma salama ne.

    18 Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta;

    waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.

    19 Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya,

    ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;

    20 ta wurin sani aka rarraba zurfafa,

    gizagizai kuma suka zubo raɓa.

    21 Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,

    kada ka bar su su rabu da kai;

    22 za su zama rai a gare ka,

    abin adon da zai gyara wuyanka.

    23 Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,

    ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;

  12. 14 Zuciya mai la’akari kan nemi sani,

    amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi.

  13. 7 An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. 8 Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. 9 Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. 10 Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna. 11 Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.

    12 Jiki guda ne, ko da yake an yi shi da gaɓoɓi da yawa; gaɓoɓin kuma ko da yake da yawa suke, jiki ɗaya ne. Haka yake da Kiristi.

  14. 66 Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau,

    gama na gaskata a umarnanka.

  15. 15 Zuciya mai la’akari kan nemi sani;

    kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.

  16. 1 Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce,

    “Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka. 2 Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3 Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko.

  17. 1 Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba. 2 Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa, 3 a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani.

  18. 1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, 3 na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a, 4 don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla, 5 don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu.

  19. 10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;

    dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.

    Gare shi ne madawwamin yabo.

  20. 16 Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.” 17 Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.

    18 Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki;

    yawan sani, yawan ɓacin rai.

  21. 16 Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, 17 amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”

  22. 22 Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.” 23 Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi. 24 Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.

  23. 7 “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. 8 Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. 9 Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”

    10 Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. 11 Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, 12 zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.

  24. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.

    1 Ya Ubangiji, ka bincike ni

    ka kuwa san ni.

    2 Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi;

    ka san tunanina daga nesa.

    3 Ka san fitata da kuma kwanciyata;

    ka saba da dukan hanyoyina.

    4 Kafin in yi magana da harshena

    ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.

    5 Ka kewaye ni, gaba da baya;

    ka sa hannunka a kaina.

    6 Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana,

    ya fi ƙarfi in gane.

  25. 6 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina. 7 Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.”

    8 Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.”

    9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’? 10 Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa. 11 Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu.

  26. 28 Ya kuma ce wa mutum,

    ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima,

    kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”

  27. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

    7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;

    ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.

  28. 6 Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome,

    amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.

    7 Ka guji wawa,

    gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.

    8 Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu,

    amma wautar wawaye ruɗu ne.

  29. 25 A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. 26 I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi.

    27 “Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.

  30. 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.

    21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

  31. 33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!

    Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,

    hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!

    34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?

    Ko kuwa yă ba shi shawara?”

    35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,

    da Allah zai sāka masa?”

    36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.

    Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.

  32. 20 Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? 21 Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. 22 Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, 23 amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, 24 amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. 25 Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

  33. 28 “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba;

    za su neme ni amma ba za su same ni ba.

    29 Da yake sun ƙi sani

    ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

    30 da yake ba su karɓi shawarata ba

    suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

    31 za su sami sakayyar abubuwan da suka yi

    su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

    32 Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su,

    rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;

    33 amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya

    yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”

  34. Maganganu Masu Hikima

    17 Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima;

    ka yi amfani da abin da nake koyarwa,

    18 gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka

    ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka.

    19 Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji,

    ina koya maka yau, har kai ma.

    20 Ban rubuta maka maganganu talatin ba,

    maganganun shawara da sani,

    21 ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai,

    saboda ka iya ba da amsa daidai

    ga duk wanda ya aike ka?

  35. 20 Ya ce,

    “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin;

    hikima da iko nasa ne.

    21 Yana sāke lokuta,

    yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu.

    Yana ba da hikima ga masu hikima

    kuma ilimi ga masu basira.

    22 Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa;

    ya san abin da yake cikin dare,

    haske kuwa yana zaune tare da shi.

    23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.

    Kai ka san hikima da iko,

    ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”

  36. 1 Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani,

    amma duk mai ƙin gyara wawa ne.

  37. 6 Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,

    ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.

  38. 31 Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske. 32 Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”

  39. 9 Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Ba idon da ya taɓa gani,

    ba kunnen da ya taɓa ji,

    ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin

    abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

    10 Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.

    Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. 11 Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12 Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. 13 Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya. 14 Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.

  40. 18 Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”; 20 kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.”

  41. 29 Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku. 30 Hikimar Solomon ta fi hikimar mutanen Gabas, ta kuma fi dukan hikimar Masar girma. 31 Ya fi kowane mutum hikima, har da Etan dangin Ezra ma. Yana da hikima fiye da Heman, Kalkol da Darda, ’ya’yan Mahol maza. Sunansa ya bazu ko’ina a ƙasashen da suke kewaye. 32 Ya yi karin magana dubu uku. Waƙoƙinsa kuwa sun kai dubu ɗaya da biyar. 33 Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi. 34 Mutane suka yi ta zuwa daga ƙasashe dabam-dabam don su ji hikimar Solomon. Sarakuna daga ko’ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.

  42. 5 Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;

    kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.

    6 Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka;

    ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.

  43. 31 “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji,

    “sa’ad da zan yi sabon alkawari

    da gidan Isra’ila

    da kuma gidan Yahuda.

    32 Ba zai zama kamar alkawarin

    da na yi da kakanni kakanninsu ba

    sa’ad da na kama su da hannu

    na bishe su daga Masar,

    domin sun take alkawarina,

    ko da yake na zama miji a gare su,”

    in ji Ubangiji.

    33 “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila

    bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji.

    “Zan sa dokata a tunaninsu

    in kuma rubuta ta a zukatansu.

    Zan zama Allahnsu,

    za su kuma zama mutanena.

    34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,

    ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’

    domin duk za su san ni,

    daga ƙaraminsu har zuwa babba,”

    in ji Ubangiji.

    “Gama zan gafarta muguntarsu

    ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”

  44. 17 Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.

  45. 3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin. 4 Amma kai, Daniyel, ka rufe zancen nan ka kuma liƙe kalmomin littafin nan har sai ƙarshe. Mutane da yawa za su yi ta kai komo don neman sani.”

  46. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. 20 Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu.

  47. 15 Kuna shari’a bisa ga ma’aunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shari’a. 16 Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni. 17 A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce. 18 Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”

    19 Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?”

    Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.”

  48. 18 Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.

    A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin.

  49. 9 Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.

  50. 31 ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu, 32 don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla. 33 Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta. 34 Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu. 35 Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne.

  51. 22 “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci?

    Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku

    wawaye kuma ku ƙi ilimi?

  52. 10 Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa,

    sani a maimakon zinariya zalla,

  53. 11 gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja,

    kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita.

    12 “Ni, hikima, ina zama tare da hankali;

    ina da sani da iya rarrabewa.

    13 Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;

    ina ƙin girman kai da fariya,

    halin mugunta da kuma muguwar magana.

    14 Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne;

    ina da fahimi da kuma iko.

  54. 2 Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo,

    amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.

  55. 16 Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya,

    ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!

  56. 23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;

    ka nemi hikima, horo da fahimi.

  57. 10 Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi waɗannan?”

    Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi.

    11 Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne

    tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana.

    12 Hikima mafaka ce

    takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi.

    Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita

    ita ce amfanin ilimi.

  58. 1 Toho zai fito daga kututturen Yesse;

    daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.

    2 Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,

    Ruhun hikima da na fahimta,

    Ruhun shawara da na iko,

    Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,

  59. 16 Yesu ya amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni. 17 Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana. 18 Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.

  60. 1 In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai. 2 In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne.

  61. 14 Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu. 15 Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu. 16 A kan gicciye, Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo sulhu tsakaninmu da Allah. 17 Ya zo ya yi muku wa’azin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa. 18 Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda.

  62. 9 Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, 10 don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi,

  63. 6 Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci. 7 Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.

  64. 12 Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,

    don mu sami zuciyar hikima.

  65. 13 Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi,

    amma bulala domin bayan marasa azanci ne.

    14 Mai hikima kan yi ajiyar sani,

    amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.

  66. 33 Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima,

    kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.

  67. 13 Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau;

    zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka.

    14 Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai;

    in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka,

    kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.

  68. 5 Ubangiji da girma yake, gama yana zaune a bisa;

    zai cika Sihiyona cikin gaskiya da adalci.

    6 Zai zama tabbataccen harsashi na koyaushe,

    ma’ajin ceto da hikima da sani a yalwace;

    tsoron Ubangiji shi ne mabuɗin wannan dukiya.

  69. 23 To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa. 24 Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane. 25 Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.

  70. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.

  71. 3 Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4 wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya.

  72. 20 Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi, 21 wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya.

    Alheri yă kasance tare da ku.

  73. 1 ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2 Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.

    3 Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. 6 Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.

  74. 4 Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.

  75. 3 “Ka daina maganganu na girman kai

    ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai;

    gama Ubangiji Allah ne masani

    daga gare shi kuma ana auna ayyuka.

  76. 12 Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba?

    Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?

    13 “Allah ne mai iko da kuma hikima,

    shawara da ganewa nasa ne.

  77. 12 Amma a ina ne za a iya samun hikima?

    Ina fahimta take zama?

    13 Mutum bai gane muhimmancinta ba,

    ba a samunta a ƙasar masu rai.

    14 Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”;

    teku ya ce, “Ba ta wurina.”

    15 Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta,

    ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.

    16 Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir,

    ko sauran duwatsu masu daraja ba.

    17 Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba,

    ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.

  78. 21 “Idanunsa suna kan al’amuran mutane;

    yana ganin tafiyarsu duka.

  79. 7 Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima.

    Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.

  80. 10 Girmankai kan jawo faɗa ne kawai,

    amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.

  81. 7 Leɓunan masu hikima sukan baza sani;

    ba haka zukatan wawaye suke ba.

  82. 15 Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace,

    amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja.

  83. 24 Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne, 25 gama in ba tare da shi ba, wa zai iya ci yă sha yă kuma ji daɗi? 26 Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

  84. 13 Na kuma ga wani misali game da hikima a duniya wanda ya burge ni sosai. 14 An yi wani ɗan ƙaramin birni mai mutane kaɗan a ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani. 15 A cikin birnin nan kuwa akwai wani mutum matalauci amma mai hikima, ya kuma ceci birnin ta wurin hikimarsa. Amma ba wanda ya tuna da matalaucin nan. 16 Sai na ce, “Hikima ta fi ƙarfe ƙarfi.” Amma aka rena hikimar matalaucin, ba a ma jin maganarsa.

    17 Raɗar mai hikima da aka saurara cikin natsuwa

    ta fi ihun mai mulkin wawaye.

    18 Hikima ta fi kayan yaƙi,

    amma mai zunubi ɗaya yakan rushe alheri mai yawa.

  85. 9 Ba za su yi lahani ko su hallaka

    wani a dutsena mai tsarki ba,

    gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji

    kamar yadda ruwaye suka rufe teku.

  86. 5 “Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka,

    kafin a haife ka, na keɓe ka;

    na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”

  87. 23 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa

    ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa

    ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa,

    24 amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan,

    cewa ya fahimci ya kuma san ni,

    cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri,

    gaskiya da kuma adalci a duniya,

    gama a waɗannan ne nake jin daɗi,”

    in ji Ubangiji.

  88. 7 Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu. 8 Kada ku zama kamar su, gama Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.

  89. 22 Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ 23 Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’

    24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

  90. 17 Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe.

  91. 3 Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.

    4 Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne. 5 Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi. 6 Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.

    7 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci. 8 Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.