46 Bible Verses About Happiness
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.
-
8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;
jikina kuma zai zauna lafiya,
10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,
ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
11 Ka sanar da ni hanyar rai;
za ka cika ni da farin ciki a gabanka,
da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
-
12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14 In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.
-
3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;
yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji
zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
-
22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.
-
13 Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,
mutumin da ya sami fahimi,
14 gama ta fi azurfa riba
tana kuma da amfani fiye da zinariya.
15 Ta fi lu’ulu’u daraja;
ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.
16 Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama;
a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
17 Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi,
dukan hanyoyinta kuma salama ne.
18 Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta;
waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
-
12 Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu
za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su,
’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai
da sassaƙa don adon fada.
13 Rumbunanmu za su cika
da kowane irin tanadi.
Tumakinmu za su ƙaru ninki dubu,
ninki dubu goma-goma a filayenmu;
14 shanunmu za su ja kaya masu nauyi.
Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba,
ba zuwan zaman bauta,
ba jin kukan damuwa a titunanmu.
15 Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka;
masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji.
-
2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
-
9 Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya. 10 Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.
-
2 Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;
zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.
Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;
ya zama mai cetona.”
3 Da farin ciki zan ɗebo ruwa
daga rijiyoyin ceto.
4 A wannan rana za ku ce,
“Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,
a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.
5 Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa;
bari a sanar da wannan ga dukan duniya.
6 Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona,
gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”
-
9 “Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. 10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. 11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.
-
22 Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,
amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
-
13 Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske,
amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.
-
13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
-
6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.
-
Waƙar haurawa.
1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,
waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
2 Za ka ci amfanin aikinka;
albarku da wadata za su zama naka.
-
16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’
18 “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’
20 “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’
-
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
-
11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
-
5 In mutum bai daɗe da aure ba, kada a sa yă je yaƙi, ko yă yi wani aiki. Gama zai huta shekara guda a gida, yă faranta wa matar da ya aura rai.
-
17 “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure;
saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.
-
20 Da ya dubi almajiransa, sai ya ce,
“Masu albarka ne ku da kuke matalauta,
gama mulkin Allah naku ne.
21 Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,
gama za ku ƙoshi.
Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,
gama za ku yi dariya.
22 Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,
suka ware ku, suka zage ku,
suna ce da ku mugaye,
saboda Ɗan Mutum.
23 “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.
-
26 Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka.
Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!
2 Ka biya masa bukatar zuciyarsa
ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela
3 Ka marabce shi da yalwar albarka
ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.
4 Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi,
tsawo kwanaki, har abada abadin
5 Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce;
ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.
6 Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka
ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.
-
13 Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo,
kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki.
-
1 A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne.
-
15 Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari
waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji.
16 Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini;
suna samun ɗaukaka cikin adalcinka.
-
21 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
-
52 Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.
-
6 Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. 7 Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. 8 In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.
-
13 Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.
-
9 Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai mayar da ku masu arziki ƙwarai a cikin dukan aiki hannuwanku, da kuma cikin ’ya’yanku, da ’ya’yan shanunku, da kuma hatsin gonarku. Ubangiji zai sāke jin daɗinku yă sa ku yi arziki, kamar dai yadda ya ji daɗin kakanninku. 10 In dai kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnansa da ƙa’idodin da aka rubuta a wannan Littafin Doka, kuka juyo ga Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.
-
4 Sa’an nan zan tafi bagaden Allah,
ga Allah, farin cikina da murnata.
Zan yabe ka da garaya,
Ya Allah, Allahna.
5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?
Me ya sa ka damu a cikina?
Ka dogara ga Allah,
gama zai sāke yabe shi,
Mai Cetona da Allahna.
-
24 Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;
bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
-
2 Bakunanmu sun cika da dariya,
harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.
Sai ana faɗi a cikin al’ummai,
“Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”
-
10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;
raina yana farin ciki a cikin Allahna.
Gama ya suturce ni da rigunan ceto
ya yi mini ado da rigar adalci,
yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist
kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
-
10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. 11 Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.
-
22 Bari duk ra’ayin da kake da shi game da wannan sha’ani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba tă ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba. 23 Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.
-
9 Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku?
-
13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.
-
8 Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka!
-
6 Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”
Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.
7 Ka cika zuciyata da farin ciki
sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.
-
5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye
za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.
-
1 Na ce wa kaina, “Zo, zan gwada ka da jin daɗi don in ga abin da yake da kyau.” Amma wannan ma ya zama ba amfani.
-
19 Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne? 20 Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.
Shows Read in context, Share and Copy.