82 Bible Verses About Rejoicing
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
-
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
-
16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
19 Kada ku danne aikin Ruhu.
-
15 Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.
-
2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
-
3 Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali ya ce, 4 “In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba? 5 In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna, 6 ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’ 7 Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.
8 “Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba? 9 In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’ 10 Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”
-
6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.
-
10 Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,
gama mulkin sama nasu ne.
11 “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. 12 Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.
13 “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
-
20 Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21 Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya. 22 Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku. 23 A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana. 24 Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.
-
1 A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne.
-
11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.
-
22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.
-
13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
-
12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14 In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.
-
18 Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki.
I, zan kuwa ci gaba da farin ciki, 19 gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata.
-
9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;
jikina kuma zai zauna lafiya,
10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,
ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
11 Ka sanar da ni hanyar rai;
za ka cika ni da farin ciki a gabanka,
da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
-
13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. 14 Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, 15 gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.
-
19 Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku. 20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”
-
40 Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi.
41 Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan. 42 Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.
-
10 Nehemiya ya ce, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku.”
-
11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;
bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.
Ka buɗe kāriyarka a bisansu,
domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.
-
17 Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba,
ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi,
ko da yake zaitun bai ba da amfani ba,
gonaki kuma ba su ba da abinci ba,
ko da yake babu tumaki a garke,
ba kuma shanu a turaku,
18 duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,
zan yi murna da Allah Mai Cetona.
19 Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina;
yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa,
yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi.
Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.
-
17 Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,
-
1 Sai Hannatu ta yi addu’a ta ce,
“Zuciyata tana farin ciki a cikin Ubangiji;
a cikin Ubangiji an sa ina jin daɗi ƙwarai.
Na buɗe bakina na yi wa abokan gābana dariya.
Kai! Ina murna domin ka cece ni!
-
14 Ki rera, ya Diyar Sihiyona;
ki tā da murya, ya Isra’ila!
Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki,
Ya Diyar Urushalima!
15 Ubangiji ya ɗauke hukuncinki,
ya mai da abokan gābanki baya.
Ubangiji, Sarkin Isra’ila, yana tare da ke;
ba kuma za ki ƙara jin tsoron wani lahani ba.
16 A wannan rana za su cewa Urushalima,
“Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona;
kada ki bar hannuwanki su raunana.
17 Ubangiji Allahnki yana tare da ke,
mai iko ne don ceto.
Zai yi matuƙar farin ciki da ke,
zai rufe ki da ƙaunarsa,
zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”
-
3 Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku. 4 A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum 5 saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, 6 da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.
-
23 Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba; 24 amma ya fi muku muhimmanci in rayu cikin jiki. 25 Na tabbata haka ne, na kuwa san zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku farin ciki, 26 domin ta wurin kasancewata tare da ku, farin cikinku cikin Kiristi Yesu zai cika sosai ta dalilina.
-
1 Saboda haka ’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!
-
10 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
-
15 Ka gane, ya Ubangiji;
ka tuna da ni ka kuma lura da ni.
Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini.
Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni;
ka tuna yadda na sha zagi saboda kai.
16 Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su;
suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna,
gama ana kirana da sunanka,
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.
-
52 Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.
-
7 Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.
-
11 An haskaka haske a kan masu adalci
da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.
12 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci,
ku kuma yabi sunansa mai tsarki.
-
46 Sai Maryamu ta ce,
“Raina yana ɗaukaka Ubangiji
47 ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
48 gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.
Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,
sunansa labudda Mai Tsarki ne.
-
4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.
-
1 In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, 2 to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa.
-
17 Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku. 18 Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu. 19 Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne? 20 Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.
-
1 Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2 Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. 3 Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.
-
6 Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.
-
2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
-
11 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai;
ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!
-
4 Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,
ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;
sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,
shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
-
18 Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,
bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.
19 Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,
bari mamanta su ishe ka kullum,
bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.
-
10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.
-
12 Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.
-
24 Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.
-
31 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”
32 Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri;
bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!
33 Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,
za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji,
gama ya zo don yă hukunta duniya.
34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
ƙaunarsa madawwamiya ce.
35 Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;
tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai,
don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki,
don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”
-
6 Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”
Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.
7 Ka cika zuciyata da farin ciki
sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.
8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,
gama kai kaɗai, ya Ubangiji,
kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.
-
8 Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,
suna ba da farin ciki ga zuciya.
Umarnan Ubangiji haske ne
suna ba da haske ga idanu.
-
5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne
amma alherinsa har matuƙa ne;
mai yiwuwa a yi kuka da dare
amma farin ciki kan zo da safe.
-
1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;
daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
2 Ku yabi Ubangiji da garaya;
ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
3 Ku rera masa sabuwar waƙa;
ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
-
22 Zabura Dutsen da magina suka ƙi
ya zama mai amfani;
23 Ubangiji ne ya yi haka,
kuma abu mai daraja ne a idanunmu.
24 Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;
bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
-
9 A wannan rana za su ce,
“Tabbatacce wannan shi ne Allah;
mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu.
Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi;
bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”
-
10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;
raina yana farin ciki a cikin Allahna.
Gama ya suturce ni da rigunan ceto
ya yi mini ado da rigar adalci,
yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist
kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
-
13 “Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu.
-
38 Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma. 39 Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.
-
23 Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau. 24 Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.
25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. 26 Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.
-
26 In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.
-
3 Na yi farin ciki ƙwarai sa’ad da waɗansu ’yan’uwa suka zo suka yi zance game da yadda kake da aminci ga gaskiyan nan da kuma yadda kake cin gaba cikin gaskiyan nan. 4 Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.
-
7 Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna
mu kuma ɗaukaka shi!
Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi,
amaryarsa kuwa ta shirya kanta.
-
9 Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa. 10 “Yabo ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da na Fir’auna, wanda kuma ya cece mutanensa daga hannun Masarawa. 11 Yanzu na san cewa Ubangiji ya fi kowane allah, gama ya yi wannan ga masu girman kai da kuma waɗanda suka wulaƙanta Isra’ila.”
-
41 “Yanzu ka tashi, ya Ubangiji Allah, ka zo wurin hutunka,
kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.
Bari firistocinka, ya Ubangiji Allah, su sanye ceto,
bari tsarkakanka su yi farin ciki cikin alherinka.
-
7 Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi,
zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi.
’Ya’yansu za su gani su yi murna;
zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.
-
10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai.
-
33 A wannan sa’a na daren, mai gadin kurkukun ya ɗauke su ya wanke musu raunukansu; nan take aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa. 34 Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don yă gaskata da Allah, shi da dukan iyalinsa.
-
11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
-
6 Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar. 7 Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya.
-
9 Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku? 10 Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.
-
7 A can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku da iyalanku za su ci, su kuma yi farin ciki a kome da kuka sa hannunku a kai, domin Ubangiji Allahnku zai albarkace ku.
-
19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,
ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.
-
11 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;
12 bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.
Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;
13 za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,
yana zuwa don yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya cikin adalci
mutane kuma cikin amincinsa.
-
Zabura ce. Don yin godiya.
1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.
-
14 Na yi farin ciki da bin farillanka
yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.
-
24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;
duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.
25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna;
bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!
-
19 Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah. 20 Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki.
-
2 Mutanen da suke tafiya cikin duhu
sun ga babban haske;
a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa
haske ya haskaka.
3 Ka fadada al’umma
ka kuma ƙara farin cikinsu;
suna farin ciki a gabanka
yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi,
kamar yadda mutane sukan yi farin ciki
sa’ad da suke raba ganima.
4 Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi,
kuka ji tsoro
nauyin da ya nawaita musu,
sandar da yake a kafaɗunsu,
sandar masu zaluncinsu.
5 Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi
da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini
zai kasance an ƙone shi
zai kuma zama abin hura wuta.
6 Gama a gare mu an haifa mana yaro,
a gare mu an ba da ɗa,
gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa.
Za a ce da shi
Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki
Uban Madawwami, Sarkin Salama.
7 Game da girmar gwamnatinsa da salama
babu iyaka.
Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa,
zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,
tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.
Ubangiji Maɗaukaki ne
ya yi niyyar aikata wannan duka.
-
10 Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke
saukowa daga sama,
ba sa komowa
ba tare da sun jiƙe duniya
sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho,
don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,
11 haka maganata da take fitowa daga bakina.
Ba za tă koma gare ni wofi ba,
amma za tă cika abin da nake so
ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.
12 Za ku fita da farin ciki
a kuma bi da ku da salama;
duwatsu da tuddai
za su ɓarke da waƙa a gabanku,
dukan itatuwan jeji kuma
za su tafa hannuwansu.
13 A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro,
a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro.
Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi,
madawwamiyar alama ce,
wadda ba za a datse ba.”
-
57 Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. 58 Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.
-
29 Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu. 30 Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
-
17 Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.
-
12 Ina da abubuwa da dama da zan rubuta muku, sai dai ba na so in yi amfani da takarda da inki in rubuta. A maimako, ina fata in ziyarce ku in kuma yi magana da ku fuska da fuska, domin farin cikinmu yă zama cikakke.
Shows Read in context, Share and Copy.