74 Bible Verses About God's Protection

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About God's Protection
  1. 1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka

    zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

    2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,

    Allahna, wanda nake dogara.”

    3 Tabbatacce zai cece ka

    daga tarkon mai farauta

    da kuma daga cututtuka masu kisa.

    4 Zai rufe ka da fikafikansa,

    a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;

    amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

    5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,

    ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,

    6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,

    ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.

    7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,

    dubu goma a hannun damanka,

    amma ba abin da zai zo kusa da kai.

    8 Za ka dai gan da idanunka

    yadda ake hukunta mugaye.

    9 In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka,

    har ma Ubangiji wanda yake mafakata,

    10 to, babu wani mugun abin da zai same ka,

    ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.

    11 Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai

    don su tsare ka a dukan hanyoyinka;

    12 za su tallafe ka da hannuwansu,

    don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.

  2. Waƙar haurawa.

    1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,

    ta ina ne taimakona zai zo?

    2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,

    wanda ya kafa sama da ƙasa.

    3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,

    shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

    4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila

    ba ya gyangyaɗi ko barci.

    5 Ubangiji yana tsaronka,

    Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;

    6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba

    balle wata da dare.

    7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,

    zai tsare ranka;

    8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka

    yanzu da har abada kuma.

  3. 1 A ƙarshe, ’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku. 2 Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya. 3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan. 4 Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta. 5 Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.

    1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

    kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

    2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza

    duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

    3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa

    duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

    4 Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna,

    tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.

    5 Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba;

    Allah zai taimake ta da safe.

    6 Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi;

    ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.

    7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;

    Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

    8 Zo ku ga ayyukan Ubangiji,

    kangon da ya kawo a kan duniya.

    9 Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit

    ko’ina a duniya.

    Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu,

    ya ƙone garkuwoyi da wuta.

    10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;

    za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,

    za a ɗaukaka ni cikin duniya.”

    11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;

    Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

  5. 10 Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;

    masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.

  6. 10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

    kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

    Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

    zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

    11 “Duk wanda ya yi fushi da kai

    tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;

    waɗanda suka yi hamayya da kai

    za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.

    12 Ko ka nemi abokan gābanka,

    ba za ka same su ba.

    Waɗanda suke yaƙi da kai

    za su zama kamar ba kome ba.

    13 Gama ni ne Ubangiji Allahnka,

    wanda ya riƙe ka da hannun damana

    ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;

    zan taimake ka.

  7. 10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

    18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. 19 Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, 20 wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.

  8. 3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;

    ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

    4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,

    ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

    5 Na kwanta na yi barci;

    na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

  9. 6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”

  10. 11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;

    bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.

    Ka buɗe kāriyarka a bisansu,

    domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.

  11. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Ya rera ta ga Ubangiji kalmomin wannan waƙa sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu, ya ce,

    1 Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.

    2 Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;

    Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka.

    Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.

  12. 7 Kai ne wurin ɓuyata;

    za ka tsare ni daga wahala

    ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela

  13. 28 Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29 Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. 30 Da ni da Uba ɗaya ne.”

  14. 13 Musa ya amsa wa mutane ya ce, “Kada ku ji tsoro. Ku tsaya dai ku ga ceton da Ubangiji zai kawo muku yau. Masarawan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba. 14 Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum.”

  15. 7 Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki,

    kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu

    da hannunka na dama.

    8 Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido;

    ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka

    9 daga mugaye waɗanda suke kai mini hari,

    daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.

    10 Sun rufe zukatansu marar tausayi,

    da bakunansu suna magana da fariya.

  16. 7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,

    ya kuwa cece su.

    8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;

    mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

    9 Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,

    gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.

  17. 16 Amma zan rera game da ƙarfinka,

    da safe zan rera game da ƙaunarka;

    gama kai ne mafakata,

    kagarata a lokacin wahala.

    17 Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;

    kai, ya Allah, kai ne kagarata,

    Allah mai ƙaunata.

  18. 17 ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara,

    za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki.

    Wannan ne gādon bayin Ubangiji,

    kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,”

    in ji Ubangiji.

  19. 13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

  20. 16 A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

  21. 3 Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya

    shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona.

    Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona.

    Daga mutane masu fitina, ka cece ni.

    4 “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,

    na kuwa tsira daga abokan gābana.

  22. 30 Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce;

    maganar Ubangiji marar kuskure ne.

    Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi.

    31 Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba?

    Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba?

    32 Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi

    ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya.

  23. 1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,

    shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,

    shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,

    “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;

    na kira ka da suna; kai nawa ne.

    2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,

    zan kasance tare da ku;

    sa’ad da kuka bi ta koguna,

    ba za su kwashe ku ba.

    Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,

    ba za tă ƙone ku ba;

    harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.

    3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;

    na bayar da Masar don fansa,

    Kush da Seba a maimakonku.

  24. 23 Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 24 Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.

  25. 17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;

    yakan cece su daga dukan wahalarsu.

    18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai

    ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

    19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,

    amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

    20 yakan tsare dukan ƙasusuwansa,

    ba ko ɗayansu da zai karye.

  26. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo.

    1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai,

    gama a gare ka raina yake samun mafaka.

    Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka

    sai masifar ta wuce.

  27. 6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai yi mini?

    7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.

    Zan yi nasara a kan abokan gābana.

    8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

    da in dogara ga mutum.

    9 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

    da in dogara ga sarakuna.

  28. 24 sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;

    sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.

    25 Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya

    ko lalacin da yakan auka wa mugaye,

    26 gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka

    zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.

  29. 114 Kai ne mafakata da garkuwata;

    na sa zuciyata a maganarka.

  30. 7 Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala,

    kana kiyaye raina;

    ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana,

    da hannunka na dama ka cece ni.

  31. 7 Ubangiji nagari ne,

    mafaka kuma a lokacin wahala.

    Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,

  32. 31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba? 33 Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa.

  33. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

    “Ba zan taɓa bar ka ba;

    ba zan taɓa yashe ka ba.”

    6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

    “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai iya yi mini?”

  34. Miktam ne na Dawuda.

    1 Ka kiyaye ni, ya Allah,

    gama a cikinka nake samun mafaka.

    2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana;

    in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”

  35. 2 Shi kaɗai ne dutsena da cetona;

    shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

  36. 32 Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba?

    Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?

  37. 9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,

    mafaka a lokutan wahala.

  38. 3 Allah yana cikin fadodinta;

    ya nuna kansa mafaka ce gare ta.

  39. 7 Domin kai ne mai taimakona,

    ina rera a cikin inuwar fikafikanka.

    8 Raina ya manne maka;

    hannunka na dama yana riƙe da ni.

    9 Su da suke neman raina za su hallaka;

    za su gangara zuwa zurfafan duniya.

  40. 4 Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura

    ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.

    Na yi ku zan kuma riƙe ku;

    zan lura da ku

    in kuma kuɓutar da ku.

  41. 24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.

  42. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

    2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,

    yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

    3 yakan maido da raina.

    Yakan bi da ni a hanyoyin adalci

    saboda sunansa.

    4 Ko da na yi tafiya

    ta kwari na inuwar mutuwa,

    ba zan ji tsoron mugu ba,

    gama kana tare da ni;

    bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

    za su yi mini ta’aziyya.

    5 Ka shirya mini tebur

    a gaban abokan gābana.

    Ka shafe kaina da mai;

    kwaf nawa ya cika har yana zuba.

    6 Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi

    dukan kwanakin raina,

    zan kuwa zauna a gidan Ubangiji

    har abada.

  43. Ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne haskena da cetona,

    wa zan ji tsoro?

    Ubangiji ne mafakar raina,

    wane ne zan ji tsoro?

  44. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.

    1 Ka ji kukata, ya Allah;

    ka saurari addu’ata.

    2 Daga iyakar duniya na yi kira gare ka,

    na yi kira yayinda zuciyata ta karai;

    ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.

    3 Gama kai ne mafakata,

    hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.

    4 Ina marmari in zauna a tentinka har abada

    in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela

  45. 7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

  46. 15 Ina tare da kai, zan lura da kai duk inda ka tafi, zan kuma dawo da kai zuwa wannan ƙasa. Ba zan rabu da kai ba sai na cika abin da na yi maka alkawari.”

  47. 5 Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

  48. 35 Ka ba ni garkuwar nasara,

    kuma hannunka na dama yana riƙe ni;

    ya sunkuya don ka mai da ni mai girma.

    36 Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina,

    don kada ɗiɗɗigena yă juya.

  49. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

    1 A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka;

    kada ka bari in taɓa shan kunya;

    ka cece ni cikin rahamarka.

    2 Ka juye kunnenka gare ni,

    ka zo da sauri ka cece ni;

    ka zama dutsen mafakata,

    mafaka mai ƙarfi na cetona.

    3 Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata,

    saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.

  50. 22 Ubangiji yakan cece bayinsa;

    ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.

  51. 7 Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,

    shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.

    8 Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;

    ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,

    gama Allah ne mafakarmu. Sela

  52. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  53. 10 Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya.

  54. 7 Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya;

    yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.

  55. 8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,

    gama kai kaɗai, ya Ubangiji,

    kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

  56. 8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

    Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

  57. 23 In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi,

    zai sa sawu su kahu;

    24 ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba,

    gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.

  58. 11 Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;

    bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.

    12 Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni;

    zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani.

    Sun fi gashin kaina yawa,

    har ma na fid da zuciya.

    13 Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji;

    Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.

  59. Waƙar haurawa. Ta Solomon.

    1 In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,

    masu gininta suna wahala a banza ne.

    In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,

    masu tsaro suna yin tsaro a banza.

  60. 33 amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya

    yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”

  61. 22 Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.”

    23 Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.

  62. 1 Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa,

    “Kada ka ji tsoro, Abram.

    Ni ne garkuwarka,

    kuma ladanka zai zama mai girma.”

  63. 9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

  64. 45 Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.

  65. 11 Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”

  66. 3 Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

    4 Ga Allah wanda maganarsa nake yabo

    ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

  67. 22 Amma Ubangiji ya zama kagarata,

    Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.

  68. 4 Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye;

    ka tsare ni daga mutane masu rikici

    waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.

  69. Ta Dawuda.

    1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena,

    wanda ya horar da hannuwana don yaƙi,

    yatsotsina don faɗa.

    2 Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata,

    katangata da mai cetona,

    garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi,

    wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.

  70. 26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,

    kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.

  71. 5 “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure;

    shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.

  72. 7 Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni,

    ba zan sha kunya ba.

    Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara,

    na kuma sani ba zan sha kunya ba.

  73. 19 Ya Ubangiji, ƙarfina da katangana,

    mafakata a lokacin damuwa,

    gare ka al’ummai za su zo

    daga iyakokin duniya su ce,

    “Kakanninmu ba su mallaki kome ba sai allolin ƙarya,

    gumakan banza da ba su yi musu amfani ba.

  74. 10 Sai ya ce musu, “Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki zai tasar wa mulki. 11 Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.

    12 “Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana. 13 Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su. 14 Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku. 15 Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata. 16 Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku. 17 Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. 18 Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. 19 Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.