30 Bible Verses About Heartbreak
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,
amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;
20 yakan tsare dukan ƙasusuwansa,
ba ko ɗayansu da zai karye.
-
2 Ubangiji ya gina Urushalima;
ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.
3 Ya warkar da masu raunanar zuciya
ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
4 Ya lissafta yawan taurari
ya kuma kira kowannensu da suna.
5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;
ganewarsa ba shi da iyaka.
6 Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai
yakan yar da mugaye a ƙasa.
-
3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”
-
27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
-
22 Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya
yă kuma adana ƙasusuwanka.
-
28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
-
26 Jikina da zuciyata za su iya raunana,
amma Allah ne ƙarfin zuciyata
da kuma rabona har abada.
-
7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
-
33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
-
20 Ko da yake ka sa na ga wahaloli,
masu yawa da kuma masu ɗaci,
za ka sāke mayar mini da rai;
daga zurfafan duniya
za ka sāke tā da ni.
-
12 Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo,
amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
13 Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa,
amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.
14 Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne,
mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
15 Fahimta mai kyau kan sami tagomashi,
amma hanyar marar aminci tana da wuya.
16 Kowane mai azanci yakan nuna sani,
amma wawa yakan yi tallen wawancinsa.
-
8 A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. 9 An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. 10 Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit. Ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka
ko ka hore ni cikin hasalarka.
2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma;
Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
3 Raina yana cikin wahala.
Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?
4 Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni;
ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
5 Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu.
Wa ke yabonka daga kabari?
6 Na gaji tiƙis daga nishi.
Dukan dare na jiƙe gadona da kuka
na jiƙe kujerata da hawaye.
7 Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki;
sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.
-
1 Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,
domin Ubangiji ya shafe ni
domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.
Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,
don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru
in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu
-
6 “Saboda ka yi nishi, ɗan mutum! Yi nishi a gabansu da ajiyar zuciya da ɓacin rai.
-
10 kuma fansassu na Ubangiji za su komo.
Za su shiga Sihiyona da rerawa;
matuƙar farin ciki zai mamaye su.
Murna da farin ciki za su sha kansu,
baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.
-
21 Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”
22 Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.
-
33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. 34 Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?”
Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”
35 Yesu ya yi kuka.
-
20 Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21 Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya. 22 Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku.
-
18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba.
-
9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.
-
5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne
amma alherinsa har matuƙa ne;
mai yiwuwa a yi kuka da dare
amma farin ciki kan zo da safe.
-
18 “Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru;
kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce.
19 Duba, ina yi abu sabo!
Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba?
Ina yin hanya a cikin hamada
rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.
-
4 Masu albarka ne waɗanda suke makoki,
gama za a yi musu ta’aziyya.
-
18 “Ruhun Ubangiji yana kaina,
domin ya shafe ni,
in yi wa matalauta wa’azin bishara.
Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku,
in kuma buɗe idanun makafi,
in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.
-
4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.
8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.
-
6 Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. 7 Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba.
Shows Read in context, Share and Copy.