58 Bible Verses About Gratitude
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
-
15 Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.
16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
-
12 Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa. 13 Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya. 14 An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.
15 Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu. 16 Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. 17 Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.
-
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
2 Ku yi godiya ga Allahn alloli.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
3 Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
4 Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
5 Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
-
10 To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. 11 Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
12 Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. 13 Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. 14 A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. 15 Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!
-
6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.
-
1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2 Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,
babban Sarki a bisa dukan alloli.
4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,
ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,
da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,
bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
-
Ta Dawuda.
1 Yabi Ubangiji, ya raina;
dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
2 Yabi Ubangiji, ya raina,
kada kuma ka manta dukan alheransa,
3 wanda yake gafarta dukan zunubai
yake kuma warkar da dukan cututtuka,
4 wanda ya fanshi ranka daga rami
ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau
domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
-
6 To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa, 7 ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.
-
12 Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, 13 suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”
14 Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.
15 Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. 16 Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
17 Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? 18 Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?”
-
2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;
ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.
3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.
Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;
mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.
4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya
filayen gidansa kuma da yabo;
ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;
amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.
-
2 Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya. 3 Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi.
-
15 Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.
16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. 17 Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.
-
56 Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. 57 Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
58 Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
-
17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
-
14 Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.
15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. 16 Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
-
LITTAFI NA BIYAR
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
2 Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan,
su da aka fansa daga hannun maƙiyi,
3 su da ya tattara daga ƙasashe,
daga gabas da yamma, daga arewa da kudu.
-
34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
15 Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah, 16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa.
-
7 A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.
8 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
9 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.
10 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
11 Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
-
4 Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu. 5 Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku
-
1 Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum 2 da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3 Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4 wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda.
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
-
14 “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah,
ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,
15 ku kira gare ni a ranar wahala;
zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”
-
30 Zan yabe sunan Allah cikin waƙa
in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
31 Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya,
fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
32 Matalauta za su gani su kuma yi murna,
ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!
-
14 Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina. 15 Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. 16 Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin?
-
6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya ji kukata na neman jinƙai.
7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
-
Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.
1 Yana da kyau a yabi Ubangiji
a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
2 don a yi shelar ƙaunarka da safe
amincinka kuma da dare,
-
23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.
Kai ka san hikima da iko,
ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”
-
9 Amma ni, da waƙar godiya,
zan miƙa tawa hadaya gare ka.
Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi.
Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”
-
3 Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa. 4 Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.
-
11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
-
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.
-
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;
ku kada garaya ga Allahnmu.
8 Ya rufe sararin sama da gizagizai;
yana tanada wa duniya ruwan sama
yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
9 Yakan tanada wa shanu abinci
da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.
-
41 Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42 Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”
-
6 Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah. 7 Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai.
-
16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, 17 suna cewa,
“Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,
domin ka karɓi ikonka mai girma
ka kuma fara mulki.
-
2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako
ka kuwa warkar da ni.
3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;
ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.
4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;
ku yabi sunansa mai tsarki.
5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne
amma alherinsa har matuƙa ne;
mai yiwuwa a yi kuka da dare
amma farin ciki kan zo da safe.
-
18 Zan yi godiya cikin taro mai girma;
cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.
-
1 Yabi Ubangiji.
Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
-
8 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
9 gama yana shayar da masu ƙishirwa
yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.
-
24 Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;
bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
-
21 Duk da haka na tuna da wannan
na kuma sa bege ga nan gaba.
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;
saboda haka zan jira shi.”
25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,
ga kuma wanda yake neman shi;
-
1 Bulus, Sila da Timoti,
Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi.
Alheri da salama su kasance tare da ku.
2 Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu. 3 Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.
-
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
-
3 Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku. 4 Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka. 5 Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar 6 da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta.
-
11 Girma da iko
da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji,
gama kome a sama da ƙasa naka ne.
Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji;
an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
12 Wadata da girma daga gare ka suke;
kai ne mai mulkin dukan abubuwa.
A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke
don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.
13 Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka,
muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.
14 “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.
-
17 Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa
zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.
-
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
2 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
3 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
-
Ta Dawuda.
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
a gaban “alloli” zan rera yabo.
2 Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki
zan kuma yabi sunanka
saboda ƙaunarka da amincinka,
saboda ka ɗaukaka a bisa kome
sunanka da kuma maganarka.
3 Sa’ad da na kira, ka amsa mini;
ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.
4 Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji,
sa’ad da suka ji maganganun bakinka.
5 Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji,
gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.
-
35 Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci.
-
4 Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina, 5 domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.
-
17 Zan yi hadayar godiya gare ka
in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
-
13 Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.
-
6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.
-
11 Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12 suna cewa,
“Amin!
Yabo da ɗaukaka,
da hikima da godiya da girma
da iko da ƙarfi
sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.
Amin!”
Shows Read in context, Share and Copy.