77 Bible Verses About Giving Thanks
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
15 Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.
16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
-
15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
-
10 To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. 11 Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
12 Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. 13 Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. 14 A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. 15 Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!
-
2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;
ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.
3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.
Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;
mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.
4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya
filayen gidansa kuma da yabo;
ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;
amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.
-
4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
-
15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.
-
1 Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,
2 Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ’yan’uwa cikin Kiristi da suke a Kolossi.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu, su kasance tare da ku.
3 Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku. 4 Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka. 5 Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar 6 da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta. 7 Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu, 8 wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.
9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. 11 Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki 12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. 13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.
-
1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2 Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,
babban Sarki a bisa dukan alloli.
4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,
ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,
da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
-
14 Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.
15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. 16 Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
-
30 Zan yabe sunan Allah cikin waƙa
in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
31 Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya,
fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
-
1 Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. 2 Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca. 3 Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. 4 Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, 5 domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.
-
14 “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah,
ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,
15 ku kira gare ni a ranar wahala;
zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”
-
13 A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana. 14 Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku. 15 Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.
-
2 Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya.
-
4 Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu. 5 Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku 6 gama shaidarmu game da Kiristi ta tabbata a cikinku. 7 Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 8 Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9 Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.
-
1 Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum 2 da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3 Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4 wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya.
-
6 To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa, 7 ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.
-
10 Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa,
“Yabo gare ka, ya Ubangiji,
Allah na mahaifinmu Isra’ila,
har abada abadin.
11 Girma da iko
da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji,
gama kome a sama da ƙasa naka ne.
Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji;
an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
12 Wadata da girma daga gare ka suke;
kai ne mai mulkin dukan abubuwa.
A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke
don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.
13 Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka,
muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.
14 “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.
-
15 Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah, 16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19 Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan 20 da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21 Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. 22 Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. 23 Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.
-
34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta.
-
14 Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina. 15 Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. 16 Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin?
-
LITTAFI NA BIYAR
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
2 Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan,
su da aka fansa daga hannun maƙiyi,
3 su da ya tattara daga ƙasashe,
daga gabas da yamma, daga arewa da kudu.
-
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
2 Ku yi godiya ga Allahn alloli.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
3 Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
10 To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.
-
8 Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya.
-
57 Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
-
12 Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa. 13 Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya. 14 An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.
15 Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu. 16 Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. 17 Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.
-
9 Amma ni, da waƙar godiya,
zan miƙa tawa hadaya gare ka.
Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi.
Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”
-
16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, 17 suna cewa,
“Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,
domin ka karɓi ikonka mai girma
ka kuma fara mulki.
-
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;
ku kada garaya ga Allahnmu.
8 Ya rufe sararin sama da gizagizai;
yana tanada wa duniya ruwan sama
yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
9 Yakan tanada wa shanu abinci
da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.
-
23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.
Kai ka san hikima da iko,
ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”
-
3 Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. 4 Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.
-
9 Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. 10 Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,
“Ceto na Allahnmu ne,
wanda yake zaune a bisan kursiyi,
da kuma na Ɗan Ragon.”
11 Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12 suna cewa,
“Amin!
Yabo da ɗaukaka,
da hikima da godiya da girma
da iko da ƙarfi
sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.
Amin!”
13 Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?”
14 Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.”
Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.
-
1 Bulus, Sila da Timoti,
Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi.
Alheri da salama su kasance tare da ku.
2 Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu. 3 Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.
4 Gama mun sani, ’yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku, 5 domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku.
-
8 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
9 gama yana shayar da masu ƙishirwa
yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.
-
17 Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa
zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.
-
Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.
1 Yana da kyau a yabi Ubangiji
a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
2 don a yi shelar ƙaunarka da safe
amincinka kuma da dare,
3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma
da kuma ƙarar garaya.
-
11 Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
-
3 Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku. 4 A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum 5 saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, 6 da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.
7 Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina daure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni. 8 Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.
9 Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, 10 don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi, 11 cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.
-
3 Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa. 4 Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.
-
7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
-
18 Zan yi godiya cikin taro mai girma;
cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.
-
1 Yabi Ubangiji.
Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
-
17 Zan yi hadayar godiya gare ka
in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
-
11 Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili. 12 Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, 13 suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”
14 Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.
15 Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. 16 Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
17 Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? 18 Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?” 19 Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
-
7 A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.
8 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
9 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.
-
11 Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa,
“Shi nagari ne;
ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.”
Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.
-
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
2 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
3 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
-
26 Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”
27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28 Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.
-
1 Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba. 2 Bangaskiyar mutum ta yarda masa yă ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai. 3 Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yă rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yă ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi. 4 Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yă yi aiki mai kyau, ko yă kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
5 Wani yakan ɗauki wata rana da daraja fiye da sauran ranaku; wani kuma yana ganin dukan ranakun ɗaya ne. Ya kamata kowa yă kasance da tabbaci a cikin zuciyarsa. 6 Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah. 7 Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai.
-
17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
-
1 Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.” 2 Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa. 3 Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin. 4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu. 5 Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah. 6 Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi.
A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya. 7 Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama. 8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,
“ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki
shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’
wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”
9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, 10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,
11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,
ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,
domin ka halicci dukan abubuwa,
kuma ta wurin nufinka aka halicce su
suka kuma kasance.”
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda.
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
-
11 Ka mai da kukata ta zama rawa;
ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,
12 don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba.
Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.
-
17 Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. 18 An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.
-
21 Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22 Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23 amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24 Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25 Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu!
Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.
-
13 Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara. 14 Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba. 15 To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina. 16 A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba? 17 Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.
18 Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka. 19 Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.
-
1 Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu,
Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu, 2 zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.
3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
4 Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina, 5 domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka. 6 Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi. 7 Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.
-
4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;
ku yabi sunansa mai tsarki.
5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne
amma alherinsa har matuƙa ne;
mai yiwuwa a yi kuka da dare
amma farin ciki kan zo da safe.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Kada A Hallaka.” Zabura ta Asaf. Waƙa ce.
1 Muna maka godiya, ya Allah,
muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa;
mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.
-
Ta Dawuda.
1 Yabi Ubangiji, ya raina;
dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
2 Yabi Ubangiji, ya raina,
kada kuma ka manta dukan alheransa,
3 wanda yake gafarta dukan zunubai
yake kuma warkar da dukan cututtuka,
4 wanda ya fanshi ranka daga rami
ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau
domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. 7 A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8 wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. 10 Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.
11 A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi. 12 Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah. 13 An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. 14 Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.
-
3 Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona
zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta;
zai sa hamadanta ta zama kamar Eden,
ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji.
Za a sami farin ciki da murna a cikinta,
godiya da ƙarar rerawa.
-
21 Duk da haka na tuna da wannan
na kuma sa bege ga nan gaba.
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;
saboda haka zan jira shi.”
-
13 Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.
-
Ta Dawuda.
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
a gaban “alloli” zan rera yabo.
2 Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki
zan kuma yabi sunanka
saboda ƙaunarka da amincinka,
saboda ka ɗaukaka a bisa kome
sunanka da kuma maganarka.
3 Sa’ad da na kira, ka amsa mini;
ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.
4 Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji,
sa’ad da suka ji maganganun bakinka.
5 Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji,
gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.
-
19 Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane.
-
30 In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?
31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
-
23 Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni,
ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”
-
21 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
22 Bari su miƙa hadaya ta godiya
su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.
-
49 Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji;
zan rera yabai ga sunanka.
-
1 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
-
28 Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya;
kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.
29 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
-
4 A wannan rana za ku ce,
“Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,
a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.
5 Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa;
bari a sanar da wannan ga dukan duniya.
-
12 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci,
ku kuma yabi sunansa mai tsarki.
-
9 Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane ya ce, 10 “Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. 11 Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. 12 Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’
13 “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’
14 “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
Shows Read in context, Share and Copy.