48 Bible Verses About God's Holiness

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About God's Holiness
  1. 13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; 16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”

    17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18 Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19 sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.

    22 Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya. 23 Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. 24 Gama,

    “Dukan mutane kamar ciyawa suke,

    darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;

    ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,

    25 amma maganar Ubangiji tana nan har abada.”

    Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

  2. 1 A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. 2 A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. 3 Suna kiran juna,

    “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;

    duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

    4 Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.

  3. 11 Wane ne cikin alloli,

    ya yi kamar ka, ya Ubangiji?

    Wane ne kamar ka,

    mai ɗaukaka cikin tsarki,

    mai banrazana cikin ɗaukaka,

    mai aikata al’ajabai?

    12 “Ka miƙa hannunka na dama,

    ƙasa ta haɗiye abokan gābanka.

    13 A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe

    mutanen da ka fansa.

    A cikin ƙarfinka, za ka bishe su

    zuwa mazauninka mai tsarki.

  4. 1 Sai Hannatu ta yi addu’a ta ce,

    “Zuciyata tana farin ciki a cikin Ubangiji;

    a cikin Ubangiji an sa ina jin daɗi ƙwarai.

    Na buɗe bakina na yi wa abokan gābana dariya.

    Kai! Ina murna domin ka cece ni!

    2 “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji

    babu wani, in ban da kai;

    babu wani dutse kamar Allahnmu.

  5. 44 Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa. 45 Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne.

    46 “ ‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa. 47 Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’ ”

  6. 2 “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.

  7. 3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,

    “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,

    ya Ubangiji Maɗaukaki.

    Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,

    ya Sarkin zamanai.

    4 Wane ne ba zai ji tsoronka,

    yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?

    Gama kai kaɗai ne mai tsarki.

    Dukan al’ummai za su zo

    su yi sujada a gabanka,

    gama an bayyana ayyukan adalcinka.”

  8. 1 Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.” 2 Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa. 3 Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin. 4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu. 5 Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah. 6 Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi.

    A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya. 7 Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama. 8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,

    “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki

    shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’

    wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”

  9. 15 Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa

    wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne,

    “Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri,

    amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu,

    don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u

    in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.

  10. 5 Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu

    ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa;

    shi mai tsarki ne.

  11. 9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  12. 1 Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba. 2 Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. 3 Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.

    4 Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne. 5 Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi. 6 Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.

    7 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci. 8 Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis. 9 Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah. 10 Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

  13. 43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

  14. 25 “Ga wa za ku kwatanta ni?

    Ko kuwa wa yake daidai da ni?” In ji Mai Tsarkin nan.

  15. 5 Allah ya ce, “Kada ka zo kusa, tuɓe takalmanka, gama inda kake tsaye, wuri ne mai tsarki.”

  16. 8 Allah yana mulki a bisa al’ummai;

    Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.

  17. Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza.

    1 Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo,

    a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.

  18. 21 Na damu saboda sunana mai tsarki, wanda gidan Isra’ila ya ɓata a cikin al’ummai inda suka tafi.

    22 “Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba dominku ba ne, ya gidan Isra’ila da nake yin waɗannan abubuwa, amma saboda sunana ne mai tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al’ummai inda kuka tafi. 23 Zan nuna tsarkin girman sunana, wanda aka ɓata a cikin al’umma, sunana da kuka ɓata a cikinsu. Sa’an nan al’ummai za su san cewa ni ne Ubangiji, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinku a idanunsu.

  19. 49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,

    sunansa labudda Mai Tsarki ne.

  20. 29 ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa.

    Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa;

    ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.

  21. 3 Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan;

    kai ne yabon Isra’ila.

  22. Ta Dawuda.

    1 Yabi Ubangiji, ya raina;

    dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

  23. 26 Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama. 27 Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa. 28 Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.

  24. 26 Ku zama tsarkakakke gare ni, gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, na kuma keɓe ku daga al’ummai don ku zama nawa.

  25. 19 Yoshuwa ya ce wa mutanen, “Ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba gama shi Allah mai tsarki ne; mai kishi kuma. Ba zai gafarta muku zunubin tawaye ba. 20 In kuka juya wa Ubangiji baya, kuka bauta wa waɗansu alloli, zai juya yă kawo muku bala’i, yă hallaka ku, yă kawo ƙarshenku.”

  26. 3 Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?

    Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

    4 Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,

    wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki

    ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

    5 Zai sami albarka daga Ubangiji

    da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

  27. 9 Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;

    ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.

  28. 35 Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina,

    ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,

  29. 8 Kuma babbar hanya za tă kasance a can;

    za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki.

    Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba;

    za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce;

    mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.

  30. 15 Ni ne Ubangiji, Mai Tsarkin nan,

    Mahaliccin Isra’ila, Sarkinku.”

  31. 5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan.

  32. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?

    Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

  33. 12 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci,

    ku kuma yabi sunansa mai tsarki.

  34. 1 Ubangiji yana mulki,

    bari al’ummai su yi rawan jiki;

    yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi,

    bari duniya ta girgiza.

    2 Ubangiji mai girma yana a Sihiyona;

    an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai.

    3 Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana,

    shi mai tsarki ne.

  35. 19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

  36. 6 Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki.

    7 “ ‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu. 8 An ɗauke su da tsarki, domin suna miƙa abincin Allahnku. An ɗauka su masu tsarki gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, Ni wanda ya mai da ku masu tsarki.

  37. 4 Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;

    Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.

    Yana kallon ’ya’yan mutane;

    idanunsa suna bincike su.

  38. 22 Zan yabe ka da garaya

    saboda amincinka, ya Allah;

    zan rera yabo gare ka da molo,

    Ya Mai Tsarki na Isra’ila.

  39. 32 Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole Isra’ilawa su gane Ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji, wanda ya keɓe ku a matsayin tsarkaka

  40. 10 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki

    bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.

  41. 10 Da sai in ji daɗi

    duk zafin da nake sha

    ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.

  42. 21 A cikinsa zukatanmu na farin ciki,

    gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.

  43. 41 Sau da sau suka riƙa gwada Allah;

    suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila.

  44. 16 Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya,

    kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.

  45. 14 Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi,

    ya ƙaramin Isra’ila,

    gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji,

    Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  46. 15 Ka duba daga sama ka gani

    daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka.

    Ina kishinka da kuma ikonka?

    Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu.

  47. 20 Amma Ubangiji yana a cikin haikalinsa mai tsarki;

    bari dukan duniya tă yi shiru a gabansa.

  48. 13 Ku yi tsit a gaban Ubangiji, dukanku ’yan adam, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.”