51 Bible Verses About Loving Your Mother
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
25 Ƙarfi da mutunci su ne suturarta;
za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.
26 Tana magana da hikima,
kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.
27 Tana lura da sha’anin gidanta
kuma ba ta cin abincin ƙyuya.
28 ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka;
haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,
29 “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo,
amma ke kin fi su duka.”
30 Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;
amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
31 Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta,
bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.
-
1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
-
25 To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26 Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27 ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
-
12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
-
22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,
kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.
23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;
ka nemi hikima, horo da fahimi.
24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;
duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.
25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna;
bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!
-
1 Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2 Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.
3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4 Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5 su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.
-
3 Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku? 4 Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’ 5 Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’ 6 ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.
-
Gargaɗi don a rungumi hikima
8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9 Za su zama kayan ado don su inganta ka
da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
-
6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
-
12 Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“Zan fadada salama gare ta kamar kogi,
wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu;
za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta
ku kuma yi wasa a gwiwoyinta.
13 Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta
haka zan ta’azantar da ku;
za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”
-
16 Ka ba da girma ga mahaifinka da mahaifiyarka, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka, don ka yi tsawon rai, ka kuma sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
-
14 Amma Sihiyona ta ce, “Ubangiji ya yashe ni,
Ubangiji ya manta da ni.”
15 “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta
ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?
Mai yiwuwa ta manta,
amma ba zan taɓa manta da ke ba!
16 Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;
katangarki kullum suna a gabana.
-
1 Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka, 2 tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki.
3 Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. 4 Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. 5 Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako. 6 Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai. 7 Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi. 8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.
-
1 Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2 sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3 Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4 Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.
-
3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,
yara lada ne daga gare shi.
4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi
haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.
5 Mai albarka ne mutumin
da korinsa sun cika da su.
Ba za a kunyata su ba
sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.
-
4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.
8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.
-
3 Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina. 4 Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki. 5 An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.
-
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.
3 “ ‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku.
-
13 Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
-
20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
21 Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;
ka ɗaura su kewaye da wuyanka.
22 Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;
sa’ad da kake barci, za su lura da kai;
sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.
23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,
wannan koyarwa haske ne,
kuma gyare-gyaren horo
hanyar rayuwa ce,
24 suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a
daga sulɓin harshen mace marar aminci.
-
46 Sai Maryamu ta ce,
“Raina yana ɗaukaka Ubangiji
47 ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
48 gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.
Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
-
Maganar ƙarshe. Mace Mai Halin Kirki
10 Wa yake iya samun mace mai halin kirki?
Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
11 Mijinta yana da cikakken amincewa da ita
kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.
12 Takan yi masa alheri ba mugunta ba,
dukan kwanakin ranta.
-
17 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”
18 Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?”
Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, 19 ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”
-
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
-
9 Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku. 10 Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.”
-
23 Elkana mijinta ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi miki kyau. Ki jira har sai bayan kin yaye shi. Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Saboda haka matar ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta har ta yaye shi.
24 Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo. 25 Bayan an yanka bijimin, sai suka kawo yaron wurin Eli. 26 Sai ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ba ka gane ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana addu’a ga Ubangiji. 27 Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi. 28 Saboda haka, na ba da shi ga Ubangiji muddin ransa, zai zama na Ubangiji.” A can kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.
-
20 Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.
-
51 Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta. 52 Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.
-
8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9 Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10 Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.
-
22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.
-
8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.
-
16 Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. 17 Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.”
-
6 Jikoki rawanin tsofaffi ne,
kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
-
19 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”
-
13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
-
14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
-
4 Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.
-
22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
23 Sai mutumin ya ce,
“Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana
nama kuma na namana.
Za a ce da ita ‘mace,’
gama an ciro ta daga namiji.”
24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.
-
1 Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari. 2 Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari. 3 Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku.
-
6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
-
1 Mace mai hikima kan gina gidanta,
amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.
2 Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji,
amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.
-
15 Sandar gyara kan ba da hikima,
amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
16 Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa,
amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane.
17 Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama;
zai ba ka farin cikin da kake so.
-
20 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
-
7 Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. 8 Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne. 9 Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa. 10 Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu. 11 Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. 12 Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.
-
9 Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta
ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki.
Yabi Ubangiji.
-
20 Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa,
amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.
-
26 Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa
ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.
27 In ka daina jin umarni, ɗana,
za ka kuwa kauce daga kalmomin sani.
-
39 Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
-
38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
-
32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.
-
16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. 17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
Shows Read in context, Share and Copy.