42 Bible Verses About Nature

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Nature
  1. 26 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”

    27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

    Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

    Miji da mace ya halicce su.

    28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”

    29 Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. 30 Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.

    31 Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.

  2. 18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.

    21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

    1 Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;

    sararin sama suna furta aikin hannuwansa.

    2 Kowace rana tana yin jawabi;

    kowane dare yana nuna sani.

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda.

    1 Ya Ubangiji, shugabanmu,

    sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

    Ka kafa ɗaukakarka

    bisa sammai.

    2 Daga leɓunan yara da jarirai

    ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka

    da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

    3 Sa’ad da na dubi sammai,

    aikin yatsotsinka,

    wata da taurari

    waɗanda ka ajiye a wurarensu,

    4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,

    ɗan mutum da kake lura da shi?

    5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah

    ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

    6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;

    ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

    7 dukan shanu da tumaki,

    da kuma namun jeji,

    8 tsuntsayen sararin sama

    da kifin teku,

    da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.

  5. 15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. 16 Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. 17 Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. 18 Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici. 19 Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, 20 ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.

  6. 5 Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. 6 Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan. 7 Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. 8 Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. 11 A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.

  7. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.

    22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.

  8. 10 Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.”

    Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba;

    zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.

    11 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;

    bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;

    12 bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.

    Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;

    13 za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,

    yana zuwa don yă hukunta duniya.

    Zai hukunta duniya cikin adalci

    mutane kuma cikin amincinsa.

  9. 4 Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su.

    Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, 5 babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar, 6 amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa. 7 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.

    8 To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi. 9 Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.

  10. 7 “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka,

    ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.

    8 Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka,

    ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.

    9 Wane ne cikin waɗannan bai san

    cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?

    10 Ran kowace halitta yana a hannunsa,

    haka kuma numfashin dukan ’yan adam.

  11. 26 Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. 27 Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.

  12. 1 Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2 Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. 3 Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. 4 Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5 ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.

  13. 9 Zuciya ta fi kome ruɗu

    ta fi ƙarfin warkewa.

    Wa zai iya gane ta?

  14. 17 In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan, 18 kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka. 19 To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.” 20 Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro. 21 Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.

    22 Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka. 23 In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su. 24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?

  15. 6 Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama; 7 hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba. 8 Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.

  16. 35 Amma wani yana iya tambaya yă ce, “Ta yaya ake tā da matattun? Da wane irin jiki za su tashi?” 36 Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu. 37 Sa’ad da kuke shuki, ba tsiron da zai yi girma ba ne kuka shuka, ƙwayar ce kawai, ko ta alkama ko kuma na wani irin dabam. 38 Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta. 39 Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu. 40 Akwai jikuna iri na samaniya, akwai kuma jikuna iri na duniya; sai dai darajar jikunan samaniya dabam take, darajar jikunan duniya kuma dabam take. 41 Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja.

    42 Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka tā da shi kuma ba ya ruɓewa; 43 akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma tā da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma tā da shi da ƙarfi; 44 akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya.

    In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma. 45 Haka yake a rubuce cewa, “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai. 46 Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya. 47 Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. 48 Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama. 49 Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama.

    50 Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba.

  17. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.

  18. 24 “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. 25 Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. 26 Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. 27 Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. 28 ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’

  19. 1 A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri, 2 amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. 3 Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. 4 Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.

  20. 15 Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.

  21. 14 Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu,

    tsire-tsire domin mutum ya nome,

    suna fid da abinci daga ƙasa,

    15 ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna,

    mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske,

    abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.

    16 Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai,

    al’ul na Lebanon da ya shuka.

    17 A can tsuntsaye suke sheƙunnansu;

    shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir.

    18 Manyan duwatsu na awakin jeji ne;

    tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.

  22. 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

    28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?

  23. 10 Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.

    Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. 11 Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12 Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. 13 Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya. 14 Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.

  24. 1 ’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai. 2 Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba. 3 Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba? 4 Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba?

  25. 6 Sai Ubangiji Allah ya sa wata ’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa. 7 Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye ’yar kuringar har ta mutu. 8 Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.”

    9 Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?”

    Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.”

    10 Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita. 11 Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”

  26. 12 Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su. 13 Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci. 14 Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar. 15 To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su. 16 Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.

  27. 14 Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi,

  28. 16 Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, 17 amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”

  29. 11 Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba.”

    12 Allah ya kuma ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na yi tsakanina da ku, da kowace halitta tare da ku; alkawari na dukan zamanai masu zuwa. 13 Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya. 14 Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan, 15 zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba. 16 Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.”

  30. 3 Yabe shi, rana da wata,

    yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

    4 Yabe shi, ku bisa sammai

    da kuma ku ruwan bisa sarari.

    5 Bari su yabi sunan Ubangiji,

    gama ya umarta aka kuwa halicce su.

  31. 3 Za a wofinta duniya ƙaƙaf

    a kuma washe ta sarai.

    Ubangiji ne ya faɗa haka.

    4 Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane,

    duniya tana shan azaba ta kuma raunana,

    masu daraja na duniya suna shan azaba.

    5 Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta

    sun ƙi yin biyayya da dokoki,

    sun keta farillai

    suka kuma karya madawwamin alkawari.

    6 Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya;

    dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu.

    Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya,

    kuma kaɗan ne kurum suka rage.

  32. 8 “Gama tunanina ba tunaninku ba ne,

    yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,”

    in ji Ubangiji.

    9 “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,

    haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa

    tunanina kuma dabam da naku.

    10 Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke

    saukowa daga sama,

    ba sa komowa

    ba tare da sun jiƙe duniya

    sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho,

    don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,

    11 haka maganata da take fitowa daga bakina.

    Ba za tă koma gare ni wofi ba,

    amma za tă cika abin da nake so

    ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.

    12 Za ku fita da farin ciki

    a kuma bi da ku da salama;

    duwatsu da tuddai

    za su ɓarke da waƙa a gabanku,

    dukan itatuwan jeji kuma

    za su tafa hannuwansu.

    13 A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro,

    a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro.

    Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi,

    madawwamiyar alama ce,

    wadda ba za a datse ba.”

  33. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata!

  34. 14 Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. 15 Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. 16 In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. 17 Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. 18 Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. 19 Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi. 20 To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.

    21 Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22 Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23 amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24 Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25 Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu!

    Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.

  35. 5 Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci. 6 Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai.

  36. 25 Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa,

    da kuma hanyar walƙiyar tsawa

    26 don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin

    jeji inda ba mai zama ciki

    27 don a ƙosar da wurin da ya bushe

    a sa ciyawa ta tsiro a can?

    28 Ruwan sama yana da mahaifi?

    Wa ya zama mahaifin raɓa?

    29 Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara?

    Wane ne ya haifi jaura daga sammai

    30 lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse,

    lokacin da saman ruwa ya daskare?

  37. 24 Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!

    Cikin hikima ka yi su duka;

    duniya ta cika da halittunka.

    25 Akwai teku, babba da kuma fāɗi,

    cike da halittun da suka wuce ƙirga,

    abubuwa masu rai babba da ƙarami.

  38. 5 Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja,

    zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.

  39. 6 Muryar tana cewa, “Ka yi shela.”

    Na kuwa ce, “Me zan yi shelar?”

    “Dukan mutane kamar ciyawa suke,

    kuma dukan ɗaukakarsu kamar furannin jeji ne.

    7 Ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi,

    domin Ubangiji ya hura iska a kansu.

    Tabbatacce mutane ciyawa ne.

    8 Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi,

    amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada.”

  40. 13 Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi;

    yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya.

    Yakan aiki walƙiya da ruwan sama

    ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.

  41. 22 Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya. 23 Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.

    24 Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!”

    Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. 25 Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?”

    A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”

  42. 6 Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.