50 Bible Verses About God's Creation

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About God's Creation
  1. 1 A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. 2 To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.

    3 Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. 4 Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. 5 Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.

    6 Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” 7 Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. 8 Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.

    9 Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. 10 Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.

    11 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. 12 Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. 13 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.

    14 Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15 bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. 16 Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. 17 Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, 18 su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.

    20 Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” 21 Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22 Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” 23 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.

    24 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. 25 Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

    26 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”

    27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

    Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

    Miji da mace ya halicce su.

    28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”

    29 Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. 30 Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.

    31 Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.

  2. 8 To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi. 9 Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.

    10 Akwai wani kogi mai ba da ruwa ga lambun wanda ya gangaro daga Eden, daga nan ya rarrabu, ya zama koguna huɗu. 11 Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya. 12 (Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.) 13 Sunan kogi na biyu, Gihon. Shi ne ya malala kewaye da ƙasar Kush. 14 Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites.

    15 Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi. 16 Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, 17 amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”

    18 Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

    19 To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. 20 Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.

    Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

    23 Sai mutumin ya ce,

    “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

    nama kuma na namana.

    Za a ce da ita ‘mace,’

    gama an ciro ta daga namiji.”

    24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

    25 Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.

  3. 15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. 16 Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. 17 Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. 18 Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici. 19 Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, 20 ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.

  4. 1 Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.

    2 Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. 3 Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.

  5. 1 A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri, 2 amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. 3 Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. 4 Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.

  6. 18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.

    21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

    24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. 25 Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.

  7. 1 Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. 2 Yana nan tare da Allah tun farar farawa. 3 Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi. 4 A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5 Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.

  8. 5 Ubangiji yana ƙaunar adalci

    duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.

    6 Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai,

    rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.

    7 Ya tattara ruwan teku cikin tuluna;

    ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.

    8 Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji;

    bari dukan mutanen duniya su girmama shi.

    9 Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance;

    ya umarta, ya kuwa tsaya daram.

  9. 3 Sa’ad da na dubi sammai,

    aikin yatsotsinka,

    wata da taurari

    waɗanda ka ajiye a wurarensu,

    4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,

    ɗan mutum da kake lura da shi?

    5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah

    ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

    6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;

    ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

    7 dukan shanu da tumaki,

    da kuma namun jeji,

    8 tsuntsayen sararin sama

    da kifin teku,

    da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.

    9 Ya Ubangiji, shugabanmu,

    sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

  10. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

    1 Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;

    sararin sama suna furta aikin hannuwansa.

    2 Kowace rana tana yin jawabi;

    kowane dare yana nuna sani.

    3 Ba magana, ba kalmar da aka hurta,

    ba wani amon da aka ji daga gare su.

    4 Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,

    kalmominsu zuwa iyakokin duniya.

    A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,

    5 wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,

    kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.

    6 Takan taso daga ƙarshen sammai

    ta kewaye zuwa wancan;

    babu abin da yake ɓuya wa zafinta.

  11. 3 Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.

  12. 18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.

    22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.

  13. 22 Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce, “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai. 23 Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu,

    Ga Allahn da ba a sani ba.

    To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.

    24 “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. 25 Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. 26 Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. 27 Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. 28 ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’

    29 “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa. 30 A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba. 31 Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.”

    32 Sa’ad da suka ji maganar tashin matattu, waɗansunsu suka yi tsaki, amma waɗansu suka ce, “Muna so mu ƙara jin ka a kan wannan batu.” 33 Da wannan, Bulus ya bar Majalisar. 34 Waɗansu mutane kima suka zama mabiyan Bulus suka kuwa gaskata. A cikinsu kuwa akwai Diyonasiyus ɗan Majalisar Areyofagus, haka kuma wata mace mai suna Damaris, da waɗansu dai haka.

  14. 11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,

    ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,

    domin ka halicci dukan abubuwa,

    kuma ta wurin nufinka aka halicce su

    suka kuma kasance.”

  15. 6 Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.

  16. 7 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.

  17. 8 Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. 9 Kwana shida za ka yi dukan aikinka, 10 amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. 11 Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  18. 3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,

    babban Sarki a bisa dukan alloli.

    4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,

    ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

    5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,

    da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

    6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,

    bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

    7 gama shi ne Allahnmu

    mu mutanen makiyayansa ne,

    garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.

    Yau, in kuka ji muryarsa,

  19. 1 Yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji daga sammai,

    yabe shi a bisa sammai.

    2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,

    yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

    3 Yabe shi, rana da wata,

    yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

    4 Yabe shi, ku bisa sammai

    da kuma ku ruwan bisa sarari.

    5 Bari su yabi sunan Ubangiji,

    gama ya umarta aka kuwa halicce su.

    6 Ya sa su a wurarensu har abada abadin;

    ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.

    7 Yabi Ubangiji daga duniya,

    ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,

    8 walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai,

    hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,

    9 ku duwatsu da dukan tuddai,

    itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,

    10 namun jeji da dukan dabbobin gida,

    ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,

    11 sarakunan duniya da dukan al’ummai,

    ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,

    12 samari da ’yan mata,

    tsofaffi da yara.

    13 Bari su yabi sunan Ubangiji,

    gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka;

    darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.

    14 Ya tayar wa mutanensa ƙaho,

    yabon dukan tsarkakansa,

    na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa.

    Yabi Ubangiji.

  20. 3 Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.

    4 “Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna. 5 Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.

    6 “Duk wanda ya zub da jinin mutum,

    ta hannun mutum za a zub da jininsa;

    gama a cikin siffar Allah ne,

    Allah ya yi mutum.

  21. Zabura ta Dawuda.

    1 Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta,

    duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;

    2 gama ya gina ta a kan tekuna

    ya kafa ta a kan ruwaye.

  22. 13 Gama ka halicci ciki-cikina;

    ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

    14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

    ayyukanka suna da banmamaki,

    na san da haka sosai.

    15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

    sa’ad da aka yi ni asirce.

    Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

    16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;

    dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

    kafin ɗayansu yă kasance.

  23. 5 Ga abin da Allah Ubangiji ya ce,

    shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su,

    wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta,

    wanda ya ba wa mutanenta numfashi,

    da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.

    6 “Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci;

    zan riƙe hannunka.

    Zan kiyaye ka in kuma sa ka

    zama alkawari ga mutane

    haske kuma ga Al’ummai,

    7 don ka buɗe idanun makafi

    ka ’yantar da kamammu daga kurkuku

    kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.

    8 “Ni ne Ubangiji; sunana ke nan!

    Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka.

    9 Duba, abubuwan da sun tabbata,

    sababbin abubuwa kuwa nake furtawa;

    kafin ma su soma faruwa

    na sanar da su gare ku.”

    10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,

    ku yi yabonsa daga iyakar duniya,

    ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,

    ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.

  24. 17 Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo! 18 Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu, 19 wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu. 20 Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah. 21 Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.

  25. 7 Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari;

    ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.

    8 Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa,

    duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.

    9 Ya rufe fuskar wata,

    ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,

    10 ya zāna iyakar fuskar ruwa

    a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.

    11 Madogaran sama sun girgiza,

    saboda tsawatawarsa.

    12 Da ikonsa ya kwantar da teku;

    da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.

    13 Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau

    da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.

    14 Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa.

    Kaɗan kawai muke ji game da shi!

    Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”

  26. 5 Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa), 6 duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.

  27. 4 Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.” 5 Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma. 6 Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci. 7 Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.

    8 Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. 9 Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.

    10 Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu.

    11 Da yake za a hallaka dukan abubuwa ta haka, waɗanne irin mutane ne ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi rayuwar tsarki da ta tsoron Allah, 12 yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi. 13 Amma bisa ga alkawarinsa muna zuba ido ga sabuwar sama da kuma sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zama.

  28. 16 Sa’an nan ya ce wa macen,

    “Zan tsananta naƙudarki ainun,

    da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya.

    Za ki riƙa yin marmarin mijinki

    zai kuwa yi mulki a kanki.”

    17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’

    “Za a la’anta ƙasa saboda kai.

    Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.

    18 Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya

    za ka kuwa ci ganyayen gona.

    19 Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,

    da yake daga cikinta aka yi ka.

    Gama kai turɓaya ne,

    kuma ga turɓaya za ka koma.”

  29. 7 “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka,

    ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.

    8 Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka,

    ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.

    9 Wane ne cikin waɗannan bai san

    cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?

    10 Ran kowace halitta yana a hannunsa,

    haka kuma numfashin dukan ’yan adam.

    11 Ko kunne ba ya gwada kalmomi

    kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci?

    12 Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba?

    Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?

  30. 2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;

    ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

    3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.

    Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;

    mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

  31. 8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

  32. 10 Ya kuma ce,

    “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya,

    sammai kuma aikin hannuwanka ne.

    11 Su za su hallaka, amma kai kana nan;

    dukansu za su tsufa kamar riga.

    12 Za ka naɗe su kamar mayafi,

    kamar riga za su sauya.

    Amma kai ba za ka canja ba,

    shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”

  33. 28 Ba ku sani ba?

    Ba ku ji ba?

    Ubangiji madawwamin Allah ne,

    Mahaliccin iyakokin duniya.

    Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,

    kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

  34. 6 Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’

    Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’

    Kawo ’ya’yana maza daga nesa

    ’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,

    7 kowa da ake kira da sunana,

    wanda aka halitta saboda ɗaukakata,

    wanda na siffanta na kuma yi.”

  35. 11 “Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’ ”

    12 Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa;

    ya kafa duniya ta wurin hikimarsa

    ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.

    13 Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi;

    yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya.

    Yakan aiki walƙiya da ruwan sama

    ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.

  36. 8 A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba. 9 Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za tă warkar da shi 10 sai ya ɗaga murya ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka!” Da jin haka, sai mutumin ya yi wuf ya kuma fara tafiya.

    11 Sa’ad da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ihu da harshen Likayoniyawa, suna cewa, “Alloli sun sauka mana da siffar mutane!” 12 Sai suka ba wa Barnabas, sunan Zeyus, Bulus kuma suka kira Hermes domin shi ne shugaban magana. 13 Firist na Zeyus, wanda haikalinsa ke bayan birni, ya kawo bijimai da furanni a ƙofofin birni domin shi da taron mutanen sun so su miƙa musu hadayu.

    14 Amma da manzannin nan Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage tufafinsu suka ruga cikin taron, suna ihu suna cewa, 15 “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu. 16 A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama. 17 Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.” 18 Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jama’an nan yin musu hadaya.

  37. 1 Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,

    2 “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata

    da surutan wofi?

    3 Ka sha ɗamara kamar namiji;

    zan yi maka tambaya,

    za ka kuwa amsa mini.

    4 “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya?

    Gaya mini, in ka sani.

    5 Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani!

    Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?

    6 A kan me aka kafa tushenta,

    ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,

    7 yayinda taurarin safe suke waƙa tare

    dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.

    8 “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi,

    lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.

    9 Lokacin da na yi wa gizagizai riga

    na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,

    10 sa’ad da na yi masa iyaka na

    sa masa ƙofofi da wurin kullewa.

    11 Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai,

    ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?

    12 “Ko ka taɓa ba safiya umarni

    ko kuma ka sa asuba ta fito,

    13 don ta kama gefen duniya

    ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?

    14 Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi;

    ta fito a fili kamar riga.

    15 An hana mugaye haskensu,

    hannun da suka ɗaga an karya shi.

    16 “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku,

    ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?

    17 Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa?

    Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?

    18 Ko ka gane fāɗin duniya?

    Gaya mini, in ka san wannan duka.

    19 “Ina ne hanyar zuwa gidan haske?

    Kuma a ina duhu yake zama?

    20 Ko za ka iya kai su wurarensu?

    Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama?

    21 Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin!

    Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa.

    22 “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara

    ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara

    23 waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala,

    domin kwanakin yaƙi da faɗa?

    24 Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya,

    ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?

    25 Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa,

    da kuma hanyar walƙiyar tsawa

    26 don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin

    jeji inda ba mai zama ciki

    27 don a ƙosar da wurin da ya bushe

    a sa ciyawa ta tsiro a can?

    28 Ruwan sama yana da mahaifi?

    Wa ya zama mahaifin raɓa?

    29 Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara?

    Wane ne ya haifi jaura daga sammai

    30 lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse,

    lokacin da saman ruwa ya daskare?

    31 “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta?

    Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?

    32 Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu

    ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?

    33 Ka san dokokin sammai?

    Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?

    34 “Za ka iya tsawata wa gizagizai

    ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?

    35 Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa?

    Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’

    36 Wane ne yake cika zuciya da hikima

    ko kuma yake ba zuciya ganewa?

    37 Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai?

    Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai

    38 sa’ad da ƙura ta yi yawa

    ta daskare a wuri ɗaya?

    39 “Za ka iya farauto wa zakanya nama,

    ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu.

    40 Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu,

    ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?

    41 Wane ne yake ba hankaka abinci

    lokacin da ’ya’yansa suke kuka ga Allah,

    kuma suna yawo don rashin abinci?

  38. 25 A farkon fari ka kafa tushen duniya,

    sammai kuma aikin hannuwanka ne.

    26 Za su hallaka, amma za ka ci gaba;

    duk za su tsufe kamar riga.

    Kamar riga za ka canja su

    za a kuwa zubar da su.

    27 Amma kana nan yadda kake,

    kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.

  39. 1 Yabi Ubangiji, ya raina.

    Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai;

    kana saye da daraja da ɗaukaka.

    2 Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga

    ya shimfiɗa sammai kamar tenti

    3 ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye.

    Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa

    yana hawa a kan fikafikan iska.

    4 Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa

    harsunan wuta kuma bayinsa.

    5 Ya kafa duniya a kan tussanta;

    ba za a iya matsar da ita ba.

    6 Ka rufe ta da zurfi kamar da riga

    ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.

    7 Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu

    da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;

    8 suka gudu a bisa duwatsu,

    suka gangara zuwa cikin kwaruruka,

    zuwa wurin da ka shirya musu.

    9 Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa;

    ba za su ƙara rufe duniya ba.

    10 Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka;

    yana gudu tsakanin duwatsu.

    11 Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji;

    jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.

    12 Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan;

    suna rera cikin rassa.

    13 Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama;

    ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.

    14 Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu,

    tsire-tsire domin mutum ya nome,

    suna fid da abinci daga ƙasa,

    15 ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna,

    mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske,

    abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.

    16 Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai,

    al’ul na Lebanon da ya shuka.

    17 A can tsuntsaye suke sheƙunnansu;

    shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir.

    18 Manyan duwatsu na awakin jeji ne;

    tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.

    19 Wata ne ke ƙididdigar lokuta,

    rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.

    20 Ka yi duhu, sai ya zama dare,

    sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.

    21 Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta

    suna kuma neman abincinsu daga Allah.

    22 Rana ta fito, sai suka koma shiru;

    suka koma suka kwanta a kogwanninsu.

    23 Mutum yakan tafi aikinsa,

    zuwa wurin aikinsa har yamma.

    24 Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!

    Cikin hikima ka yi su duka;

    duniya ta cika da halittunka.

    25 Akwai teku, babba da kuma fāɗi,

    cike da halittun da suka wuce ƙirga,

    abubuwa masu rai babba da ƙarami.

    26 A can jiragen ruwa suna kai komo,

    kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.

    27 Waɗannan duka suna dogara gare ka

    don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.

    28 Sa’ad da ba su da shi,

    sai su tattara shi;

    sa’ad da ka buɗe hannunka,

    sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.

    29 Sa’ad da ka ɓoye fuskarka,

    sai su razana;

    sa’ad da ka ɗauke numfashinsu,

    sai su mutu su kuma koma ga ƙura.

    30 Sa’ad da ka aika da Ruhunka,

    sai su halittu,

    su kuma sabunta fuskar duniya.

    31 Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada;

    bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa,

    32 shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana,

    wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.

    33 Zan rera ga Ubangiji dukan raina;

    zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.

    34 Bari tunanina yă gamshe shi,

    yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.

    35 Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya

    mugaye kuma kada a ƙara ganinsu.

    Yabi Ubangiji, ya raina.

    Yabi Ubangiji.

  40. 17 “Ga shi, na halicci

    sabuwar sama da kuma sabuwar duniya.

    Abubuwa na dā za a manta da su,

    ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.

    18 Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada

    a abin da na halitta,

    gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna

    mutanenta kuwa abin farin ciki.

    19 Zan yi farin ciki a kan Urushalima

    in kuma yi murna saboda mutanena;

    a can ba za a ƙara jin

    karar makoki da na kuka ba.

  41. 4 Ruhun Allah ne ya yi ni;

    numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.

  42. 18 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa,

    shi da ya halicci sammai,

    shi ne Allah;

    shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya,

    ya kafa ta;

    bai halicce ta don ta zama ba kome ba,

    amma ya yi ta don a zauna a ciki,

    ya ce,

    “Ni ne Ubangiji,

    kuma babu wani.

  43. 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

    28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?

  44. 1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

    5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”

  45. 1 To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”

    2 Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, 3 amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”

    4 Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. 5 Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”

    6 Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.

  46. 1 Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu.

    Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.

  47. 25 “Ga wa za ku kwatanta ni?

    Ko kuwa wa yake daidai da ni?” In ji Mai Tsarkin nan.

    26 Ku ɗaga idanunku ku duba sammai.

    Wane ne ya halicce dukan waɗannan?

    Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya,

    yana kiransu, kowanne da sunansa.

    Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma,

    babu ko ɗayansu da ya ɓace.

  48. 17 “A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka.

  49. 10 Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.

  50. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.