61 Bible Verses About Rain
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
41 Sai Iliya ya ce wa Ahab, “Ka haura gida, ka ci, ka sha, gama ina jin motsin ruwan sama mai yawa.” 42 Sai Ahab ya ruga don yă ci, yă sha, amma Iliya ya hau kan ƙwanƙolin Karmel, ya rusuna ƙasa, ya sa fuska a tsakanin gwiwarsa.
43 Ya ce wa bawansa, “Tafi ka dubi wajen teku.” Sai bawan ya haura ya duba.
Ya ce, “Ba kome a can.”
Sau bakwai Iliya ya ce, “Koma.”
44 Sau na bakwai, bawan ya ce, “Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku.”
Sai Iliya ya ce, “Je ka faɗa wa Ahab, ‘Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama yă tare ka.’ ”
45 Ana cikin haka, sarari ya ƙara duhunta da girgije, iska ta taso, sai ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauko, Ahab kuwa ya hau zuwa Yezireyel. 46 Ikon Ubangiji ya sauko a kan Iliya, ya sha ɗamara, ya ruga a guje a gaban Ahab har zuwa Yezireyel.
-
16 Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.
17 Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi. 18 Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.
-
24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”
-
10 Ƙasar da kuke shiga, ku karɓa, ba kamar ƙasar Masar ba ce, inda kuka fito, inda kuka shuka iri, ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu. 11 Amma ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaki, ƙasa ce ta duwatsu da kwaruruka wadda ruwan sama ne yake jiƙe ta. 12 Ƙasa ce da Ubangiji Allahnku yake lura da ita; idanun Ubangiji Allahnku yana a kai daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.
13 Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, 14 sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku. 15 Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi.
16 Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada, 17 don kada fushin Ubangiji yă ƙuna a kanku, yă rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.
-
23 Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,
ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,
gama ya ba ku
ruwan bazara cikin adalci.
Yakan aika muku yayyafi a yalwace,
na bazara da na kaka, kamar dā.
24 Masussukai za su cika da hatsi;
randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.
25 “Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru
waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa,
da kuma sauran fāra da tarin fāra
babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku.
26 Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi,
za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku,
wanda ya yi muku ayyukan banmamaki;
mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.
-
7 Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah,
sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi, Sela
8 duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama,
a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai,
a gaban Allah, Allah na Isra’ila.
9 Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah;
ka rayar da gādonka da ya gāji.
10 Mutanenka suka zauna a cikinsa,
kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta.
-
35 “Sa’ad da sammai sun kulle, babu kuma ruwan sama domin mutane sun yi maka zunubi, sa’ad da suka yi addu’a suna fuskantar wannan wuri, suka kuma furta sunanka, suka juye daga zunubinsu domin ka hore su, 36 ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo.
-
6 Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka,
kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
-
43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.
-
10 Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke
saukowa daga sama,
ba sa komowa
ba tare da sun jiƙe duniya
sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho,
don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,
11 haka maganata da take fitowa daga bakina.
Ba za tă koma gare ni wofi ba,
amma za tă cika abin da nake so
ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.
-
9 A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi.
-
3 “ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, 4 zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu. 5 Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku.
-
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;
ku kada garaya ga Allahnmu.
8 Ya rufe sararin sama da gizagizai;
yana tanada wa duniya ruwan sama
yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
-
15 “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu. 16 A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama. 17 Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.”
-
14 In kuka ji tsoron Ubangiji, kuka bauta masa, kuka yi masa biyayya, ba ku kuwa ƙi bin umarninsa ba, in kuma ku da sarkin da yake mulkinku kun bi Ubangiji Allahnku, to, za ku zauna lafiya. 15 Amma in ba ku yi biyayya ga Ubangiji ba, in kuma kuka ƙi bin umarnansa, fushinsa zai zauna a kanku.
16 Yanzu ku tsaya tsit ku ga abin da Ubangiji ke dab da yi a gabanku. 17 Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.
18 Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.
19 Dukan mutane suka ce wa Sama’ila, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda bayinka, domin kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”
-
1 “Ku zo, mu koma ga Ubangiji.
Ya yayyage mu kucu-kucu
amma zai warkar da mu;
ya ji mana ciwo
amma zai daure mana miyakunmu.
2 Bayan kwana biyu zai rayar da mu,
a rana ta uku zai tashe mu,
don mu rayu a gabansa.
3 Bari mu yarda da Ubangiji;
bari mu nace gaba don mu yarda da shi.
Muddin rana tana fitowa,
zai bayyana;
zai zo mana kamar ruwan bazara,
kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”
-
1 Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara;
Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari.
Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama
yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.
-
6 Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’
ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
7 Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa,
ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.
-
1 Ka jefa burodinka a bisa ruwaye,
gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.
2 Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas,
gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.
3 In gizagizai sun cika da ruwa,
sukan zub da ruwan sama bisa duniya.
Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa,
inda ya fāɗi a nan zai kwanta.
4 Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba,
mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba.
5 Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba,
ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya,
haka ba za ka fahimci aikin Allah
Mahaliccin dukan abubuwa ba.
6 Ka shuka irinka da safe,
da yamma kuma kada ka janye hannunka,
gama ba ka san wanda zai yi albarka ba,
ko wannan ko wancan,
ko kuma duka biyunsu su yi albarka.
-
16 Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul. 17 In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. 18 In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba. 19 Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.
-
22 Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama?
Sararin sama kansu sukan yi yayyafi?
A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu.
Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka,
gama kai ne kake yi wannan duka.
-
15 Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan;
tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara.
-
4 Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.”
5 Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi.
-
1 To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”
-
24 Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu,
wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara,
wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’
-
22 Zan yi hukunci a kansa da annoba da kuma zub da jini; zan yi ruwa mai yawa da ƙanƙara da kibiritu mai cin wuta a kansa da a kan sojojinsa da kuma a kan al’ummai masu yawa da suke tare da shi.
-
4 Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su.
Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, 5 babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar, 6 amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa.
-
2 Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama
kalmomina kuma su sauko kamar raɓa,
kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa,
kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi.
-
24 Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa,
waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.
25 Dukan ’yan adam sun gani;
mutane sun hanga daga nesa.
26 Allah mai girma ne,
ya wuce ganewarmu!
Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
27 “Yana sa ruwa yă zama tururi
yă zubo daga sama.
28 Gizagizai suna zubo da raɓarsu
kuma ruwan sama yana zubowa ’yan adam a wadace.
29 Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai
yadda yake tsawa daga wurin zamansa?
30 Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi,
tana haskaka zurfin teku.
31 Haka yake mulkin al’ummai
yana kuma tanada abinci a wadace.
32 Yana cika hannuwansa da walƙiya
kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.
33 Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa;
ko shanu sun san da zuwansa.
-
7 Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. 8 Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa. 9 ’Yan’uwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa!
10 ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala. 11 Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.
-
10 Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya.
11 A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. 12 Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in.
-
6 Ubangiji yana yin abin da ya ga dama,
a sammai da kuma a duniya,
cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.
7 Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya;
yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama
ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.
-
7 “Na kuma hana muku ruwan sama
tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi.
Na sa aka yi ruwan sama a wani gari,
sai na hana a yi a wani gari.
Wata gona ta sami ruwan sama;
wata gona kuma ta bushe.
-
1 Bayan dogon lokaci, a cikin shekara ta uku, maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Tafi, ka gabatar da kanka ga Ahab, zan kuwa aika da ruwan sama a ƙasar.” 2 Saboda haka Iliya ya tafi ya gabatar da kansa ga Ahab.
Yanzu dai yunwa ta tsananta a Samariya,
-
23 Lokacin da ya cika cikinsa,
Allah zai zuba fushinsa a kansa,
zai daddaka shi.
-
23 Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama,
haka jita-jita kan kawo fushi.
-
7 Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah.
-
12 Allah ya kuma ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na yi tsakanina da ku, da kowace halitta tare da ku; alkawari na dukan zamanai masu zuwa. 13 Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya. 14 Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan, 15 zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba. 16 Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.”
17 Saboda haka Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na kafa tsakanina da dukan masu rai a duniya.”
-
27 Na ga daga abin da ya yi kamar kwankwasonsa zuwa bisa ya yi kamar ƙarfe mai walƙiya, sai ka ce wuta, kuma daga kwankwasonsa zuwa ƙasa ya yi kamar wuta; haske kuma mai walƙiya sosai kewaye da shi. 28 Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka hasken da ya kewaye shi.
Wannan shi ne kwatancin kamannin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na fāɗi rubda ciki, na kuma ji muryar wani tana magana.
-
26 Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka. 27 Itatuwan gona za su ba da ’ya’yansu, ƙasa kuma za tă ba da amfaninta; mutane za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.
-
54 Ya ce wa taron, “Sa’ad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi. 55 Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi. 56 Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba?
-
6 Za tă zama rumfa da inuwar da za tă tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama.
-
1 Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi,
haka girmamawa bai dace da wawa ba.
-
3 Mai mulkin da ya danne talakawa
yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi.
-
8 “Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama;
bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci.
Bari ƙasa ta buɗe,
bari ceto ya tsiro,
bari adalci ya yi girma tare da shi;
ni, Ubangijine, na sa ya faru.
-
12 Ku shuka wa kanku adalci,
ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa,
ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba;
gama lokaci ne na neman Ubangiji,
sai ya zo
ya zubo adalci a kanku.
-
33 Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke. 34 Da Fir’auna ya ga cewa ruwa da ƙanƙara da tsawa sun daina, sai ya sāke yin zunubi. Shi da fadawansa, suka taurare zukatansu.
-
26 “Sa’ad da sammai suka rufu ba kuwa ruwan sama saboda mutanenka sun yi maka zunubi, sa’ad da kuwa suka yi addu’a suna duban waje wannan wuri suka kuma furta sunanka suka juye daga zunubinsu domin ka azabta su, 27 sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace da za su yi zama, ka kuma aika ruwan sama a ƙasar da ka ba mutanenka gādo.
-
11 Ubangiji zai azurta ku sosai, a ’ya’yan cikinku, a ’ya’yan dabbobinku da kuma a hatsin gonarku, a cikin ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku.
12 Ubangiji zai buɗe sammai, wurin ajiyarsa mai yalwa, don yă aika da ruwan sama a gonarku a lokacinsa, yă kuma albarkaci dukan aikin hannuwanku. Za ku ba wa al’ummai masu yawa rance, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba.
-
22 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa dukan Masar, a bisa mutane da dabbobi, da bisa dukan abubuwan da suke girma a gonakin Masar.” 23 Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar; 24 ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma. 25 Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace. 26 Wuri guda kaɗai da ba a yi ruwan ƙanƙara ba, shi ne yankin Goshen, inda Isra’ilawa suke.
-
6 Zan mai da ita kango,
ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba,
sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can
Zan umarci gizagizai
kada su yi ruwan sama a kanta.”
-
6 A kan mugaye zai zuba
garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;
iska mai zafi zai zama rabonsu.
-
14 Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama
haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa.
-
12 Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa;
ya kafa duniya ta wurin hikimarsa
ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
13 Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi;
yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya.
Yakan aiki walƙiya da ruwan sama
ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.
-
18 Saboda haka, gobe war haka, zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske, irin wadda Masar ba tă taɓa gani ba tun kahuwarta, har yă zuwa yanzu.
-
12 Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. 13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.
-
6 Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so.
-
10 Rizfa ’yar Aiya ta ɗauki tsumma ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutse. Tun daga farkon girbi har ruwa damina ya sauko a kan gawawwakin, ba tă yarda tsuntsayen sama su taɓa su da rana ko mugayen namun jeji da dare ba.
-
12 sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce,
“Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.
13 “Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena, 14 in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.
-
12 Ya mai da duhu abin rufuwarsa
gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi.
-
2 Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi.
Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna,
kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa,
zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.
Shows Read in context, Share and Copy.