41 Bible Verses About Astrology

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Astrology
  1. 11 Bala’i zai fāɗo a kanki,

    kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba.

    Masifa za tă fāɗo a kanki

    da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba;

    lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba

    za tă auko miki nan da nan.

    12 “Ki dai ci gaba, da sihirinki

    da kuma makarunki masu yawa,

    waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya.

    Mai yiwuwa ki yi nasara,

    mai yiwuwa ki jawo fargaba.

    13 Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai!

    Bari masananki na taurari su zo gaba,

    waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata,

    bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.

    14 Tabbas suna kama da bunnu;

    wuta za tă cinye su ƙaf.

    Ba za su ma iya ceton kansu

    daga ikon wutar ba.

    Ba wutar da wani zai ji ɗumi;

    ba wutar da za a zauna kusa da ita.

    15 Abin da za su iya yi miki ke nan kawai,

    waɗannan da kika yi ta fama da su

    kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya.

    Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa;

    babu ko ɗayan da zai cece ki.

  2. 9 Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can. 10 Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri, 11 ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu. 12 Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku. 13 Dole ku zama marasa zargi a gaban Ubangiji Allahnku.

    14 Al’ummai da za ku kora sukan saurari waɗannan masu maita, ko masu duba. Amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.

  3. 27 Daniyel ya amsa, “Babu wani mai hikima, ko mai sihiri, ko mai dabo ko mai duban da zai iya warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi, 28 amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne,

  4. 1 Ku ji abin da Ubangiji yana ce muku, ya gidan Isra’ila. 2 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “Kada ku koyi hanyoyin al’ummai

    ko ku razana game da alamun sararin sama,

    ko da yake al’ummai sun razana saboda su.

    3 Gama al’adun mutane banza ne;

    sukan yanke itace daga kurmi,

    sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago.

  5. 15 Ba ku ga wata siffa a ranar da Ubangiji ya yi magana da ku a Horeb daga wuta ba. Saboda haka ku lura da kanku sosai, 16 don kada ku lalace, ku kuma yi wa kanku gunki, siffa ta wani kama, ko a kamannin namiji, ko kuwa ta mace, 17 ko a kamannin wata dabba a duniya, ko na wani tsuntsun da yake tashi a sama, 18 ko kuwa a kamannin wata halittar da take rarrafe a ƙasa, ko na wani kifi a cikin ruwaye a ƙarƙashi. 19 Sa’ad da kuka ɗaga ido kuka kali sama, kuka ga rana da wata, da taurari, da dukan halittun sama, sai ku kula fa, kada ku jarrabtu, ku ce za ku yi musu sujada, ko ku bauta musu; abubuwan nan Ubangiji Allahnku ne ya rarraba wa dukan al’umman da suke ko’ina a ƙarƙashin sararin sama.

  6. 31 “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta?

    Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?

    32 Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu

    ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?

    33 Ka san dokokin sammai?

    Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?

  7. 14 Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15 bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. 16 Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. 17 Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, 18 su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.

  8. 10 Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki suka ce, “Babu wani mutum a duniyan nan da zai iya yin abin da sarki yake nema! Babu wani sarki mai daraja da girma wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya ga masu sihiri ko masu dabo ko masanan taurari. 11 Abin da sarki yake nema yana da wuya matuƙa. Babu wani da zai iya bayyana wannan ga sarki sai dai alloli; kuma ba su zama tare da ’yan adam.”

  9. 1 Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima 2 suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”

    3 Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima.

  10. 7 Sa’ad da masu sihiri, da masu dabo, da masanan taurari da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya fassarta mini mafarkin ba.

  11. 19 Sarki kuwa ya yi magana da su, sai ya gano cewa babu wani kamar Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya; don haka sai suka shiga yi wa sarki hidima. 20 A dukan al’amuran hikima da na fahimta wanda sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa sau goma.

  12. 2 In an sami wani namiji ko ta mace mai zama a cikinku, a ɗaya daga biranen da Ubangiji ya ba ku yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku ta wurin karya alkawarinsa, 3 wanda ya saba wa umarnina, har ya yi sujada ga waɗansu alloli, yana rusuna musu, ko ga rana, ko ga wata, ko kuwa ga taurarin sama, 4 in kuwa aka faɗa muku wannan, to, dole a bincika sosai. In kuwa gaskiya ne, aka kuma tabbatar cewa wannan abin ƙyama ya faru a cikin Isra’ila, 5 sai a ɗauki namijin, ko ta mace wanda ya aikata wannan mugun abu zuwa ƙofar birni, a jajjefe wannan mutum sai ya mutu. 6 Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku, za a iya kashe mutum, amma ba za a iya kashe mutum bisa ga shaida mutum guda ba. 7 Hannuwan shaidun ne za su zama na farko a kisan wanda ake zargin, sa’an nan hannuwan dukan mutane. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  13. 26 “ ‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa.

    “ ‘Kada ku yi duba ko sihiri.

    27 “ ‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku.

    28 “ ‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji.

  14. 3 Sa’ad da na dubi sammai,

    aikin yatsotsinka,

    wata da taurari

    waɗanda ka ajiye a wurarensu,

    4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,

    ɗan mutum da kake lura da shi?

  15. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

    1 Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;

    sararin sama suna furta aikin hannuwansa.

    2 Kowace rana tana yin jawabi;

    kowane dare yana nuna sani.

    3 Ba magana, ba kalmar da aka hurta,

    ba wani amon da aka ji daga gare su.

    4 Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,

    kalmominsu zuwa iyakokin duniya.

    A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,

    5 wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,

    kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.

    6 Takan taso daga ƙarshen sammai

    ta kewaye zuwa wancan;

    babu abin da yake ɓuya wa zafinta.

  16. 6 “ ‘Zan yi gāba da mutumin da ya juyo ga masu duba da bokaye, don yă yi karuwanci ta wurin bin su, zan kuma raba shi daga mutanensa.

  17. 19 Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai? 20 Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani.

  18. 2 Sai sarki ya sa aka tattara masa masu sihiri da masu dabo da bokaye da masanan taurari domin su faɗi abin da ya yi mafarki a kai. Da suka shigo suka tsaya a gaban sarki,

  19. 30 “ ‘Ku kiyaye Asabbacina, ku kuma girmama wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji.

    31 “ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  20. 27 “ ‘Namiji, ko ta macen da yake mai duba, ko maita a cikinku dole a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu; alhakin jininsu zai zauna a kansu.’ ”

  21. 8 (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare,

    wanda ya mai da duhu ya zama haske

    ya kuma baƙanta rana ta zama dare,

    yakan kwashe ruwan teku

    ya zubar a ƙasa,

    Ubangiji ne sunansa,

  22. 22 ku ƙi kowace mugunta.

  23. 23 Gama tawaye yana kama da zunubi na duba,

    girman kai kuma yana kama da bautar gumaka.

    Saboda ka ƙi maganar Ubangiji,

    shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”

  24. 4 “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda

    da kuma dukan mazaunan Urushalima.

    Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri,

    da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,

    5 waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki

    don su yi sujada ga rundunar taurari.

    Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji

    suke kuma rantsuwa da sunan Molek.

  25. 7 Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske;

    yana hana taurari yin haske.

    8 Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai

    ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.

    9 Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza,

    da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.

    10 Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa,

    mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.

  26. 3 Ya warkar da masu raunanar zuciya

    ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

    4 Ya lissafta yawan taurari

    ya kuma kira kowannensu da suna.

  27. 16 Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada. 17 Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.

    18 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari,

  28. 7 Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”

    8 Sa’an nan sai dukan masu hikima suka zo ciki, amma ba su iya karanta rubutun ba ko su faɗa wa sarki abin da yake nufi. 9 Saboda haka Sarki Belshazar ya firgita ƙwarai kuma fuskarsa ta ƙara ruɗewa. Hakimansa kuma suka rikice.

  29. 25 “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.

  30. 18 Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu. 19 Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin. 20 Ta haka maganar Ubangiji ta bazu ko’ina ta kuma yi ƙarfi.

  31. 19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

  32. 6 Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

  33. 13 Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba, 14 bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.

  34. 26 In na dubi rana cikin haskenta,

    ko kuma wata yana tafiyarsa,

    27 zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye,

    hannuna kuma ya sumbace su.

    28 Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan

    don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.

  35. 9 Duba, ranar Ubangiji tana zuwa,

    muguwar rana, mai hasala da zafin fushi,

    don ta mai da ƙasar kango

    ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.

    10 Taurarin sama da ƙungiyoyinsu

    ba za su ba da haskensu ba.

    Rana za tă yi duhu

    wata kuma ba zai ba da haskensa ba.

  36. 2 Za a shimfiɗa su a rana da wata da kuma dukan taurarin sammai, waɗanda suka ƙaunata suka kuma bauta wa, waɗanda suka bi suka nemi shawarar suka kuma yi wa sujada. Ba za a tattara su ko a binne su ba, amma za su zama kamar juji a jibge a ƙasa.

  37. 19 Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.”

    Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!

  38. 2 Gumaka suna maganganun ruɗu,

    masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya,

    suna faɗa mafarkan ƙarya

    suna ba da ta’aziyyar banza.

    Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki

    waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.

  39. 9 Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.

  40. 29 “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan

    “ ‘sai a duhunta rana,

    wata kuma ba zai ba da haskensa ba;

    taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama,

    za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’

    30 “A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.

  41. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.