36 Bible Verses About Bitterness

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Bitterness
  1. 14 Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji. 15 Ku lura fa kada wani yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai yă tsira har yă kawo rikici, yă kuma ƙazantar da mutane da yawa. 16 Ku lura kada wani yă zama mai fasikanci, ko marar tsoron Allah kamar Isuwa, wanda saboda ƙwaryar abinci ɗaya tak ya sayar da gādonsa na ɗan fari. 17 Daga baya, kamar yadda kuka sani, sa’ad da ya nemi yă gāji wannan albarka, aka ƙi shi. Bai sami zarafin tuba ba, ko da yake ya nemi albarkan nan da hawaye.

  2. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

  3. 14 Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15 Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.

  4. 25 A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”

  5. 20 Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta

    nagarta kuma mugunta,

    waɗanda suke mai da duhu haske

    haske kuma duhu,

    waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi

    zaƙi kuma ɗaci.

  6. 26 “Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, 27 kada kuma ku ba wa Iblis dama.

  7. 22 Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka. 23 Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.”

  8. 13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. 14 Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. 15 Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. 16 Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.

    17 Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. 18 Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.

  9. 19 Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

  10. 22 Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba. 23 Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara). 24 Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”

    25 Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi.

    A can Ubangiji ya yi musu doka da farilla, a can kuma ya gwada su. 26 Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”

    27 Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.

  11. 14 “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”

  12. 18 Bayan da firist ya sa matan ta tsaya a gaban Ubangiji, sai yă kunce gashin kanta, yă kuma sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi, yayinda shi kansa zai riƙe ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana. 19 Sa’an nan firist zai sa tă yi rantsuwa, yă kuma ce mata, “In ba wani mutumin da ya kwana da ke kuma ba ki kauce kin ƙazantar da kanki yayinda kike auren mijinki ba, kada wannan ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, yă cuce ki.

  13. 1 “Na gaji da rayuwa;

    saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi

    yadda raina yake jin ba daɗi.

  14. 10 Kowace zuciya ta san ɓacin ranta,

    kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa.

  15. 25 Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai,

    bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.

  16. 25 Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa

    da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.

  17. 17 Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne. 18 Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. 19 Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji. 20 A maimakon haka,

    “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi;

    in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha.

    Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”

    21 Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

  18. 19 ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba, 20 gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.

  19. 14 Suka baƙanta wa Isra’ilawa rai da bauta mai wuya, ta wurin sa su yin tubali da yumɓu, da kuma kowace irin bauta a gonaki. A cikin dukan ayyukansu, Masarawa ba su ji tausayinsu ba ko kaɗan.

  20. 23 “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci. 24 Sai yă sa macen tă sha ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, wannan ruwa kuwa zai shiga cikinta yă kawo mata wahala mai zafi.

  21. 11 Za su yi bikin da yamma, a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Za su ci naman tunkiya, tare da burodi marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.

  22. 11 “Saboda haka ba zan yi shiru ba;

    zan yi magana cikin ɓacin raina,

    zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina.

  23. 13 Ya harbi zuciyata

    da kibiyoyin kwarinsa.

    14 Na zama abin dariya ga mutanena duka;

    suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.

    15 Ya cika ni da kayan ɗaci

    ya gundure ni da abinci mai ɗaci.

  24. 12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

  25. 34 Sa’ad da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya fashe da kuka mai zafi kuma da ƙarfi, ya ce wa mahaifinsa, “Ka albarkace ni, ni ma, baba!”

  26. 8 A wannan dare, za su gasa naman, su ci da ganyaye masu ɗaci, da kuma burodi marar yisti.

  27. 3 Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma,

    maganarta tana da sulɓi fiye da mai;

    4 amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya,

    mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.

  28. 11 Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya?

  29. 11 sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.

  30. 1 Sa’an nan Ayuba ya amsa,

    2 “Ko a yau, ina kuka mai zafi;

    hannunsa yana da nauyi duk da nishin da nake yi.

    3 Da a ce na san inda zan same shi;

    da a ce zan iya zuwa wurin da yake zama!

    4 Zan kai damuwata wurinsa

    in yi gardama da shi.

  31. 19 Na tuna da azabata da kuma sintiri,

    da na yi ta yi da ɗacin rai.

    20 Na tuna su sosai,

    sai kuma na ji ba daɗi a raina.

  32. 10 Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki

    kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka.

    Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki

    za ku kuma aske kawunanku.

    Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi

    kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci.

  33. 1 Sa’ad da Mordekai ya sami labari game da dukan abin da aka yi, sai ya yayyage rigunansa, ya sanya tsummokin makoki, ya zuba toka a kā, ya kuma shiga ciki birni yana kuka mai zafi da ƙarfi.

  34. 12 Ƙiyayya kan haddasa wahala,

    amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.

  35. 7 Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma

    amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.

  36. 26 Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci

    mace wadda take tarko ne,

    wadda zuciyarta tarko ne

    wadda kuma hannuwanta sarƙa ne.

    Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata,

    amma za tă kama mai zunubi.