41 Bible Verses About Loving Your Husband

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Loving Your Husband
  1. 22 Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. 23 Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. 24 To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

    25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. 27 Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. 28 Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. 29 Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya, 30 gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.

  2. 1 Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2 Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

    3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4 Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5 su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

  3. 4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

    8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.

  4. 18 Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

    19 To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. 20 Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.

    Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

    23 Sai mutumin ya ce,

    “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

    nama kuma na namana.

    Za a ce da ita ‘mace,’

    gama an ciro ta daga namiji.”

    24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

    25 Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.

  5. 7 Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.

  6. 18 Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

    19 Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

  7. 8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

  8. 12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

  9. 9 Biyu sun fi ɗaya,

    gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

    10 In ɗaya ya fāɗi,

    abokinsa zai taimake shi yă tashi.

    Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi

    ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!

    11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.

    Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?

    12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,

    mutum biyu za su iya kāre kansu.

    Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.

  10. 2 Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. 3 Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. 4 Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. 5 Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

  11. 27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

    Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

    Miji da mace ya halicce su.

    28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”

  12. 5 Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka. 6 Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’ 7 ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, 8 su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’ Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. 9 Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”

  13. 33 Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.

  14. 11 Mijinta yana da cikakken amincewa da ita

    kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.

    12 Takan yi masa alheri ba mugunta ba,

    dukan kwanakin ranta.

    13 Takan zaɓi ulu da lilin

    ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.

    14 Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne

    tana kawo abincinta daga nesa.

    15 Takan farka tun da sauran duhu;

    ta tanada wa iyalinta abinci

    ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.

    16 Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta;

    daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.

    17 Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru;

    hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.

    18 Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta,

    kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.

    19 Da hannunta take riƙe abin kaɗi

    ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.

    20 Takan marabci talakawa

    takan kuma taimaki masu bukata.

  15. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.

  16. 7 Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.

    8 To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake. 9 Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.

    10 Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta. 11 In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yă saki matarsa.

    12 Ga sauran kuwa (ni ne fa na ce ba Ubangiji ba), in wani ɗan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yă sake ta. 13 In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yă zauna tare da ita, kada tă kashe auren. 14 Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba ’ya’yanku ba za su zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne.

    15 Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne. 16 Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?

  17. 6 Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka,

    kamar hatimi a hannunka;

    gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa,

    kishinta yana kamar muguntar kabari,

    yana ƙuna kamar wuta mai ci,

    kamar gagarumar wuta.

    7 Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba,

    koguna ba za su iya kwashe ta ba.

    In wani zai bayar da

    dukan dukiyar gidansa don ƙauna,

    za a yi masa dariya ne kawai.

  18. 13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

  19. 1 A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku. 2 Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna. 3 Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna.

  20. 7 Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. 8 Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne.

  21. 5 Gama Mahaliccinki shi ne mijinki,

    Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki;

    ana ce da shi Allahn dukan duniya.

  22. 12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

  23. 3 Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai;

    ka ɗaura su kewaye da wuyanka,

    ka rubuta su a allon zuciyarka.

    4 Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau

    a gaban Allah da kuma a gaban mutane.

  24. 2 Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure. 3 Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.

  25. 8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.

  26. 1 Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2 Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. 3 Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. 4 Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5 ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6 Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7 Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah.

  27. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

  28. 4 Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

  29. 15 Ku sha ruwa daga tankinku,

    ruwa mai gudu daga rijiyarku.

    16 In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje,

    rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?

    17 Bari su zama naka kaɗai,

    don kada ka raba da baƙi.

    18 Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,

    bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

    19 Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,

    bari mamanta su ishe ka kullum,

    bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

    20 Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali?

    Don me za ka rungume matar wani?

  30. 22 Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau

    ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

  31. 14 Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne,

    amma mace mai basira daga Ubangiji ne.

  32. 18 Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 19 Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye.

    20 Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.

  33. 31 “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’ 32 Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.

  34. 11 Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. 12 In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

  35. 4 Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. 5 Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.

  36. 10 Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.

  37. 39 Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da ’yanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji.

  38. 3 To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.

  39. 28 Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu.

  40. 1 Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba

  41. 12 Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.