Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 95

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;

bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.

2 Bari mu zo gabansa da godiya

mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,

babban Sarki a bisa dukan alloli.

4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,

ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,

da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,

bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

7 gama shi ne Allahnmu

mu mutanen makiyayansa ne,

garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.

Yau, in kuka ji muryarsa,

8 “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba,a

kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massab a hamada,

9 inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni,

ko da yake sun ga abin da na yi.

10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara;

na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce,

kuma ba su san hanyoyina ba.’

11 Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina,

‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

Translator’s notes

  1. 95:8 (a): Meriba yana nufin faɗa.
  2. 95:8 (b): Massa yana nufin gwaji.

Zabura 95