Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 47

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce.

1 Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai;

ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.

2 Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne,

Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!

3 Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu,

mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.

4 Ya zaɓar mana gādonmu,

abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela

5 Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki,

Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.

6 Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai;

ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.

7 Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya;

ku rera zabura ta yabo gare shi.

8 Allah yana mulki a bisa al’ummai;

Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.

9 Manyan mutanen al’ummai sun taru

a matsayin mutanen Allah na Ibrahim,

gama sarkunan duniya na Allah ne;

ana ɗaukaka shi ƙwarai.

Zabura 47