Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 8

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.a Zabura ta Dawuda.

1 Ya Ubangiji, shugabanmu,

sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

Ka kafa ɗaukakarka

bisa sammai.

2 Daga leɓunan yara da jarirai

ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka

da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

3 Sa’ad da na dubi sammai,

aikin yatsotsinka,

wata da taurari

waɗanda ka ajiye a wurarensu,

4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,

ɗan mutum da kake lura da shi?

5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allahb

ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;

ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

7 dukan shanu da tumaki,

da kuma namun jeji,

8 tsuntsayen sararin sama

da kifin teku,

da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.

9 Ya Ubangiji, shugabanmu,

sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

Translator’s notes

  1. 8:0 (a): Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce.
  2. 8:5 (b): Ko kuwa da rayayyun sama

Zabura 8