Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 87

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce.

1 Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.

2 Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona

fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.

3 Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke

Ya birnin Allah, Sela

4 “Zan lissafta Rahab

a cikin waɗanda suka san ni,

Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush,

zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”

5 Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce,

“Wannan da wancan an haifa a cikinta,

Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”

6 Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa,

“An haifi wannan a Sihiyona.” Sela

7 Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera,

“Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”

Zabura 87