Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 53

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat.a Wani maskilb na Dawuda.

1 Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa,

“Ba Allah.”

Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau;

babu wani mai aikata abu mai kyau.

2 Allah yana duba daga sama

a kan ’ya’yan mutane

yă ga ko akwai wani wanda ya gane,

wani wanda yake neman Allah.

3 Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace;

babu guda da yake aikata abu mai kyau,

babu ko ɗaya.

4 Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo?

Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi,

ba sa kuma kira ga Allah.

5 Ga shi fa, sun firgita don tsoro,

ko da yake babu dalilin tsoro,

gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa,

za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su.

6 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana!

Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa,

bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!

Translator’s notes

  1. 53:0 (a): Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
  2. 53:0 (b): Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.

Zabura 53