Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 54

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskila ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?”

1 Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka;

ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.

2 Ka ji addu’ata, ya Allah;

ka saurari maganar bakina.

3 Baƙi suna kawo mini hari;

mutane marasa imani suna neman raina,

mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela

4 Tabbatacce Allah ne mai taimakona,

Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.

5 Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina;

cikin amincinka ka hallaka su.

6 Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka;

zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.

7 Gama ya cece ni daga dukan wahalolina,

idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.

Translator’s notes

  1. 54:0 (a): Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.

Zabura 54