Dawuda a Jejin Zif da Mawon

1059 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Sama’ila 23:13–23

13 Saboda haka Dawuda da mutanensa wajen mutum ɗari shida suka bar Keyila, suka yi ta tafiya daga wannan wuri zuwa wancan. Sa’ad da aka gaya wa Shawulu cewa Dawuda ya tsere daga Keyila, sai ya fasa tafiya can.

14 Dawuda ya zauna a jeji cikin kogunan duwatsu da kuma tuddan jejin Zif. Kowace rana Shawulu ya yi ta neman Dawuda amma Allah bai bashe Dawuda a hannunsa ba.

15 A lokacin da Dawuda yana zaune a Horesh cikin jejin Zif, ya sami labari cewa Shawulu ya fito don yă kashe shi. 16 Yonatan ɗan Shawulu kuwa ya tafi wurin Dawuda a Horesh, ya ƙarfafa shi yă dogara ga Allah. 17 Ya ce, “Kada ka ji tsoro, mahaifina Shawulu ba zai taɓa sa hannu a kanka ba. Za ka zama sarki a Isra’ila, ni kuma in zama na biyu gare ka. Kai, ko mahaifina Shawulu ma ya san da haka.” 18 Su biyunsu kuwa suka ɗaura yarjejjeniya a gaban Ubangiji. Sai Yonatan ya koma gida amma Dawuda ya zauna Horesh.

19 Zifawa suka tafi wurin Shawulu a Gibeya suka ce masa, “Ashe, ba Dawuda ne yake ɓuya a cikinmu a kogwannin duwatsu a Horesh a bisan tudun Hakila, kudu da Yeshimon ba? 20 Yanzu, ya sarki, ka gangaro, ka zo a duk lokacin da ka ga ya yi maka, ka zo mu kuma hakkinmu ne mu bashe shi a hannun sarki.”

21 Shawulu ya ce, “Ubangiji ya yi muku albarka, gama kun damu da ni. 22 Ku tafi ku ƙara shiri. Ku san inda yakan tafi, wane ne kuma ya gan shi a can. An gaya mini cewa shi mai wayo ne sosai. 23 Ku binciko duk wuraren da yakan ɓuya, sai ku dawo ku gaya mini tabbataccen labari. Sa’an nan zan tafi tare da ku in yana can. Zan nemi shi ko’ina cikin dukan kabilar Yahuda.”

Zabura 54

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?”

1 Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka;

ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.

2 Ka ji addu’ata, ya Allah;

ka saurari maganar bakina.

3 Baƙi suna kawo mini hari;

mutane marasa imani suna neman raina,

mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela

4 Tabbatacce Allah ne mai taimakona,

Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.

5 Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina;

cikin amincinka ka hallaka su.

6 Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka;

zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.

7 Gama ya cece ni daga dukan wahalolina,

idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.

1 Sama’ila 23:24–28

24 Sai suka tashi suka koma Zif, suka sha gaban Shawulu. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon cikin Araba, kudu da Yeshimon. 25 Shawulu da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya gangara cikin duwatsu ya zauna a cikin jejin Mawon. Sa’ad da Shawulu ya ji haka, sai ya tafi jejin Mawon yana fafaran Dawuda.

26 Shawulu yana tafiya a gefe ɗaya na dutsen, Dawuda da mutanensa kuma suna a wancan gefe, suna hanzari su ɓace wa Shawulu. Sa’ad da Shawulu da sojojinsa suka kusa cimma Dawuda da mutanensa don su kama su, 27 sai wani manzo ya zo wurin Shawulu yana cewa, “Ka koma da sauri, Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.” 28 Shawulu kuwa ya janye daga fafaran Dawuda, ya tafi yă ƙara da Filistiyawa. Dalilin ke nan da ake kiran wannan wuri Sela Hammalekot, wato, dutsen tserewa.