Dawuda a En Gedi
1058 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
29 Dawuda kuwa ya haura daga can ya zauna a kogwannin duwatsun En Gedi.
24:1 Bayan da Shawulu ya komo daga fafaran Filistiyawa, sai aka gaya masa cewa, “Dawuda yana can a Jejin En Gedi.” 2 Saboda haka Shawulu ya zaɓi mutum dubu uku daga cikin dukan Isra’ila, suka fita neman Dawuda da mutanensa kusa da Duwatsun Awakin Jeji.
3 Da Shawulu ya isa inda ake ajiye garken tumaki a bakin hanya inda akwai kogo, sai ya shiga ciki kogon don yă yi bayan gari. Dawuda da mutanensa kuwa suna can zaune a ƙurewar kogon. 4 Mutanen Dawuda suka ce, wannan rana ce Ubangiji ya yi magana ya ce maka, “Zan ba da maƙiyinka a hannunka domin ka yi abin da ka ga dama da shi.” Sai Dawuda ya tashi a hankali ya je ya yanke shafin rigar Shawulu.
5 Daga baya Dawuda ya damu domin ya yanke shafin rigar Shawulu. 6 Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji yă sawwaƙe in yi abu haka ga shugabana da Ubangiji ya shafe, ko in ɗaga hannuna in kashe shi, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.” 7 Da wannan magana Dawuda ya kwaɓi mutanensa, bai yarda su fāɗa wa Shawulu ba. Shawulu kuwa ya bar kogon ya yi tafiyarsa.
8 Daga baya Dawuda ya fita daga kogon sai ya kira Shawulu ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki!” Da Shawulu ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. 9 Ya ce wa Shawulu, “Me ya sa kake saurari mutanen da suke cewa, ‘Dawuda ya dāge yă cuce ka’? 10 Yau ka ga da idonka yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a cikin kogon nan. Waɗansu sun ce mini in kashe ka, amma na bar ka, na ce, ‘Ba zan sa hannuna a kan shugabana ba, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.’ 11 Babana, duba, ga shafin rigarka a hannuna, na yanke shafin rigarka amma ban kashe ka ba. Yanzu ka gane ka kuma sani cewa ba ni da laifin aikata kome ko tayarwa, ban yi maka laifi ba, amma kana farautar raina. 12 Ubangiji zai shari’anta tsakanina da kai. Ubangiji zai sāka mini laifin da ka yi mini, amma ni kam ba zan taɓa ka ba. 13 Kamar yadda karin maganan nan na dā ya ce, ‘Daga cikin masu mugunta, mugunta ke fitowa,’ hannuna dai ba zai taɓa ka ba.
14 “Wane ne sarkin Isra’ila, ka fito kake bi? Wa kake kora? Kana bin mataccen kare ko kuɗin cizo? 15 Ubangiji yă zama alƙali, yă yi shari’a tsakanina da kai, bari Ubangiji yă duba, yă tsaya mini, yă nuna ba ni da laifi.”
16 Da Dawuda ya gama wannan magana, sai Shawulu ya ce, “Muryarka ke nan ɗana Dawuda?” Sai ya fasa da kuka. 17 Ya ce, “Ka fi ni gaskiya, ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta. 18 Ga shi yanzu ka faɗa mini alherin da ka yi mini. Ubangiji ya bashe ni a hannunka amma ba ka kashe ni ba. 19 In mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi yă tafi lafiya ba tare da yin masa rauni ba? Ubangiji yă sāka maka, gama ka nuna mini alheri a yau. 20 Na sani tabbatacce za ka zama sarki. Masarautar Isra’ila za tă kahu a hannunka. 21 Yanzu ka rantse mini da Ubangiji cewa ba za ka hallaka zuriyarta ko ka share sunana daga iyalin mahaifina ba.”
22 Sai Dawuda ya rantse wa Shawulu. Sa’an nan Shawulu ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka haura zuwa wurin ɓuya.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo.
1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai,
gama a gare ka raina yake samun mafaka.
Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka
sai masifar ta wuce.
2 Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka,
ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.
3 Ya aika daga sama ya kuwa cece ni,
yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Sela
Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.
4 Ina tsakiyar zakoki;
ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane,
mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi,
waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.
5 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
6 Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna,
damuwa ta sha ƙarfina.
Sun haƙa rami a hanyata,
amma su kansu suka fāɗa a cikinta. Sela
7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah,
zuciyata tana nan daram;
zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
8 Ka farka, raina!
Ku farka, garaya da molo!
Zan sa safe yă farka.
9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai a cikin mutane.
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;
amincinka na kaiwa sarari.
11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.
58:1 Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai?
Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?
2 Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci,
da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya.
3 Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce;
daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata.
4 Dafinsu ya yi kamar dafin maciji,
kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa,
5 da ba ya jin muryar gardi,
kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama.
6 Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah;
ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji!
7 Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa;
sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke.
8 Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya,
kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana.
9 Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa,
ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.
10 Masu adalci za su yi murna sa’ad da aka rama musu,
sa’ad da suka wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.
11 Sa’an nan mutane za su ce,
“Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai;
tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.”
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda.
1 Ya Allah, kai ne Allahna,
da nacewa na neme ka;
raina yana ƙishinka,
jikina yana marmarinka,
cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye
inda babu ruwa.
2 Na gan ka a wuri mai tsarki
na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,
leɓunana za su ɗaukaka ka.
4 Zan yabe ka muddin raina,
kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
5 Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau;
da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
6 A gadona na tuna da kai;
ina tunaninka dukan dare.
7 Domin kai ne mai taimakona,
ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
8 Raina ya manne maka;
hannunka na dama yana riƙe da ni.
9 Su da suke neman raina za su hallaka;
za su gangara zuwa zurfafan duniya.
10 Za a bayar da su ga takobi
su kuma zama abincin karnukan jeji.
11 Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah;
dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi,
amma za a rufe bakunan maƙaryata.