Dawuda a Keyila

1060 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Sama’ila 23:1

1 Sa’ad da aka ce wa Dawuda, “Duba ga Filistiyawa suna yaƙi da mutanen Keyila, suna kwashe musu hatsi a masussukai.”

1 Sama’ila 22:20–23

20 Amma Abiyatar ɗan Ahimelek jikan Ahitub ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda. 21 Abiyatar gaya wa Dawuda cewa, “Shawulu ya hallaka firistocin Ubangiji.” 22 Dawuda ya ce wa Abiyatar, “Lalle a wancan ranar, sa’ad da na ga Doyeg mutumin Edom a can, na san tabbatacce zai gaya wa sarki. Ni ne sanadin mutuwar dukan iyalin mahaifinka. 23 Ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro mutumin da yake neman ranka, yana nema raina ma. Ka zauna lafiya tare da ni.”

1 Sama’ila 23:6

6 (Abiyatar ɗan Ahimelek ya zo da efod sa’ad da ya gudo zuwa wurin Dawuda a Keyila.)

1 Sama’ila 23:2–5

2 Sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya ce, “In tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?”

Ubangiji kuwa ya ce masa, “Jeka ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci Keyila.”

3 Amma mutanen Dawuda suka ce masa, “Ga shi, a nan ma a Yahuda muna jin tsoro, balle mu tafi Keyila mu yi yaƙi da sojojin Filistiyawa!”

4 Dawuda ya sāke nemi nufin Ubangiji, sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka gangara zuwa Keyila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.” 5 Sa’an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Keyila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kwashe musu shanunsu, suka jijji wa Filistiyawa ƙwarai, suka cece mutanen Keyila daga hannunsu.

1 Sama’ila 23:7–12

7 Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya tafi Keyila, sai ya ce, “Allah ya bashe shi a hannuna, domin Dawuda ya kulle kansa ke nan da ya shiga birnin da yake da ƙofofin da ake kulle da ƙarafa.” 8 Shawulu ya kira dukan sojojinsa don yaƙi, su gangaro zuwa Keyila su mamaye Dawuda da mutanensa.

9 Da Dawuda ya ji labari Shawulu yana shirya hanyar da zai kashe shi, sai ya ce wa Abiyatar firist, “Kawo mini efod a nan.” 10 Dawuda ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bawanka ya sami labari cewa tabbatacce Shawulu yana shirin zuwa Keyila yă hallaka garin saboda ni. 11 Mutanen Keyila za su bashe ni a gare shi? Shawulu zai gangaro nan kamar yadda bawanka ya sami labari? Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka gaya wa bawanka.”

Ubangiji ya ce, “Zai zo.”

12 Dawuda ya sāke cewa, “Mutanen Keyila za su bashe ni da mutanena ga Shawulu?”

Ubangiji ya ce, “Za su yi.”

Zabura 31

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1 A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka;

kada ka bari in taɓa shan kunya;

ka cece ni cikin rahamarka.

2 Ka juye kunnenka gare ni,

ka zo da sauri ka cece ni;

ka zama dutsen mafakata,

mafaka mai ƙarfi na cetona.

3 Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata,

saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.

4 Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini,

gama kai ne mafakata.

5 Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna;

ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.

6 Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza;

na dogara ga Ubangiji.

7 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikin ƙaunarka,

gama ka ga azabata

ka kuma san wahalar raina.

8 Ba ka ba da ni ga abokin gāba ba

amma ka sa ƙafafuna a wuri mai sarari.

9 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama ina cikin damuwa;

idanuna sun gaji da baƙin ciki,

raina da jikina sun tafke tilis.

10 Baƙin ciki ya rufe raina

shekaruna sun cika da nishi;

ƙarfina ya karai saboda azaba,

ƙasusuwana kuma sun gaji tiƙis.

11 Saboda dukan abokan gābana,

Na zama tamƙar abin reni na maƙwabtana;

na zama abin tsoro ga abokaina,

waɗanda suka gan ni a titi sukan gudu daga gare ni.

12 An manta da ni sai ka ce na mutu;

na zama kamar fasasshen kasko.

13 Gama nakan ji raɗe-raɗen mutane masu yawa;

akwai tsoro a kowane gefe;

suna ƙulla maƙarƙashiya a kaina

suna shirya su ɗauke raina.

14 Amma na dogara gare ka, ya Ubangiji;

na ce, “Kai ne Allahna.”

15 Lokutana suna a hannuwanka;

ka cece ni daga abokan gābana

da kuma daga waɗanda suke fafara ta.

16 Bari fuskarka ta haskaka a kan bawanka;

ka cece ni da ƙaunarka marar ƙarewa.

17 Kada ka bari in sha kunya, ya Ubangiji,

gama na yi kuka gare ka;

amma bari mugaye su sha kunya

su kuma kwanta shiru a cikin kabari.

18 Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu,

gama da fariya da reni

suna magana da girman kai a kan adalai.

19 Alherinka da girma yake,

wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka,

wanda ka mayar a gaban mutane

a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.

20 Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su

daga makircin mutane;

a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya

daga harsuna masu zagi.

21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,

gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni

sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni.

22 Cikin tsorona na ce,

“An yanke ni daga gabanka!”

Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai

sa’ad da na kira gare ka don taimako.

23 Ku ƙaunaci Ubangiji, dukanku tsarkakansa!

Ubangiji yakan adana amintattu,

amma masu girman kai yakan sāka musu cikakke.

24 Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa,

dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.