Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 113

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Yabi Ubangiji.a

Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji,

ku yabi sunan Ubangiji.

2 Bari a yabi sunan Ubangiji,

yanzu da har abada kuma.

3 Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa,

a yabi sunan Ubangiji.

4 Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai,

ɗaukakarsa a bisa sammai

5 Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu,

Wannan mai zama a kursiyi can bisa,

6 wanda yake sunkuya yă dubi

sammai da duniya?

7 Yakan tā da matalauta daga ƙura

yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;

8 ya zaunar da su tare da sarakuna,

tare da sarakunan mutanensu.

9 Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta

ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki.

Yabi Ubangiji.

Translator’s notes

  1. 113:1 (a): Da Ibraniyanci Hallelu Ya, haka ma a aya 9.

Zabura 113