Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 56

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da murya “Kurciya a Itatuwan Oak Mai Nisa.” Ta Dawuda. Wani miktam.a Sa’ad da Filistiyawa suka kama shi a birnin Gat.

1 Ka yi mini jinƙai,

ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi;

dukan yini suna matsa harinsu.

2 Masu ɓata sunana suna bina dukan yini;

da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.

3 Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

4 Ga Allah wanda maganarsa nake yabo

ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.

Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

5 Dukan yini sun yi ta juya maganata;

kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni.

6 Sun haɗa baki, sun ɓoye,

suna kallon takawata

suna a shirye su ɗauki raina.

7 Sam, kada ka bari su kuɓuce;

cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai.

8 Ka lissafta makokina;

ka jera hawayena a littafinka,b

ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

9 Ta haka abokan gābana za su juya da baya

sa’ad da na nemi taimako.

Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.

10 Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa,

ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,

11 ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.

Me mutum zai iya yi mini?

12 Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah;

zan miƙa hadayuna na godiya gare ka.

13 Gama ka cece nic daga mutuwa

da kuma ƙafafun daga tuntuɓe,

don in yi tafiya a gaban Allah

cikin hasken rai.d

Translator’s notes

  1. 56:0 (a): Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
  2. 56:8 (b): Ko kuwa / ka sa hawayena a salkan ruwan inabinka
  3. 56:13 (c): Ko kuwa raina
  4. 56:13 (d): Ko kuwa a ƙasar masu rai

Zabura 56