Dawuda Ya Gudu zuwa wurin Ahimelek a Nob
1060 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Dawuda ya tafi Nob a wurin Ahimelek firist. Da Ahimelek ya gan shi sai ya firgita ya ce, “Me ya sa kai kaɗai ne? Me ya sa ba wani tare da kai?”
2 Dawuda ya ce wa Ahimelek firist, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya sa in yi. Na faɗa wa mutanena inda za su same ni. 3 Yanzu, me kake da shi a hannu? Ka ba ni burodi guda biyar, ko wani abu da kake da shi a nan.”
4 Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.”
5 Dawuda ya ce, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena sukan keɓe kansu a koyaushe suka tashi ’yar tafiya, balle fa a yau!” 6 Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar.
7 A ranar kuwa, ɗaya daga cikin bayin Shawulu yana can, a tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom, shugaban makiyayan Shawulu.
8 Dawuda ya ce wa Ahimelek, “Ba ka da māshi ko takobi a nan? Ban kawo māshina ko wani makami ba gama saƙon sarki ya zo mini da gaggawa.”
9 Sai firist ya ce, “Takobin Goliyat Bafilistin nan wanda ka kashe a Kwarin Ela yana nan. An naɗe shi da ƙyallen aka ajiye a bayan Efod, in kana so, sai ka ɗauka. Ba wani takobi kuma sai wancan.”
Dawuda ya ce, “Ba ni shi, ai, ba wani kamar sa.”
Dawuda Ya Gudu zuwa wurin Akish, Sarkin Gat
10 A ranar, Dawuda ya gudu daga wajen Shawulu ya tafi wuri Akish sarkin Gat. 11 Amma bayin Akish suka ce masa, “Wannan ba shi ne Dawuda sarkin ƙasar ba? Ashe, ba shi ne aka yi ta yin waƙoƙi a kansa, ana raye-raye, ana cewa,
“Shawulu ya kashe dubbai,
Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai?”
12 Dawuda ya riƙe waɗannan kalmomi a zuciyarsa, ya kuma ji tsoron Akish sarkin Gat sosai. 13 Don haka sai ya yi kamar ya taɓu a gabansu. A duk lokacin da yake tare da su, sai yă yi kamar ya haukace. Ya yi ta zāne-zāne a ƙofofi, ya bar miyau yana ta bin gemunsa.
14 Akish ya ce wa bayinsa, “Duba, wannan mutum yana hauka. Me ya sa kuka kawo shi a wurina? 15 Na rasa masu hauka ne da za ku kawo mini wannan mutum yă yi ta hauka a gabana? Dole ne wannan mutum yă shiga gidana?”
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da murya “Kurciya a Itatuwan Oak Mai Nisa.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Filistiyawa suka kama shi a birnin Gat.
1 Ka yi mini jinƙai,
ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi;
dukan yini suna matsa harinsu.
2 Masu ɓata sunana suna bina dukan yini;
da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.
3 Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.
4 Ga Allah wanda maganarsa nake yabo
ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum mai mutuwa zai yi mini?
5 Dukan yini sun yi ta juya maganata;
kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni.
6 Sun haɗa baki, sun ɓoye,
suna kallon takawata
suna a shirye su ɗauki raina.
7 Sam, kada ka bari su kuɓuce;
cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai.
8 Ka lissafta makokina;
ka jera hawayena a littafinka,
ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?
9 Ta haka abokan gābana za su juya da baya
sa’ad da na nemi taimako.
Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.
10 Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa,
ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,
11 ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?
12 Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah;
zan miƙa hadayuna na godiya gare ka.
13 Gama ka cece ni daga mutuwa
da kuma ƙafafun daga tuntuɓe,
don in yi tafiya a gaban Allah
cikin hasken rai.
Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi.
1 Zan gode wa Ubangiji kullayaumi;
yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.
2 Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji;
bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.
3 Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni;
bari mu ɗaukaka sunansa tare.
4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;
ya cece ni daga dukan tsoro.
5 Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;
fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.
6 Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi;
ya cece shi daga dukan wahalarsa.
7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,
ya kuwa cece su.
8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;
mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.
9 Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,
gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.
10 Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa,
amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.
11 Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;
zan koya muku tsoron Ubangiji.
12 Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa
yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,
13 ka kiyaye harshenka daga mugunta
da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
14 Juyo daga mugunta ku yi alheri;
nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
15 Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;
16 fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta,
don yă sa a manta da su a duniya.
17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;
yakan cece su daga dukan wahalarsu.
18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,
amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;
20 yakan tsare dukan ƙasusuwansa,
ba ko ɗayansu da zai karye.
21 Mugunta zai kashe mugu;
za a hukunta abokan gāban adalai.
22 Ubangiji yakan cece bayinsa;
ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.