Dawuda Ya Gudu zuwa Kogon Adullam

1060 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Sama’ila 22:1

1 Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da ’yan’uwansa da kuma iyalan mahaifinsa suka ji labari, sai suka tafi can wurinsa.

Zabura 142

Maskil ne ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce.

1 Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji;

na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.

2 Na kawo gunagunina a gabansa;

a gabansa na faɗa wahalata.

3 Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina,

kai ne wanda ya san hanyata.

A hanyar da nake tafiya

mutane sun kafa mini tarko.

4 Duba ta damata ka gani;

babu wanda ya kula da ni.

Ba ni da mafaka;

babu wanda ya kula da raina.

5 Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

Na ce, “Kai ne mafakata,

rabona a ƙasar masu rai.”

6 Ka saurari kukata,

gama ina cikin matsananciyar bukata;

ka cece ni daga waɗanda suke fafarata,

gama sun fi ni ƙarfi sosai.

7 Ka ’yantar da ni daga kurkuku,

don in yabi sunanka.

Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni

saboda alherinka gare ni.

1 Sama’ila 22:2

2 Dukan mutanen da suke cikin wahala, da waɗanda ake binsu bashi, da masu damuwoyi, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Yawansu ya kai ɗari huɗu.

1 Tarihi 12:8–18

8 Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.

9 Ezer shi ne babba,

Obadiya shi ne mai binsa a shugabanci, Eliyab na uku,

10 Mismanna na huɗu, Irmiya na biyar,

11 Attai na shida, Eliyel na bakwai,

12 Yohanan na takwas, Elzabad na tara,

13 Irmiya na goma da kuma Makbannai na goma sha ɗaya.

14 Waɗannan mutanen Gad shugabannin mayaƙa ne; ƙarami a cikinsu zai iya ƙara da mutum ɗari, kuma babba a cikin zai iya ƙara da dubu. 15 Su ne suka haye Urdun a wata na farko sa’ad da kogin ya yi ambaliya, suka kuma kori duk mai rai a kwarin, na wajen gabas da na wajen yamma.

16 Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa. 17 Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.”

18 Sai Ruhu ya sauko a kan Amasai, shugaban Talatin nan, sai ya ce,

“Mu naka ne, ya Dawuda!

Muna tare da kai, ya ɗan Yesse!

Nasara, nasara gare ka,

nasara kuma ga waɗanda suke taimakonka.

Gama Allahnka zai taimake ka.”

Saboda haka Dawuda ya karɓe su ya kuma mai da su shugabannin ƙungiyoyin maharansa.

2 Sama’ila 23:13–17

13 A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim. 14 Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem. 15 Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!” 16 Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji. 17 Sai ya ce, “Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba.

Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.

1 Tarihi 11:15–19

15 Wata rana uku cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara wurin Dawuda zuwa dutse a kogon Adullam, yayinda ƙungiyar Filistiyawa suke sansani a Kwarin Refayim. 16 A lokacin Dawuda yana cikin mafaka, sojojin Filistiyawa kuma suna a Betlehem. 17 Dawuda ya ji marmarin ruwan sha sai ya ce, “Kash, a ce wani zai sami mini ruwan sha daga rijiya kusa da ƙofar Betlehem mana!” 18 Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda. Amma ya ƙi yă sha; a maimako, sai ya zubar da shi a gaban Ubangiji. 19 Ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka, ya kamata in sha jinin waɗannan mutanen da suka yi kasai da rayukansu?” Domin sun yi kasai da rayukansu don su dawo da shi, Dawuda bai sha shi ba.

Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.