Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 112

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 aYabi Ubangiji.b

Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,

wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.

2 ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar;

tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.

3 Wadata da arziki suna a cikin gidansa,

adalcinsa zai dawwama har abada.

4 Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya,

mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.c

5 Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,

shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.

6 Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba;

za a tuna da mai adalci har abada.

7 Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba;

zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.

8 Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba;

a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.

9 Ya rarraba kyautansa ga matalauta,

adalcinsa zai dawwama har abada;

za a ɗaga ƙahonsad sama da bangirma.

10 Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi,

zai ciza haƙora yă kuma lalace;

sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.

Translator’s notes

  1. 112:0 (a): Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi.
  2. 112:1 (b): Da Ibraniyanci Hallelu Ya
  3. 112:4 (c): Ko kuwa / gama Ubangiji mai alheri ne, mai tausayi da kuma mai adalci.
  4. 112:9 (d): Ƙaho a nan yana nufin girma.

Zabura 112