Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 67

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa.

1 Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu

yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela

2 don a san hanyoyinka a duniya,

cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.

3 Bari mutane su yabe ka, ya Allah;

bari dukan mutane su yabe ka.

4 Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki,

gama kana mulkin mutanenka da adalci

kana kuma bi da al’umman duniya. Sela

5 Bari mutane su yabe ka, ya Allah;

bari dukan mutane su yabe.

6 Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta

Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.

7 Allah yă sa mana albarka,

dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.

Zabura 67