Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 48

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza.

1 Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo,

a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.

2 Kyakkyawa ce cikin tsayinta,

abin farin cikin dukan duniya.

Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafona ne Dutsen Sihiyona,

birninb Babban Sarki.

3 Allah yana cikin fadodinta;

ya nuna kansa mafaka ce gare ta.

4 Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni,

sa’ad da suka yi gaba tare,

5 sun gan ta suka kuwa yi mamaki;

suka gudu don tsoro.

6 Rawar jiki ya kama su a can,

zafi kamar na mace mai naƙuda.

7 Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish

da iskar gabas ta wargaje.

8 Yadda muka ji,

haka muka gani

a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki,

a cikin birnin Allahnmu.

Allah ya sa ta zauna lafiya

har abada. Sela

9 Cikin haikalinka, ya Allah,

mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.

10 Kamar sunanka, ya Allah,

yabonka ya kai iyakokin duniya;

hannunka na dama ya cika da adalci.

11 Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki,

ƙauyukan Yahuda suna murna

saboda hukuntanka.

12 Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta,

ku ƙirga hasumiyoyinta,

13 ku lura da katangarta da kyau,

ku dubi fadodinta,

don ku faɗe su

ga tsara mai zuwa.

14 Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin;

zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.

Translator’s notes

  1. 48:2 (a): Zafon yana nufin dutse mai tsarki ko kuwa gefen arewa.
  2. 48:2 (b): Ko kuwa duniya, Dutsen Sihiyona, a arewanci na

Zabura 48