An Keɓe Haikali na Biyu

515 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ezra 6:14–22

14 Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa. 15 An gama ginin haikalin a rana ta uku na watan Adar a shekara ta shida ta mulkin Sarki Dariyus.

16 Sai mutanen Isra’ila, firistoci, Lawiyawa da kuma sauran waɗanda suka dawo daga bauta suka yi bikin keɓe gidan Allah, cike da farin ciki. 17 Suka miƙa bijimai guda ɗari, da raguna ɗari biyu, da ’yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra’ila, suka kuma miƙa bunsurai guda goma sha biyu don hadaya ta zunubi, kowane bunsuru ɗaya don kowace kabila ta Isra’ila. 18 Suka kuma naɗa firistoci a gundumominsu da kuma Lawiyawa a ƙungiyoyinsu don hidimar Allah a Urushalima, bisa ga abin da aka rubuta a Littafin Musa.

19 A rana ta goma sha huɗu ga watan farko, sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi Bikin Ƙetarewa. 20 Firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka zama da tsabta. Lawiyawa suka yanka ragon Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda suka dawo daga bauta, da kuma domin ’yan’uwansu firistoci, da kuma domin kansu. 21 Sai Isra’ilawa waɗanda suka dawo daga bauta suka ci tare da duk waɗanda suka keɓe kansu daga halin ƙazanta na Al’ummai maƙwabtansu, don su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila. 22 Suka yi kwana bakwai suna Bikin Burodi Marar Yisti, suna cike da farin ciki, gama Ubangiji ya cika su da farin ciki don ya sa sarkin Assuriya ya canja tunaninsa, ya taimake su cikin aikin gidan Allah, Allah na Isra’ila.

Zabura 48

Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza.

1 Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo,

a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.

2 Kyakkyawa ce cikin tsayinta,

abin farin cikin dukan duniya.

Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona,

birnin Babban Sarki.

3 Allah yana cikin fadodinta;

ya nuna kansa mafaka ce gare ta.

4 Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni,

sa’ad da suka yi gaba tare,

5 sun gan ta suka kuwa yi mamaki;

suka gudu don tsoro.

6 Rawar jiki ya kama su a can,

zafi kamar na mace mai naƙuda.

7 Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish

da iskar gabas ta wargaje.

8 Yadda muka ji,

haka muka gani

a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki,

a cikin birnin Allahnmu.

Allah ya sa ta zauna lafiya

har abada. Sela

9 Cikin haikalinka, ya Allah,

mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.

10 Kamar sunanka, ya Allah,

yabonka ya kai iyakokin duniya;

hannunka na dama ya cika da adalci.

11 Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki,

ƙauyukan Yahuda suna murna

saboda hukuntanka.

12 Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta,

ku ƙirga hasumiyoyinta,

13 ku lura da katangarta da kyau,

ku dubi fadodinta,

don ku faɗe su

ga tsara mai zuwa.

14 Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin;

zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.

Zabura 81

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf.

1 Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu;

ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!

2 Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga,

ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.

3 Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata,

da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;

4 wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila,

farilla ta Allah na Yaƙub.

5 Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf

sa’ad da ya fito daga Masar.

Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.

6 Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku;

an ’yantar da hannuwansu daga kwando.

7 Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku,

na amsa muku daga girgijen tsawa;

na gwada ku a ruwan Meriba. Sela

8 “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku,

in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!

9 Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku;

ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.

10 Ni ne Ubangiji Allahnku

wanda ya fitar da ku daga Masar.

Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.

11 “Amma mutanena ba su saurare ni ba;

Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.

12 Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare

don su bi dabararsu.

13 “A ce mutanena za su saurare ni,

a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,

14 da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu

in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!

15 Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki,

hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.

16 Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau;

da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”

Zabura 146

1 Yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji, ya raina.

2 Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina;

zan rera yabo ga Allahna muddin raina.

3 Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna,

ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.

4 Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa;

a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.

5 Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa,

wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.

6 Mahaliccin sama da ƙasa,

teku, da kome da yake cikinsu,

Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.

7 Yakan biya bukatun mutanen da aka danne

ya kuma ba da abinci ga mayunwata.

Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,

8 Ubangiji yakan ba wa makafi ido,

Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa,

Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.

9 Ubangiji yana tsaron baƙi

yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa,

amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.

10 Ubangiji yana mulki har abada,

Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani.

Yabi Ubangiji.