An Keɓe Haikali na Biyu (continued)

515 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 147–150

1 Yabi Ubangiji.

Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu,

abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!

2 Ubangiji ya gina Urushalima;

ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.

3 Ya warkar da masu raunanar zuciya

ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

4 Ya lissafta yawan taurari

ya kuma kira kowannensu da suna.

5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;

ganewarsa ba shi da iyaka.

6 Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai

yakan yar da mugaye a ƙasa.

7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;

ku kada garaya ga Allahnmu.

8 Ya rufe sararin sama da gizagizai;

yana tanada wa duniya ruwan sama

yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.

9 Yakan tanada wa shanu abinci

da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.

10 Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki,

balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum;

11 Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa,

waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.

12 Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima;

ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.

13 Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki

yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.

14 Yana ba da salama ga iyakokinki

yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.

15 Yana ba da umarninsa ga duniya;

maganarsa tana tafiya da sauri.

16 Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu

yă kuma watsar da hazo kamar toka.

17 Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu.

Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?

18 Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su;

yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.

19 Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub,

dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.

20 Bai yi wannan ga wata al’umma ba;

ba su san dokokinsa ba.

Yabi Ubangiji.

148:1 Yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji daga sammai,

yabe shi a bisa sammai.

2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,

yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

3 Yabe shi, rana da wata,

yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

4 Yabe shi, ku bisa sammai

da kuma ku ruwan bisa sarari.

5 Bari su yabi sunan Ubangiji,

gama ya umarta aka kuwa halicce su.

6 Ya sa su a wurarensu har abada abadin;

ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.

7 Yabi Ubangiji daga duniya,

ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,

8 walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai,

hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,

9 ku duwatsu da dukan tuddai,

itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,

10 namun jeji da dukan dabbobin gida,

ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,

11 sarakunan duniya da dukan al’ummai,

ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,

12 samari da ’yan mata,

tsofaffi da yara.

13 Bari su yabi sunan Ubangiji,

gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka;

darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.

14 Ya tayar wa mutanensa ƙaho,

yabon dukan tsarkakansa,

na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa.

Yabi Ubangiji.

149:1 Yabi Ubangiji.

Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,

yabonsa a cikin taron tsarkaka.

2 Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu;

bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.

3 Bari su yabi sunansa tare da rawa

suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.

4 Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa;

yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.

5 Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma

su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.

6 Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu

takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,

7 don su ɗau fansa a kan al’ummai

da kuma hukunci a kan mutane,

8 don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi,

manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,

9 don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu.

Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa.

Yabi Ubangiji.

150:1 Yabi Ubangiji.

Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;

yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;

yabe shi saboda mafificin girmansa.

3 Yabe shi da ƙarar kakaki,

yabe shi da garaya da molo,

4 yabe shi da ganga kuna taka rawa,

yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

5 yabe shi da kuge mai ƙara,

yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji.