Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 6

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit.a Ta Dawuda.

1 Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka

ko ka hore ni cikin hasalarka.

2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma;

Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.

3 Raina yana cikin wahala.

Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?

4 Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni;

ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.

5 Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu.

Wa ke yabonka daga kabari?b

6 Na gaji tiƙis daga nishi.

Dukan dare na jiƙe gadona da kuka

na jiƙe kujerata da hawaye.

7 Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki;

sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.

8 Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta,

gama Ubangiji ya ji kukata.

9 Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa;

Ubangiji ya karɓi addu’ata.

10 Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya;

za su juya da kunya nan da nan.

Translator’s notes

  1. 6:0 (a): mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce.
  2. 6:5 (b): Da Ibraniyanci Sheol

Zabura 6