Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 42

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

LITTAFI NA BIYU a

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Maskilb ne na ’Ya’yan Kora maza.

1 Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka,

haka raina yake marmarinka, ya Allah.

2 Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai.

Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne?

3 Hawayena ne sun zama abincina

dare da rana,

yayinda mutane suke ce da ni dukan yini,

“Ina Allahnka ɗin?”

4 Waɗannan abubuwa ne nakan tuna

sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina,

yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a,

ina bishe su a jere zuwa gidan Allah,

da sowa ta farin ciki da kuma godiya

a cikin taron biki.

5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

Me ya sa ka damu a cikina?

Ka dogara ga Allah,

gama zai sāke yabe shi,

Mai Cetona da kuma Allahna.

6 Rainac yana baƙin ciki a cikina;

saboda haka zan tuna da kai

daga ƙasar Urdun,

a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.

7 Zurfi kan kira zurfi

cikin rurin matsirgar ruwanka;

dukan raƙuma da igiyoyi

sun sha kaina.

8 Da rana Ubangiji yakan nuna ƙaunarsa,

da dare waƙarsa tana tare da ni,

addu’a ga Allah na raina.

9 Na ce wa Allah Dutsena,

“Me ya sa ka manta da ni?

Me zai sa in yi ta yawo ina makoki,

a danne a hannun abokin gāba?”

10 Ƙasusuwana suna jin jiki da wahala

yayinda maƙiyana suna mini ba’a,

suna ce mini dukan yini,

“Ina Allahnka ɗin?”

11 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

Me ya sa ka damu a cikina?

Ka dogara ga Allah,

gama zai sāke yabe shi,

Mai Cetona da kuma Allahna.

Translator’s notes

  1. 42:0 (a): Cikin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci masu yawa Zabura 42 da 43, zabura guda ce.
  2. 42:0 (b): Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
  3. 42:6 (c): Kaɗan a cikin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci, Seftuwajin da Siriyak; yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci yabe shi domin taimakon cetonsa. 6 Ya Allahna, nawa

Zabura 42