Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 52

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskila ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.”

1 Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum?

Me ya sa kake fariya dukan yini,

kai da kake abin kunya a idanun Allah?

2 Harshenka kan shirya hallaka;

yana nan kamar reza mai ci,

kana ta ruɗu.

3 Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri,

ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela

4 Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,

Ya kai harshe mai ruɗu!

5 Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka.

Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka;

zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela

6 Masu adalci za su ga su ji tsoro;

za su yi masa dariya, suna cewa,

7 “Yanzu, ga mutumin

da bai mai da Allah mafakarsa ba

amma ya dogara a yawan arzikinsa

ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”

8 Amma ni kamar itace zaitun ne

ina haɓaka a gidan Allah;

na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah

har abada abadin.

9 Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi;

a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau.

Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

Translator’s notes

  1. 52:0 (a): Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.

Zabura 52