Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 43

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 aKa nuna ni marar laifi ne, ya Allah,

ka kuma nemi hakkina

a kan al’ummai marasa sanin Allah.

Ka kuɓutar da ni daga

masu ruɗu da mugayen mutane.

2 Kai ne Allah mafakata.

Me ya sa ka ƙi ni?

Me zai sa in yi ta yawo ina makoki,

a danne a hannun abokin gāba?

3 Ka aiko da haskenka da gaskiyarka,

bari su bishe ni

bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki,

zuwa wurin da kake zama.

4 Sa’an nan zan tafi bagaden Allah,

ga Allah, farin cikina da murnata.

Zan yabe ka da garaya,

Ya Allah, Allahna.

5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

Me ya sa ka damu a cikina?

Ka dogara ga Allah,

gama zai sāke yabe shi,

Mai Cetona da Allahna.

Translator’s notes

  1. 43:0 (a): Cikin rubuce-rubucen hannu masu yawa a Ibraniyanci Zabura 42 da 43 zabura guda ce.

Zabura 43