Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Zabura 3

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom.

1 Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne!

Su nawa suke gāba da ni!

2 Da yawa suna magana a kaina suna cewa,

“Allah ba zai cece shi ba.” Selaa

3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;

ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,

ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

5 Na kwanta na yi barci;

na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma

suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

7 Ka tashi Ya Ubangiji!

Ka cece ni, ya Allahna!

Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi;

ka kakkarya haƙoran mugaye.

8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo.

Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

Translator’s notes

  1. 3:2 (a): Kalmar da ba a tabbatar da ma’anarta ba, mai bayyana sau da sau a cikin Zabura; mai yiwuwa kalma ce ta kiɗi.

Zabura 3