Zabura Daga Mulkin Dawuda, Kwanakinsu Ba Su Tabbata Ba (continued)

Zaburan da Dawuda ya rubuta bayan ya zama sarki, waɗanda ba a tabbatar da ranakun rubuta su da yanayin da aka rubuta su ba.

1015 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 39

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zabura ta Dawuda.

1 Na ce, “Zan lura da hanyoyina

zan kuma kiyaye harshena daga zunubi;

zan sa linzami a bakina

muddin mugaye suna a gabana.”

2 Na yi shiru, ban ce kome ba,

Ko a kan abin da yake da kyau!

Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi;

3 zuciyata ta ƙara zafi a cikina.

Kuma sa’ad da nake tunani, wuta ta yi ta kuna;

sai na yi magana da harshena na ce,

4 “Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata

da kuma yawan kwanakina;

bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.

5 Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai;

yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka.

Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum,

har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela

6 “Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa.

Yana ta yawo, amma a banza ne kawai;

yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba.

7 “Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema?

Begena yana a gare ka.

8 Ka cece ni daga dukan laifofina;

kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye.

9 Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba,

gama kai ne wanda ka aikata wannan.

10 Ka ɗauke bulalarka daga gare ni;

na ji jiki ta wurin bugun da hannunka ya yi mini.

11 Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu;

kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi,

kowane mutum dai shaƙar iska ne. Sela

12 “Ka ji addu’ata, ya Ubangiji,

ka saurari kukata ta neman taimako;

kada ka kurmance ga kukata.

Gama ina zama tare da kai kamar baƙo,

baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance.

13 Ka kau da fuskarka daga gare ni, saboda in sāke yin farin ciki

kafin in tafi in kuma rabu da nan.”

Zabura 86

Addu’ar Dawuda.

1 Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini,

gama ni matalauci ne mai bukata kuma.

2 Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka.

Kai ne Allahna; ka ceci bawanka

wanda ya dogara gare ka.

3 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,

gama na yi kira gare ka dukan yini.

4 Ka ba bawanka farin ciki

gama gare ka, ya Ubangiji,

na miƙa raina.

5 Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji,

cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.

6 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji;

ka saurari kukata na neman jinƙai.

7 A lokacin wahala zan yi kira gare ka,

gama za ka amsa mini.

8 A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji;

babu ayyukan da za a kwatanta da naka.

9 Dukan al’umman da ka yi

za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji;

za su kawo ɗaukaka ga sunanka.

10 Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki;

kai kaɗai ne Allah.

11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji,

zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka;

ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba,

don in ji tsoron sunanka.

12 Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata;

zan ɗaukaka sunanka har abada.

13 Gama ƙaunarka da girma take gare ni;

kai ka cece ni daga zurfafa,

daga mazaunin matattu.

14 Masu girman kai suna kai mini hari, ya Allah;

ƙungiyar marasa imani suna neman raina,

mutanen da ba su kula da kai ba.

15 Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri,

mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.

16 Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai;

ka ba wa bawanka ƙarfi;

ka ceci ni gama na bauta maka

yadda mahaifiyata ta yi.

17 Ka ba ni alamar alherinka,

don abokan gābana su gani su kuma sha kunya,

gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni.

Zabura 95

1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;

bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.

2 Bari mu zo gabansa da godiya

mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,

babban Sarki a bisa dukan alloli.

4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,

ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,

da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,

bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

7 gama shi ne Allahnmu

mu mutanen makiyayansa ne,

garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.

Yau, in kuka ji muryarsa,

8 “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba,

kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,

9 inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni,

ko da yake sun ga abin da na yi.

10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara;

na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce,

kuma ba su san hanyoyina ba.’

11 Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina,

‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”