Dalilin da Ya Sa Bulus Yake Wa'azi da Himma Sosai
Da yake ya san firgicin hukuncin da ke zuwa, Bulus ya ƙara himma wajen wa'azin bishara da lallashe mutane su zama Kiristoci. Yana yin aikinsa a matsayin wanda Allah ya san shi sarai, yana kuma fatan lamirin Korintiyawa ya san shi sarai haka ma. Sa'an nan ya kāre kansa daga sukar malaman ƙarya, domin waɗanda suka tuba ta wurinsa su sami dalilan yin alfahari da shi a matsayin manzo. Ya bayyana cewa ko ya yi wa'azin bishara yana jefa ransa cikin haɗari, har ƙungiyar 'yan adawa ta ɗauke shi mahaukaci, ko kuma ya yi aiki da hankali wajen guje wa tsanantawa, ya yi haka ne saboda almajiransa.
58 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
11 To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku. 12 Ba ƙoƙari muke mu yabe kanmu a gare ku ba ne, sai dai muna ba ku damar yin taƙama da mu ne, don ku sami amsar da za ku ba wa waɗanda suke taƙama da abin da ake gani ne, a maimakon abin da yake cikin zuciya. 13 In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne. 14 Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. 15 Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
Sabuwar Halitta da Aka Sulhunta da Allah
Bisa ga gaskiyar cewa Kiristi ya mutu domin dukan mutane, Bulus ya ci gaba da kafa hujja cewa daga yanzu babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da Ba’al’umme, domin ba a ƙara ɗaukar Kiristi a matsayin mutumin Yahuda bisa ga jiki ba. Dukan waɗanda aka haɗa da Kiristi ta wurin bangaskiya sun zama sabbin halittu, kuma tsofaffin ayyukansu na zunubi sun ƙare. Amfani da albarkun wannan sabon yanayi sun fito daga Allah kaɗai, wanda ya sulhunta duniya da kansa ta wurin Kiristi Yesu, ya kuma danƙa saƙon sulhu ga manzanni. Bulus, a madadin Kiristi, yana roƙon dukan mutane su zo wurin Allah su karɓi gafarar da aka saya musu ta wurin kafarar Ɗansa, wanda aka mai da shi hadaya don zunubin mutane.
16 Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka. 17 Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo! 18 Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu, 19 wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu. 20 Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah. 21 Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
Alamomin Mai Hidima Mai Aminci
A matsayinsa na jakadan Kiristi, Bulus yana roƙon Korintiyawa kada su karɓi alherin Allah a banza, amma su yi duk abin da bishara take bukata. Ta wurin bayyana wahalolin da shi kansa ya sha, Bulus ya zana hoton mai hidimar bishara mai aminci, ta haka kuma ya tabbatar cewa malamin ƙaryar bai kai shi ba.
1 A matsayinmu na abokan aikin Allah, muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza. 2 Gama ya ce,
“A lokacin samun alherina, na ji ka,
a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.”
Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.
3 Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi. 4 A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. 5 Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. 6 Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya, 7 da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu, 8 ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya, 9 mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba, 10 cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.
Bulus Ya Hana Ƙulla Hulɗa ta Kud da Kud da Marasa Bangaskiya
Bulus ya bayyana tsananin ƙauna da soyayyarsa ga Korintiyawa. Ya tsauta musu saboda rashin ƙaunarsu, yana kuma roƙonsu, a matsayinsu na 'ya'yansa, su buɗe masa zukatansu sosai a matsayinsa na ubansu na ruhaniya. Ya hana su auren marasa bangaskiya, ko yin abota da su, ko shiga kowace irin hulɗa ta kud da kud da su. Alkawarin Allah ga waɗanda suka ware kansu daga irin waɗannan alaƙa marasa tsarki ya kamata ya zama abin da zai fi kowane abu motsa su su yi ƙoƙarin kaiwa ga kamala.
11 Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai. 12 Ba mu ƙi nuna muku ƙaunarmu ba, sai dai ku kuka ƙi nuna mana. 13 A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.
14 Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? 15 Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi? 16 Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce,
“Zan zauna tare da su,
in yi tafiya a cikinsu,
zan zama Allahnsu,
su kuma za su zama mutanena.”
17 Saboda haka,
“Sai ku fito daga cikinsu,
ku keɓe kanku,
in ji Ubangiji.
Kada ku taɓa wani abu marar tsabta,
zan kuma karɓe ku.”
18 Kuma,
“Zan zama Uba a gare ku,
ku kuma za ku zama ’ya’yana, maza da mata,
in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
7:1 Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.
Bulus Ya Nemi a Karɓe Shi a Matsayin Manzo
Bulus yana roƙon Korintiyawa su amince da shi a matsayin manzo, kuma ta wurin ambaton dalilan da ya sa ya cancanci ƙaunarsu, ya yi nuni ga halin malamin ƙaryar wanda ya saɓa wa nasa. Ya tabbatar musu cewa bai faɗi haka domin ya hukunta su ba, amma saboda tsananin ƙaunarsa gare su. Yana farin ciki da kyakkyawar zuciyarsu da biyayyarsu.
2 Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba. 3 Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. 4 Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.
Farin Cikin Bulus Saboda Labarin da Titus Ya Kawo
A matsayin shaidar ƙaunarsa, Bulus ya gaya wa Korintiyawa damuwarsa a kansu, domin yana tsoron cewa malamin ƙaryar ya ɓatar da su. Ya ba da labarin farin cikinsa sa'ad da Titus ya iso da labarin biyayyarsu da ƙaunarsu. Ya yi musu magana game da wasiƙarsa ta farko, yana tabbatar musu cewa ya ba da umarnin a kori mutumin da ya yi lalata da danginsa daga ikilisiya domin ya nuna tsananin kulawarsa da su. Ya yaba wa biyayyarsu da himmarsu da tubansu. Ya gaya musu yadda halinsu ya ta'azantar da shi, da farin cikin Titus sa'ad da ya ga haɗin kansu da biyayyarsu.
5 Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. 6 Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus, 7 ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai.
8 Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai. 9 Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba. 10 Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa. 11 Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi. 12 To, ko da yake na rubuta muku, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana. 13 Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa.
Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka. 14 Na yi taƙama da ku a wurinsa, ba ku kuwa ba ni kunya ba. Kamar dai yadda dukan abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamarmu a kanku a gaban Titus ya zama gaskiya. 15 Ƙaunar da yake yi muku ya ƙaru ƙwarai, duk sa’ad da yake tunawa da biyayyarku duka, da kuma irin yawan bangirman da kuka nuna masa lokacin da kuka karɓe shi. 16 Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.