Korintiyawa Su ne Wasiƙar Bulus

Bulus ya yi tambaya cikin habaici ko shi ma, kamar malamin ƙarya, yana bukatar ya zo musu da wasiƙun yabo. Ya bayyana cewa su kansu su ne wasiƙun yabonsa, waɗanda aka rubuta ba da tawada ba amma da Ruhun Allah mai rai. Ta haka suka zama shaidar ikon da Allah ya damƙa masa a hidimar sabon alkawari.

58 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Korintiyawa 3:1–6

1 Yabon kanmu ne kuma muka fara yi? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi? 2 Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă santa, yă kuma karanta ta. 3 Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane.

4 Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah. 5 Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne. 6 Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.

Ɗaukakar Bishara Mafi Girma

A kan malamin ƙarya, Bulus ya bayyana fifikon bishara mai ɗaukaka. Mayafin da ya rufe ɗaukakar Musa ta zahiri mai shuɗewa alama ce ta rashin bayyani da yanayin misaltawa na alkawarin mutuwa. Masu hidimar alkawarin Ruhu, ta wurin ɗaukaka mafi girma mai ɗorewa da ke cikin baiwa da hurawar Ruhu Mai Tsarki masu dawwama, sun sami ƙarfin yaye mayafin alkawarin adalci mafi ɗaukaka, su yi bayaninsa, su kuma yi wa'azinsa a ko'ina.

2 Korintiyawa 3:7–18

7 To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Isra’ilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce, 8 ashe, hidimar Ruhu ba za tă fi wannan ɗaukaka ba? 9 In hidimar da take jawo wa mutane hukunci tana da ɗaukaka haka, to, lalle, hidimar da take kawo adalci za tă fi ta ɗaukaka nesa! 10 Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu. 11 In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwammame, lalle ne yă kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa!

12 Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan. 13 Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa. 14 Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi. 15 Har yă zuwa yau, duk sa’ad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu. 16 Amma duk sa’ad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin. 17 Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake. 18 Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.

Bulus Yana Wa'azin Kiristi, Ba Kansa Ba

Bulus ya nuna cewa hidima mai ɗaukaka da aka damƙa masa tana cika shi da bege da ƙwazo wajen yin aiki. Yana so ya nuna cancantarsa ta wurin bayyana dukan gaskiyar bishara dalla-dalla, wadda za ta iya ɓoyuwa ga masu tunanin duniya kaɗai, waɗanda sha'awoyinsu da mugayen gurace-guracensu suka makantar da su. Bulus ya bayyana cewa ba ya neman ɗaukakar kansa, domin Allah ya haskaka zuciyarsa don ya ba da sanin Allah da ɗaukakarsa, waɗanda aka bayyana cikin Yesu Kiristi.

2 Korintiyawa 4:1–6

1 Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba. 2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa. 3 Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. 4 Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. 5 Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. 6 Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.

Manzanni a Matsayin Tulunan Laka

Da yake kwatanta masu hidimar bishara da tulunan yumɓu, Bulus ya bayyana cewa Allah ya zaɓi mutanen da ba su da ilimi kuma ba a ɗauke su da muhimmanci ba su zama manzanninsa, domin ya nuna cewa mafificin ikon da ya sa addininsa ya yaɗu daga Allah yake, ba daga mutane ba. Ya lissafa wahalolin da suka fuskanta, a matsayin shaida cewa cetonsu daga waɗannan wahaloli bai fito daga gare su ba, sai dai daga Allah.

2 Korintiyawa 4:7–12

7 Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. 8 A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. 9 An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. 10 Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. 11 Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. 12 Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.

Bangaskiya da Bege Suna Taimaka wa Bulus Ya Jimre

Bulus ya nuna cewa ta wurin bangaskiya ga Kiristi da begen rayuwa marar mutuwa mai ɗaukaka, yana iya shawo kan dukan wahaloli da haɗarurrukan hidimarsa ta Kirista. Ya gaya musu cewa ya jimre wa waɗannan wahaloli saboda su, domin su gamsu da gaskiyarsa, su kuma gode wa Allah. Ya bayyana tabbacinsa cewa wahalolin da yake sha saboda bishara za su sa ya sami ladan da ya dace da su a sama. Saboda haka, ba ya neman amfanin wannan duniya mai wucewa, sai dai ɗaukakar madawwamiya ta duniyar da ba a gani.

2 Korintiyawa 4:13–18

13 A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana. 14 Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku. 15 Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.

16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. 17 Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. 18 Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.

Mazaunin Sama da Zai Zo

Bulus ya ci gaba da hujjarsa ta wurin nuna yadda mazauninmu na sama zai fi wanda muke zaune a cikinsa yanzu ƙwarai. Ya tabbatar cewa Allah yana shirya mu don wannan yanayi na rashin mutuwa, yana kuma ba mu Ruhunsa a matsayin jinginarsa. Wannan yana ba shi ƙarfin hali a wa'azinsa, yana kuma sa shi ya yarda ya bar wannan jiki domin ya kasance tare da Ubangiji. Amma ko yana rayuwa ko yana mutuwa, burinsa shi ne Allah ya amince da shi, domin kowa dole ne ya ba Allah lissafi.

2 Korintiyawa 5:1–10

1 Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. 2 Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama, 3 don sa’ad da aka yi mana sutura, ba za a same mu tsirara ba. 4 Sa’ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, sai dai don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa. 5 Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.

6 Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. 7 Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. 8 Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji. 9 Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan. 10 Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.