Bulus Ya Ci Gaba Zuwa Giris

Bulus ya ci gaba daga Makidoniya zuwa Giris, wato Akayya, ya kuma zauna a can wata uku.

57 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ayyukan Manzanni 20:2–3

2 Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris, 3 inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yă koma ta Makidoniya.

Bulus Ya Sake Rubuta wa Korintiyawa 58 bayan haihuwar Almasihu

Bulus, bayan ya ji yadda Korintiyawa suka karɓi wasiƙarsa ta farko, ya rubuta wasiƙarsa ta biyu daga Filibbi, domin ya nuna dacewar halinsa a matsayin manzo kuma ya kāre ikonsa, waɗanda wani malamin ƙarya ya sa aka yi shakku game da su.

Bulus Ya Sake Gaishe da Korintiyawa

Gabatarwa da albarkar Bulus.

2 Korintiyawa 1:1–2

1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,

Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya.

2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Bulus Ya Yabi Allah Saboda Ta'aziyyarsa

Bulus ya yabi Allah saboda riƙe shi da kuma kuɓutar da shi a cikin dukan wahalolinsa da haɗurransa, domin ta wurin misalinsa wasu su sami ta'aziyya iri ɗaya a cikin irin waɗannan wahaloli.

2 Korintiyawa 1:3–7

3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. 6 In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. 7 Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.

Allah Ya Ceci Bulus a Afisa

Bulus ya faɗi yadda ikon Allah ya kuɓutar da shi daga haɗarin da yake dab da faɗa masa a Afisa. Ya nuna godiya saboda addu'o'insu dominsa.

2 Korintiyawa 1:8–11

8 ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. 9 Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. 10 Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu, 11 yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.

Gaskiyar Zuciyar Bulus ga Korintiyawa

Da ɗan nuni ga ɓatancin malamin ƙarya, Bulus ya yi farin ciki da gaskiyar zuciyarsa da tsarkin halinsa ga Korintiyawa, yana bayyana cewa ba ya da wani dalili na son kai ko neman amfanin kansa. Yana da tabbaci cewa dukansu za su amince da shi kuma su yi alfahari da shi, kamar yadda wasu suka riga suka yi, tun da za su zama farin cikinsa a ranar Ubangiji.

2 Korintiyawa 1:12–14

12 Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba. 13 Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa, 14 kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.

Dalilin da Ya Sa Bulus Ya Jinkirta Ziyarsa

Malamin ƙarya ya zargi Bulus da rashin tsayawa kan shawara da son duniya domin bai yi ziyarar da ya yi wa Korintiyawa alkawari ba. Bulus ya nuna tsayuwarsa kan abu ɗaya ta wurin koyarwar da ya koyar wadda ba ta canjawa, ya kuma yi nuni ga shafewar Ruhu Mai Tsarki, wadda ta wurinta Allah ya tabbatar da ikonsa a cikinsu. Ya bayyana da gaske cewa ainihin dalilinsa na jinkirta ziyararsa shi ne burinsa na yi musu rangwame. Ya tabbatar musu cewa, maimakon ya zo ya hukunta su, ya rubuta cikin tsananin baƙin ciki, domin ya yi farin ciki da tubarsu kuma ya gamsar da su game da girman ƙaunarsa.

2 Korintiyawa 1:15–2:4

15 Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu. 16 Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya. 17 Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”?

18 Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce. 19 Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum. 20 Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah. 21 Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu, 22 ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.

23 Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba. 24 Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.

2:1 Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba. 2 Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yă faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba? 3 Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka. 4 Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.

Ku Gafarta wa Mai Laifi, Ku Mayar da Shi

Bulus ya umurce su su sake karɓar mutumin da aka kora daga ikilisiya, wanda suka yi baƙin ciki a kansa, yanzu da ya tuba da gaske. Su nuna ƙaunarsu gare shi ta halin kirki da abokantaka, domin kada Shaiɗan ya sa ya yanke ƙauna. Bulus yana sa ran za su yi masa biyayya wajen ɗage hukuncin, kamar yadda suka yi masa biyayya wajen zartar da shi. Ya bayyana cewa a duka biyun ya yi aiki cikin suna da ikon Kiristi.

2 Korintiyawa 2:5–11

5 In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne. 6 Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka. 7 Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa. 8 Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku. 9 Abin da ya sa na rubuta muku shi ne don in ga ko za ku jimre da gwajin nan, kuna kuma yin biyayya ta kowace hanya. 10 In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi, 11 don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.

Damuwar Bulus Game da Titus

A matsayin wani dalilin rashin zuwa Korint a lokacin da aka ƙayyade, Bulus ya ambaci damuwarsa game da Titus. Ya ba da labarin nasararsa a Makidoniya, ya kuma bayyana manyan sakamakon wa'azinsa, ga waɗanda suke karɓar bishara da waɗanda suke ƙin ta. Ya ƙare da kakkausar magana game da malamin ƙarya da kuma bayyana gaskiyar zuciyarsa da rashin son kansa.

2 Korintiyawa 2:12–17

12 To, sa’ad da na tafi Toruwas don in yi wa’azin bisharar Kiristi, ko da yake na tarar cewa Ubangiji ya buɗe mini ƙofa, 13 duk da haka, ban sami salama a zuciyata ba domin ban sami ɗan’uwana Titus a can ba. Sai na yi bankwana da su na wuce zuwa Makidoniya.

14 Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina. 15 Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. 16 Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin? 17 Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.