Halin Timoti ga Dattawa da Gwauraye

An ba Timoti ƙarin umarni domin koyarwarsa ta fi samun nasara. An koya masa yadda zai yi da dattawa, da samari da 'yan mata, da kuma gwaurayen da ikilisiya take tallafa musu da sadaka. Kada a karɓi wadda ba ta kai shekara sittin ba, don kada mata masu ƙananan shekaru, idan an karɓe su aka kuma hana su aure, su bar addinin Kirista ko su jawo wa sunan Kirista kunya.

57 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Timoti 5:1–16

1 Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka, 2 tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki.

3 Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. 4 Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. 5 Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako. 6 Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai. 7 Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi. 8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

9 Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta, 10 aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.

11 Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure. 12 Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko. 13 Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba. 14 Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna. 15 Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.

16 In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.

Girmama Dattawa, Yin Hankali Wajen Naɗa Su

An ba Timoti umarni game da yadda zai yi da dattawa, wato fastocin ikilisiya. Masu hidima nagari sun cancanci girma da albashi ninki biyu, kuma ikilisiya ta tanadar musu abin da ya dace. Sai da cikakkiyar shaida za a tsauta wa dattawa, sa'an nan a yi hakan a fili domin ya zama gargaɗi ga wasu. An umurci Timoti da gaske ya guji son kai sarai a shugabancinsa, ya kuma naɗa dattawa da matuƙar kulawa da hankali, bayan ya binciki halayensu da aminci, domin kada ya shiga cikin wani laifi ko rashin ɗa'a da zai bayyana daga baya. A wani ɗan kaucewa daga batun, Bulus ya ba shi shawara game da lafiyarsa.

1 Timoti 5:17–25

17 Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa. 18 Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.” 19 Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku. 20 Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro. 21 Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.

22 Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.

23 Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.

24 Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya. 25 Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su.

Bayi Su Girmama Iyayengijinsu

Domin addinin Kirista ba ya canja dangantakar zamantakewa, a gaya wa masu yi wa wasu hidima da bayi su nuna girmamawar da ta dace har ga iyayengijinsu arna. An gargaɗe su musamman su yi irin wannan biyayyar ga iyayengijinsu Kirista, kada kuma su bar haɗin kansu na 'yan'uwantaka a matsayin Kiristoci ya hana su yin ayyukan da aka san sun rataya a wuyansu.

1 Timoti 6:1–2

1 Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu. 2 Waɗanda suke da iyayengiji masu bi, to, kada su yi musu reni domin su ’yan’uwa ne. A maimako, sai ma su fi bauta musu, saboda waɗanda suke cin moriyar hidimarsu masu bi ne, ƙaunatattu ne kuma a gare su.

Waɗannan su ne abubuwan da za ka koya musu ka kuma gargaɗe su.

Bulus Ya La'anci Malaman da Suke Sa a Bi Al'adun Yahudawa

An la'anci malaman da suke sa a bi al'adun Yahudawa, waɗanda suke riƙe da koyarwar da ta bambanta da koyarwar gaskiya, kuma suke cewa mutane ba su da wajibcin sauke nauyin da ya rataya a kansu a matsayinsu na 'yan ƙasa. An tsauta musu saboda jayayya da faɗace-faɗacensu game da kalmomi, da kuma sa ribarsu ta duniya gaba da darajar Allah da yaɗuwar gaskiyarsa. An ƙarfafa gamsuwa a kowane matsayi na rayuwa, tun da dukan dukiyar duniya banza ce. Yawan son arziki babban haɗari ne.

1 Timoti 6:3–10

3 In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba, 4 yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace 5 da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi.

6 Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. 7 Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. 8 In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. 9 Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. 10 Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.

An Umurci Timoti a Gaban Allah Ya Tsaya da Ƙarfi

An kira Timoti, a matsayin wanda Allah ya hure masa, ya nisanci waɗannan munanan ayyuka ya kuma bi ibada. Bulus ya umurce shi, kamar a gaban Allah kuma yana duban babbar ranar shari'a, ya tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya, ya gudanar da aikinsa da lamiri mai kyau, ya kuma guji duk dalilai na son duniya da kwaɗayi. Bulus ya ƙare da bayyana babbar ɗaukakar Kiristi, wadda za a bayyana nan gaba.

1 Timoti 6:11–16

11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali. 12 Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa. 13 Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida, 14 ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi, 15 wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji, 16 wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.

Masu Arziki Su Dogara ga Allah, Ba Dukiya Ba

An umurci Timoti ya gargaɗi masu arziki kada su dogara ga dukiyarsu marar tabbas, sai dai ga Allah wanda yake ba da ita. An ƙarfafa su su zama masu arzikin ayyukan alheri, domin su tara wa kansu albarku mafi ɗorewa kuma na har abada.

1 Timoti 6:17–19

17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

Umarnin Ƙarshe na Bulus a Riƙe Bangaskiya

Bulus ya ƙare wasiƙar yadda ya fara ta, yana sake ƙarfafa Timoti ya tsaya da ƙarfi cikin koyarwar Kirista, ya kuma guji duk hasashe na falsafa marasa amfani da malaman ƙarya suke ƙoƙarin yaɗawa sosai.

1 Timoti 6:20–21

20 Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi, 21 wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya.

Alheri yă kasance tare da ku.