Bulus Ya Ba Maza da Mata Umarnai Game da Ibada
An sake ƙarfafa wajibcin addu’a. An umurci maza su yi addu’o’i a gaban jama’a, waɗanda bai kamata a taƙaita su ga majami’a ko haikali a Urushalima ba; idan an yi su da ibada, suna karɓuwa a kowane wuri. An ƙarfafa matan Kirista su yi ayyuka nagari, su kuma yi shiru. Tufafinsu su dace da shaidarsu ta rayuwa mai tsarki. Saboda laifinta, mace za ta kasance ƙarƙashin namiji. Za a rage la’anar da aka furta a kanta idan ta kasance cikin bangaskiya da tsarki.
57 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
8 Ina so maza a ko’ina su ɗaga hannuwansu masu tsarki cikin addu’a, ba tare da fushi ko faɗa ba. 9 Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba, 10 sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah.
11 Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya. 12 Ban ba mace izini ta koyar ko tă yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru. 13 Gama Adamu ne aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u. 14 Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi. 15 Amma mata Za tă sami ceto za su sami ceto ta wurin haihuwa, in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata.
Halayen da Ake Bukata ga Bishof da Masu Hidima
An bayyana halayen da ake bukata ga bishof, wanda yake kula da ikilisiyoyi da yawa, da kuma mai hidima da yake kula da ikilisiya guda.
1 Ga wata tabbatacciyar magana. In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya, yana marmarin yin aiki mai daraja ne. 2 To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3 ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba. 4 Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace. 5 (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?) 6 Kada yă zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girman kai yă kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis. 7 Dole kuma yă kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yă zama abin kunya yă kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.
Yadda Dole ne Dikon da Matansu Su Kasance
An jera halayen da ake bukata ga dikon. Matansu su zama abin koyi ga mutane.
8 Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba. 9 Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta. 10 Dole a fara gwada su tukuna; sa’an nan in ba a sami wani abin zargi game da su ba, sai su shiga aikin masu hidima.
11 A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.
12 Dole mai hidimar ikkilisiya yă zama mijin mace guda dole kuma yă iya tafiyar da ’ya’yansa da kuma iyalinsa da kyau. 13 Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.
Bulus Ya Ƙarfafa Timoti a Ayyukansa
Bulus ya ƙarfafa Timoti a ayyukansa na bishof da mai hidima ta wurin tuna masa da koyarwar addinin Kirista mafi ɗaukaka.
14 Ko da yake ina sa zuciya zo wurinka nan ba da daɗewa ba, ina rubuta muka waɗannan umarnai domin, 15 in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jama’ar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya. 16 Ba shakka, asirin addini da girma yake.
Ya bayyana cikin jiki,
Ruhu ya nuna shi adali ne,
mala’iku suka gan shi,
aka yi wa’azinsa cikin al’ummai,
aka gaskata shi a duniya,
aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.
Bulus Ya Yi Annabcin Ridda ta Ikilisiya
Ta wurin Ruhun Allah, Bulus ya yi annabcin yadda ikilisiyar Kirista za ta kauce wa bangaskiya, ya kuma bayyana irin gurɓacewarta, yana nuna a kaikaice cewa malaman da suke sa a bi al'adun Yahudawa suna cikin masu shirya mata hanya. An gargaɗi Timoti ya guji kowane irin karkata zuwa ga waɗannan gurɓacewa, an kuma ƙarfafa shi ya koyar da aikata nagarta da ibada a matsayin hidima kaɗai mai amfani kuma karɓaɓɓiya ga Kirista. An ce masa ya nace wajen koyar da wannan muhimmiyar gaskiya, duk da cewa za a zage shi a kuma tsananta masa saboda haka.
1 Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. 2 Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca. 3 Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. 4 Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, 5 domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.
6 In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi. 7 Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah. 8 Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa. 9 Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. 10 Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.
11 Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa.
Bulus Ya Ba Timoti Umarni Game da Halinsa
Bulus ya ba Timoti umarni game da halinsa, yana so ya ajiye duk batutuwan zato a koyarwarsa. Ya zama abin koyi ga ikilisiya, ya kuma ba da kansa ga hidima, da karatu, da nazari, da zurfafa tunani, da kamun kai. Ta yin haka zai ceci kansa, ya kuma zama hanyar ceto ga wasu.
12 Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki. 13 Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa. 14 Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka.
15 Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka. 16 Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.