Demetiriyus Ya Tayar da Gungun Masu Fushi a Afisa
Bulus ya ci gaba da zama a Afisa. Demetiriyus ya tayar da gungun masu fushi a can.
57 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
23 Kusan wannan lokaci sai aka yi wani babban hargitsi game da wannan Hanyar. 24 Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba. 25 Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a. 26 Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan. 27 Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.”
28 Da suka ji haka, sai suka yi fushi ƙwarai suka fara ihu suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!” 29 Jim kaɗan sai hayaniya ta tashi a dukan birnin. Sai mutane suka cafke Gayus da Aristarkus, abokan tafiyar Bulus daga Makidoniya, suka ruga da zuwa fili da nufi ɗaya. 30 Bulus ya so ya bayyana a gaban taron, amma almajirai ba su bar shi ba. 31 Har waɗansu shugabannin lardin ma, abokan Bulus, suka aika masa suna roƙonsa kada yă kuskura ya shiga filin nan.
32 Taron kuwa ya ruɗe. Waɗansu suna ihu suna ce abu kaza, waɗansu kuma wani abu dabam. Yawancin mutane kuma ba su ma san abin da ya sa suke a wurin ba. 33 Yahudawa suka tura Alekzanda gaba, sai waɗansu a taron suka riƙa yin masa ihu. Sai ya ɗaga hannu don a yi shiru don yă kāre kansa a gaban mutane. 34 Amma sa’ad da suka gane shi mutumin Yahuda ne, sai duk suka yi ihu gaba ɗaya na kusa sa’a biyu, suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
35 Sai magatakardar birnin ya sa taron su yi shiru, sa’an nan ya ce, “Mutanen Afisa, ashe duk duniya ba tă san cewa birnin Afisa ce mai lura da haikalin Artemis mai girma da kuma siffarta da ya fāɗi daga sama ba? 36 Saboda haka, da yake ba dama a yi mūsun wannan gaskiya, ya kamata ku natsu kada ku yi kome da garaje. 37 Kun kawo mutanen nan a nan, gashi kuwa ba su yi fashin haikali ba, ba su kuwa saɓa wa alliyarmu ba. 38 To, in haka ne, in Demetiriyus da abokan sana’arsa suna da wata magana game da wani ai, kotuna suna nan a buɗe, akwai kuma muƙaddasai. Suna iya kai ƙara. 39 In kuma akwai wani abu har yanzu da kuke so ku kawo, dole a daidaita shi a majalisa. 40 Yadda yake a yanzu, muna a hatsarin amsa zargin ta da hargitsi saboda abin da ya faru yau. Da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa aka yi wannan hargitsi ba.” 41 Bayan da ya faɗi haka, sai ya sallami taron.
Bulus Ya Bar Afisa Zuwa Makidoniya
1 Sa’ad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya.
Bulus Ya Rubuta wa Timoti
Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta farko zuwa ga Timoti, don ya ba shi umarnin yadda zai murƙushe koyarwar ƙarya da ɓarna da masu tsananin kishin addinin Yahuda suke ƙoƙarin kafa a ikilisiyar Afisa, wadda aka naɗa shi ya shugabanta.
Bulus Ya Gai da Timoti
Gaisuwar.
1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,
2 Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya.
Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.
Dalilin da Ya Sa Bulus Ya Bar Timoti a Afisa
Bulus ya tuna wa Timoti dalilin da ya sa ya bar shi a Afisa: don ya yi hamayya da masu tsananin kishin addinin Yahuda, waɗanda suke ƙoƙarin gauraya lissafin zuriyoyi da al’adu cikin koyarwar Kirista.
3 Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba 4 ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya.
Manufa da Amfanin Doka
Bulus ya bayyana manufa da amfanin Doka, yana nuna cewa ta jitu sarai da addinin Kirista, domin tana wajabta kyawawan halaye tana kuma hukunta kowace irin mugunta.
5 Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya. 6 Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana. 7 So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai.
8 Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata. 9 Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, 10 da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa, 11 da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.
Jinƙan Kiristi Wajen Mai da Bulus Manzo
Bulus ya ɗan karkata daga batun don ya yi magana dalla-dalla a kan alherin Kiristi na mai da shi manzon wannan bishara mai ɗaukaka. Saboda jinƙan da Allah ya nuna masa, ya gayyaci dukan masu zunubi zuwa tuba.
12 Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa. 13 Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya. 14 An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.
15 Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu. 16 Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. 17 Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.
An Umurci Timoti Ya Riƙe Bangaskiya
Bulus ya tuna wa Timoti cewa an naɗa shi ga hidimar Kirista ta wurin annabci, ya kuma ƙarfafa shi ya riƙe tsarkakakkiyar bangaskiya da lamiri mai kyau. Ana hukunta Alekzanda da Himenayus, waɗanda ba su riƙe ko ɗaya daga cikin waɗannan ba, saboda rashin ibadarsu.
18 Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau, 19 kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu. 20 Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.
Bulus Ya Umurci A Yi Addu’a ga Dukan Mutane
Yana hamayya da Kiristoci masu neman a bi addinin Yahudawa, Bulus ya umurci waɗanda suka tuba zuwa addinin Kirista su yi addu’a domin dukan mutane cikin halin alheri na bishara, ko Yahudawa ne ko al’ummai, musamman domin sarakuna da masu iko na kowace al’umma da ƙasa. Ya bayyana cewa wannan yana faranta wa Allah rai, wanda yake so dukan mutane su sami ceto, kuma a wurinsa akwai Matsakanci ɗaya kaɗai tsakanin Allah da mutanen dukan al’ummai. An naɗa Bulus don ya sanar da waɗannan gaskiyoyi ga al’ummai da kuma Yahudawa.
1 Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum 2 da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3 Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4 wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya. 5 Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, 6 wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci. 7 Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.