Adamu na Farko da na Biyu
An tabbatar wa Yahudawa da gaskiyar tashin matattu ta wurin kamancin da yake tsakanin Adamu na farko da na biyu.
57 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
45 Haka yake a rubuce cewa, “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai. 46 Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya. 47 Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. 48 Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama. 49 Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama.
Nasara a Kan Zunubi da Mutuwa
Bulus ya tabbatar cewa jikinmu na yanzu ba zai iya shiga yanayin ruhaniya ba. Ya bayyana yadda tashin matattu zai faru da canji mai ɗaukaka da zai kasance cikin yanayin rashin mutuwa, tare da cikakkiyar nasara a kan zunubi da mutuwa. A kan waɗannan dalilai aka ƙarfafa Korintiyawa su kasance da bangaskiya mai aiki kuma tabbatacciya.
50 Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba. 51 Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu 52 farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu. 53 Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. 54 Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”
55 “Ya ke mutuwa, ina nasararki?
Ya ke mutuwa, ina dafinki?”
56 Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. 57 Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
58 Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
Bulus Ya Ba da Umarnin Tara Tallafi ga Talakawa
Da yake amsa tambayar Korintiyawa ta ƙarshe, Bulus ya ba da umarnai game da yadda ya kamata Kiristoci su tanada wa talakawa, ya kuma yi alkawarin aika da gudummawar da suka tara zuwa Urushalima.
1 To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa. 2 A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. 3 In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima. 4 In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.
Saƙonnin Bulus na Ƙarshe da Gaisuwarsa
Bulus ya kammala wasiƙarsa da saƙonni da gaisuwa iri-iri. Ya ba su labarin ɗansa Timoti, da kuma cewa Afollos yana niyyar zuwa ya gan su. Ya yaba wa Timoti a gare su. Ya ƙarfafa su su kasance da bangaskiya da ƙauna. Ya yaba wa Istifanas da Fortunatus da Akaikus a gare su. Ya kammala da gaisuwa da fatan alheri.
5 Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya. 6 Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni. 7 Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda. 8 Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos, 9 domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.
10 In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. 11 Kada fa wani yă ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yă koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da ’yan’uwa.
12 Batun ɗan’uwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yă zo wurinku tare da ’yan’uwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi.
13 Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi. 14 Ku yi kome da ƙauna.
15 Kun san cewa iyalin gidan Istifanas ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku ’yan’uwa, 16 ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa. 17 Na yi farin ciki da isowar Istifanas, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba. 18 Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane.
19 Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa.
Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.
20 Dukan ’yan’uwa a nan suna gaisuwa.
Ku gai da juna da sumba mai tsarki.
21 Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.
22 Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji!
23 Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku.
24 Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.