Shaidun Tashin Kiristi daga Matattu

Bulus ya ci gaba da ƙaryata wata koyarwar kuskure ta Yahudawa game da tashin matattu wadda ta bazu a tsakanin Korintiyawa. Ya koma ga shaidar waɗanda suka gani da idanunsu a matsayin hujja mafi ƙarfi ta tashin Kiristi daga matattu.

57 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Korintiyawa 15:1–11

1 To, ’yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai. 2 Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da wa’azin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan.

3 Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi, 4 cewa an binne shi an kuma tashe shi a rana ta uku bisa ga Nassi, 5 cewa ya bayyana ga Bitrus, sa’an nan ga Sha Biyun. 6 Bayan haka, ya bayyana ga fiye da ɗari biyar daga cikin ’yan’uwa a lokaci guda. Yawancinsu kuwa suna nan da rai, ko da yake waɗansu sun riga sun yi barci. 7 Sa’an nan ya bayyana ga Yaƙub, sa’an nan ga dukan manzannin, 8 a ƙarshe duka, ya bayyana a gare ni, kamar wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba.

9 Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban kuma isa a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikkilisiyar Allah. 10 Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. A’a, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne. 11 To, ko ni ne, ko su ne, wannan shi ne abin da muke wa’azi, shi ne kuma abin da kuka gaskata.

Tashin Kiristi Ya Tabbatar Matattu Za Su Tashi

Bulus ya tabbatar daga tashin Kiristi cewa lalle za a tā da matattu. Ta wurin Adamu ’yan adam suka shiga ƙarƙashin mutuwa, kuma ta wurin Kiristi ake tā da su zuwa rai.

1 Korintiyawa 15:12–22

12 Amma in ana wa’azi cewa Kiristi ya tashi daga matattu, yaya waɗansu a cikinku suke cewa babu tashin matattu? 13 In babu tashin matattu, to, ba a tā da Kiristi ma ba ke nan. 14 In ba a tashe Kiristi ba kuwa, ai, wa’azinmu, da bangaskiyarku banza ne. 15 Sai ma ya zama mun zama masu ba da shaidar ƙarya game da Allah ke nan, domin mun shaida game da Allah cewa ya tashe Kiristi daga matattu. Bai tashe Kiristi ba ke nan, in lalle ba a tā da matattu. 16 Gama in ba a tā da matattu ba, to, Kiristi ma ba a tashe shi ba ke nan. 17 In kuwa ba a tashe Kiristi ba, bangaskiyarku a banza take, ya zama har yanzu kuna cikin zunubanku ke nan. 18 Ashe, waɗanda suka yi barci a cikin Kiristi ma sun hallaka ke nan. 19 In a wannan rayuwar ce kaɗai muke da bege cikin Kiristi, mun zama abin tausayi fiye da dukan mutane.

20 Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci. 21 Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum. 22 Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi.

Jerin Tashin Matattu

Bulus ya bayyana jerin tashin matattu. Kiristi zai miƙa mulkinsa na matsakanci bayan an tā da ’yan adam daga kabari, an kuma hallaka zunubi da mutuwa.

1 Korintiyawa 15:23–28

23 Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa. 24 Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko. 25 Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. 26 Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa. 27 Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi. 28 Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome.

Musun Tashin Matattu Ya Saɓa wa Baftisma

Rashin gaskata tashin matattu ya saɓa wa abin da muke furtawa a baftisma, yana kuma ƙarfafa rayuwar lalata. Ya gargaɗe su kada a ruɗe su.

1 Korintiyawa 15:29–34

29 To, in babu tashin matattu, mene ne waɗanda ake musu baftisma saboda matattu za su yi? In ba a tā da matattu sam, me ya sa ake yin wa mutane baftisma saboda su? 30 Mu ma don me muke sa kanmu cikin hatsari a kowace sa’a? 31 Ina fuskantar mutuwa kowace rana. I, kamar yadda yake tabbatacce cewa ina taƙama da ku cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu. 32 In na yi kokawa da mugayen namomin jeji a Afisa bisa ga ra’ayin mutane ne kawai, mece ce ribata, in har ba a tā da matattu? Ai,

“Sai mu ci mu sha,

da yake gobe za mu mutu.”

33 Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.” 34 Ku koma cikin hankalinku yadda ya kamata, ku kuma daina yin zunubi, gama akwai waɗansu da ba su san Allah ba, na faɗi wannan ne don ku kunyata.

Kamar Iri, Jiki Zai Tashi da Canji

Bulus ya amsa ƙin yarda da tashin matattu na masana falsafa ta wurin kwatanta shi da tsirowar shuka daga irinta. Ya nuna cewa jikin mutum da aka binne a ƙasa zai sake tashi haka nan a tashin matattu, halayensa sun canja, surarsa kuma ta fi kyau.

1 Korintiyawa 15:35–44

35 Amma wani yana iya tambaya yă ce, “Ta yaya ake tā da matattun? Da wane irin jiki za su tashi?” 36 Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu. 37 Sa’ad da kuke shuki, ba tsiron da zai yi girma ba ne kuka shuka, ƙwayar ce kawai, ko ta alkama ko kuma na wani irin dabam. 38 Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta. 39 Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu. 40 Akwai jikuna iri na samaniya, akwai kuma jikuna iri na duniya; sai dai darajar jikunan samaniya dabam take, darajar jikunan duniya kuma dabam take. 41 Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja.

42 Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka tā da shi kuma ba ya ruɓewa; 43 akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma tā da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma tā da shi da ƙarfi; 44 akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya.

In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma.